← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 113

Sashe 45

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sam Zahra'u ƙin zama tayi a asibitin, shi kuma yace wallahi bata isa ta bisa ba tunda bata da mutuncin da zata iya zama a asibiti wurin mahaifiyarsa, saboda haka yana fita itama ta fito yana bakin titi yaga ta tari napep ta hau.
Abun duniya duk ya ishe shi, jikinsa har wani ɗumi yay kamar me zazzaɓi. Ya rasa dalilin da yasa cikin ƴan kwanakin nan zuciyarsa ta addabe shi da tuna masa irin azabar da ubangiji ya tanadarwa wanda bai kwatanta adalci ba tsakanin matansa, ya sani ba wai bai sani ba ubangiji ba ya barin mijin da duk ya ƙuntata rayuwar iyalinsa, jiya har da mummunar mafarki yay da har yau ya kasa gane ma'anarsa balle yasan in da ya dosa da musababbin yinsa.

Kai tsaye gida ya wuce, yana zuwa ɓangaren Malam ya nufa. Sai da ya jima zaune yana jiran Malam ɗin kafin ya fito, bayan sun gaisa ne kansa ƙasa ya rasa ta inda zai fara magana. Malam dai kallonsa kawai yake yay guntun murmushi irin na su na manya yace da shi,"Ka zo ka saka ni gaba, da wani abu ne? Ko jikin mahaifiyar taku ne".

Ƙeya ya ɗan sosa kan yace,"Dama Malam akan waccan maganar da na maka ne kwanakin baya". Yay maganar cikin kame kame.

Malam yace,"Wacce magana kenan, abubuwan da yawa bana iya tunawa ba".

Sai ya ɗago ya kalli mahaifin nasa kaɗan kafin ya kuma sadda kai ƙasa, shi kansa nauyin maganar yake ji to amma babu yanda ya iya haka dole yace,"Amm Amm akan maganar Sa'ida, na maka magana tun kafin ta fita idda sai baka ce komai ba, to yanzu ina so ne na shiga sahun manema aurenta don Allah a shige min gaba".

Malam yay masa wani duba na baka da hankali, so yake ya mayar da shi mutumin banza, tun ba'ai wata biyu da rabuwan auren ba yake ta masa zarya, haka yay ta damunsa da kira shi lallai yana so zai dawo da matarsa. Malam kuwa bai basa fuska ba sam hasalima ranar farko da ya fara yi masa maganar sai da yay masa tatas to da yake É—an yau ne baka haifi halinsa ba saboda rashin kunya bai fasa masa maganar ba, shi kuwa ko gani yay iyayen Sa'ida ma za su kuma basa Æ´arsu ai sai ya hana.

Har da zuwansa wajen Amarya itama zai kama ƙafa da ita ta taya shi shawo kan mahaifin nasa da ike idan tasa baki a magana Malam kan yarda, dan ko cikin matansa ma yafi shawara da ita.
To itama dama sam bata ji daɗin rabuwar auren ba, don a lokacin ji tayi da ace ita ta haifi Nazifi babu abin da zai hana bata masa duka ba don bai wuce duka a wurinta ba. Shi yasa ko da yaje mata da zancen komen yana magiyan akan ta roƙa masa Malam tace masa,"Babu ruwana Nazifi ba za ka haɗa ni faɗa da shi ba kuma kaja mahaifiyarka ta zo tana jin haushina, kana dai ganin a irin yanda ku ka rabu da yarinyar nan ni ban ma zaton zaka iya cewa zaka mayar da ita ba, wallahi ce na ke ka shafeta a babin rayuwarka".

Sau biyu yana zuwar mata da ƙoƙon bararsa taga kamar dai duk hankalinsa a tashe yake, sai ta basa shawaran cewa yaje gidan su Sa'idan ya samu mahaifanta ko ita ya nemeta ya bata haƙuri idan ta haƙura shikenan sai su sasanta kansu amma ita ba zata iya saka baki a sha'anin ba, babu ruwanta kar ta zo tayi baƙin jini kuma ya janyo mata faɗan kullum a wurin Malam.

Lokacin jinsa yay tamkar zai hauka, bai san dalilin da yasa tunanin Sa'ida da al'amarinta da shi ba ya addabesa, tun da ya rabu da ita bai yi danasani ba balle nadama, imfact ji ma yake kamar ya rabu da wata ƙaya ne, kuma dama bai san ma shi ba sonta yake ba sai da ya auri Zahra'u, to a yanzu ma da suka rabu ba wai don yana sonta ne zai mayar da ita ba, ba don tausayi ko don ya wulaƙantata ba kamar yanda ya sha alwashi lokacin da aka tilasta masa sakinta, a'a haka kawai zuciyarsa ke faɗa masa cewa ya dawo da ita kamar hakan na da amfani a gare shi, kamar yana da buƙatarta musamman ma idan yaga halin ciwon da mahaifiyarsa ke ciki.
Har magana yay da abokinsa Hamisu shima yace bai da shawarar da zai basa ta wannan ɓangaren, bai kuma isa ya tunkari Iyam da zancen ba, su Yaya ma duk ba zasu goyi da bayan hakan ba shiyasa ma babu wacca ya tunkara da maganar a cikin Yayyun nasa, balle yanzu ma da basa wata hulɗa da Yaya gaba suke a tsakaninsu.

Sai daga baya yay amfani da shawaran Amarya yaje gidan su Sa'idan har sau biyu sai dai ya rasa ta yanda zai aika a kirawo masa ita, idan ma ta fito bai san me zai ce mata ya kawo shi wurinta ba.
zuwansa na uku ne kuma suka haɗu da Abbaa ya dawo daga masallaci, lokacin Abbaa har ya shiga soro sai ya dawo ganin baƙuwar mota a ƙofar gidan, bai ma san Nazifin ba ne don har ya fito a motar ya durƙusa a gabansa suka gaisa bai ɗauka muryarsa ba.

Kuma hakan sai yasa du ya diririce, Abbaa ma yay zaton ko cikin zawaran da ke zuwa wurin Sa'ida ne sai da yace masa shi ne tukunna Abbaa yace,"Ohh to lafiya, me ya kawo ka gidana?".

Babu kunya kuma yake faÉ—awa Abbaan abun da ya kawosa wai so yake a basa dama ya shiga cikin manema auren Sa'ida.
Abbaa ya dakatar da shi cikin ɗaga murya,"Hala sai da ka maku kafin ka zo ko? Manta irin rashin mutuncin da ka shuka mana kayi ne? Ko saboda wancan lokacin ban ce da kai komai ba shi ne ka samu zarafin dawo min gida saboda baka da ta ido...Ai Kai dai ba zan taɓa mancewa da butulu ba irinka, Nazifi lokacin da ka shigo rayuwar ƴata cikin gata da jin daɗi ka sameta, duk da burin da na ke da shi akanta haka na haƙura lokacin da ka nemi auranta na aura maka ita saboda ina maka kallon ɗana wanda zai kula da rayuwar ƴata ya ingatata, ashe ashe kai ɗin baƙin mijici ne ban sani ba, na baka amanarta ka ɓige da cin zarafinta da wulaƙantata saboda kayi kuɗi, har sai da ta kai ta kawo ka mata ƙazafin kisa ka ɓatata a idon duniya, kuma tsabar ka isa ka zo har gabana ka sakar min ita, sannan yazu saboda kai fitsararre ne ka sake ɗebo ƙafafun rashin kunyarka ka zo wurina kana roƙon na baka damar ka mayar da ita, ai ko a baya abin da ka aikata mata rashin sanar da ni ne da wallahi sai nayi shari'a da kai...Ka saki ƴata kuma kun rabu, ba zan lamunci raini da iskancinka ba wai zaka sake aurenta, to bara na faɗa maka in dai batun mayar da aurenku ne ka bar tunaninsa domin lamari ne da ba zai taɓa yiwuwa ba, ni ba sakaran uba ba ne da zan ƙara yarda ƴata ta komawa wanda bai san darajarta ba...don haka kayi gaggawar tashi ka bar min ƙofar gida kafin na kira Imam ya fito yay maka dukan saɓa kamanni, ina ga rashin dakuwar shi ya baka lasisin dawowar mara kunyar banza da wofi".

Ya faɗa yana kallonsa cikin fusata. A lokacin gaba ɗaya kasa yin wata magana yay haka ya kasa ɗagowa ya dubi Abbaan, kansa a sunkuye ya miƙe yana jin ƙafafunsa a sanyaye ya koma mota ya bar wajen, duka abin da Abbaa ya faɗa masa bai ji zafi ba kuma bai ji haushinsa ba, sai dai duk yanda zai yi zai yi wajen ganin ya dawo da Sa'ida gidansa.

Malam ya katse tunaninsa da cewa,"....
__________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA*
Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA*
Halimahz

*LOKACI NE*
Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo

*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻*
09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR22FT5*
"Kai É—ago fuskarka ka kalle ni".
Ya É—ago yana duban Malam É—in wanda ke jifansa da mugun kallo.

"Ka san dai ni ba shashasha ba ne, kuma ba sakarai ba ne mara tunani irinka, da hankalina kuma ni ba mutumin banza ba ne kamarka, don haka kar ka ƙara zuwa gabana da maganar wani wai kana so ka mayar da tsohuwar matarka...kai ban da ɗan banza ne baka da ta ido mutanen da ka nunawa rashin mutuncinka kace a koma a ƙara nema maka auren ƴarsu, to wallahi ko ji nayi za su sake baka ƴar su sai na hana...".

"Don Allah Malam ayi haƙuri...".
"Dilla gafara rufe min baki bana son jin komai, ka tashi ka bani wuri idan ka san abun da ya kawoka kenan, idan kuwa ka ƙara yunƙurin min magana irin wannan Allah sai ka ga yanda zamu kwashe da kai".

Malam yay ta masa faɗa, shi dai a zuciyarsa bai san haƙiƙanin abin da yake ji ba, amma tabbas da Malam ɗin zai san a halin da yake ciki la shakka zai ji kukansa kuma ya karɓi roƙonsa.
Sallama yaywa Malam ɗin ya fita cikin sanyin jiki, wajen Amarya ya shiga suka gaisa, ta kawo masa abinci ya zauna yaci, ita ma nan yay ta faman roƙo da magiya tace ita fa sam ba da ita ba wannan lamarin, yaje ya samu Ummaa suyi maganar.
Chapter 45 · 0% Book details