← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 113

Sashe 49

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace,"Yauwa to dai shi, yay mana bayani yace wani bawan Allah ne da ya saba ɗaukar nauyin karatun ƴan makaranta sai aka haɗa da sunanki a list ɗin, shi Sa'id ma ce yay yana zargin wani mutum da suka taɓa haɗuwa acan makarantar da yaje dubo miki jarabawar intiro ɗin da kika yi...to dai ina ba ki labari shi dareta ɗin sai da muka kusa faɗa da shi saura kaɗan yay zuciya yace an cire sunanki saboda na takura shi da tambaya ina cewa ya faɗa min tsakani da Allah ba cutarmu za su yi ba".

Abbaa yay maganar yana dariya, muma duk dariyar muka yi, yace,"Yo Allah kuwa magana ta tsakani da Allah, yanda duniyar nan ta zama babu gaskiya da amana sai a zo a yaudaremu a cucemu saboda anga abin da muke so kenan mun ƙwallafa rai akan samu, shiyasa ni kuwa nayi ta jefa masa tambayoyi ina yaji tsoron tsayuwa a gaban Allah, ke har da wa'azizzika na dinga masa ƙarshe shima sai ya sakko yana dariya, yace bai ga laifina ba duniyar ce ta lalace. To dai kinga ai sai muka samu fahimtar juna yay min bayanai sosai da na gamsu amma duk da hakan dai na sa Yayyunki su ƙara bincike akai".

Na ce,"Abbaa ai ni da tunanina ma Suprise ɗin Safiyya ne, dama adu'a bata fi ƙarfin komai ba ina ta faɗawa Allah ya bani ta wata hanyar, sai ga shi ma Abbaa an ɗauke maka ɗawainiyar komai karatu kawai zan yi Abbaa".

Haƙoran gabansa tass a waje yace,"To Sa'ida ko da ba'a ɗauke min ko sisi ba ai in har an ba ki gurbin karatun an gama yi min komai, ba ni da shi, ban tara ba, ban bawa wani ajiya ba, amma kuma Allah ne mai yi, ba zai hana ni ba, zai hore min na yi miki duk wata hidima da ta shafi karatunki Sa'ida, ni dai fatana Allah yasa ki fara a sa'a kema na ganki cikin kayan asibiti kina taimakon al'umma musamman talakawa, kuma ina roƙon Allah ya bani tsawon rai naga wannan lokaci, ke kuma yasa miki albarka a karatun. Sa'ida bana mancewa lokacin da za'a haifi Imam irin rashin rashin kirkin da malaman asibiti suka mana akan babu kuɗin magani da alluran da za'a siya, don Allah Sa'ida ki zama me taimakawa ba mai wulaƙantawa ba, kar kuɗi su rufe miki ido ki kasa taimakon al'ummar Annabi".

Na sa hannu ina goge hawayena na ce,"In sha Allahu Abbaa, na maka alƙawari Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana, na gode na gode sosai Allah yay muku sakayya da gidan aljannah, ina son ku wallahi ina sonku Allah yasa kuci moriyar ɗawainiyar da ku ka yi akaina".

Ummani tace,"To mora kuma na nawa Sa'ida, ai mu babu abin da zamu ce da ubangiji sai godiya da ya bamu ƴaƴa masu jin ƙan mu da tausayinmu, ke ma ƴar sana'ar da kike yi da ɗan albashin da ake baki ba ga shi nan ba yaushe rabon da mu sayi sabulu da omo da kuɗinmu, ai Alhamdulillahi Allah ya ƙara buɗa muku ya sawa nemanku albarka".

Abbaa yace,"To yanzu ina kika zaɓa can ƙasar turawan ko kuwa nan dai in dai muka fi kauri".

Kafin na ce wani abu Ummani ta riga ni da cewa,"A'a fa Abbaansu na faɗa maka ta dai yi karatunta anan, ni bana son wannan nisan, ina zamu turata ƙasar waje tana mace a'a tayi a gabanmu ta gama har Allah ya kawo mata mijin aure, ni dai ka ma cire batun bata wani zaɓi na in da take so".

Abbaa yace,"To anji ta bakinki Hajiya Sa'a Babar Sa'ida". Sai ya maida dubansa garen yace,"Ina jinki Æ´ar albarka ina kike so? Baturiyar za ki koma ko kuwa dai kasar ki ta gado garin hausawa".

Ina wasa da yatsun hannuna na ce,"Abbaa ni ai na bar muku zaɓin duk inda ku ka ce nan zan je, zaɓinku shi ne nawa".

Sai Abbaa ya dubi Yaya Imam ya ce,"Imamu me ka ce? Kun san abin da kuka ce akan karatun nan shi ne, tunda kun fi mu sanin lamuran yanda suke, jiyan Sa'id yace aji ta bakinta tukunna".

Yaya Imam yana kallon Ummani yace,"Ehh ya kira ni ai a daren jiyan muka yi magana, ni da ce nayi ai ba aure ba ne da za'a bata zaɓi, inda muka ga yafi a turata can ɗin kawai. to yanzu tunda ta baku zaɓi kawai ka yanke magana Abbaa, zaka fi mu hange da zurfin nazari".

Abbaa yay shiru na ƴan daƙiƙa, ya numfasa kafin yace,"To da muka dawo daga masallacin asuba na yiwa ƴan uwana maganar, mun tattauna da su akai na faɗa musu duk yanda aka yi kun san sha'ani irin wannan abun da zai je ya dawo ake ji ba wani abu ba. To shi Babanku Tijjani yace idan za'a bi shawaransa a barta ta tafi can ƙasar wajen saboda samun ingancin karatun, namu da na su ba ɗaya ba ne. To Amma ya kuke gani Imam taje can ɗin ko nan ɗin?".

Yaya Imam yace,"Ke ki faÉ—a da kan ki, can É—in ko nan?".

Nayi shiru, Abbaa ya numfasa kafin yace,"To ni dai har ga Allah sallar da nayi a jiya ta istikara zuciyata tafi samun natsuwa da fitar taki Sa'ida, kuma dama zaɓin Allah shi muke nema, ni na yarda da ke na kuma yarda da irin tarbiyar da na baki, sannan na yarda da Allah ne me kiyayewa da karewa, wayonmu ko dabararmu ba su zasu mana ba, adu'a ce muna miki kuma ba zamu fasa ba, Allah zai tsare mana ke sannan kema kuma ki tsare mutuncinki. Naga ƴaƴa mata da yawa da suka fita karatun nan suka yi lafiya suka gama lafiya, ni dai roƙona a gare ki kiyi abin da ya kai ki Sa'ida, ba yinmu ba ne yin Allah ne, kuma ya dubemu ne ya dubi kyakykyawar niyayyarmu ta manufarmu akan karatunki, ki taimaka min Sa'ida kar ki bani kunya, kin dai gani irin yanda ƴan uwanki suke ta fafutukar nema miki ta gwamnati ma ba'a samu ba, amma Allah da ikonsa sai ya ba ki rabo a inda bamu taɓa tunani da kai kanmu can ba don sun fi ƙarfinmu, ko ba ƙasar waje za ki fita ba Sa'ida ko anan za ki zauna nasihar dai duka ɗaya ce, idan kika kiyaye sai Allah ma ya kiyaye ki, kin dai sani kaf danginmu babu me ɗaukarki ya kai ki wannan makaranta me tsada ta ɗururuwan kuɗaɗe, to amma da ke abun na Allah ne muna zaune sai ga shi ya kawo miki. Allah yay miki albarka, Allah ya lulluɓe rayuwarki da kariyarsa, ya ba ki sa'a da nasara a karatun nan da za ki fara".

Dukanmu muka amsa da amin, ni dai gaba É—aya jikina ya mutu. Sai kuma Abbaa ya sake cewa,"Amma kar ki yi maganar da kowa tukunna ki bari sai tafiyar ta kankama, sha'anin rayuwar nan kake ji baka sanin zuciyar wamda kake tare da shi, wani yana nan bai son ci gabanka amma a fuska yana nuna maka ya fi kowa sonka, to ki bar abun da ke sai ahalinki duk wanda za ki faÉ—awa ki jira zuwa ranar tafiyarki sai ki kira waya kuyi sallama cikin aminci...nan da sati na sama naji ko?".

Na buɗe takardun na miƙawa Yaya Imam ya duba yace,"Ehh litinin ta sama kenan ban da wannan me zuwan".

"To yanzu me da me ya kamata a siya mata, kuma wanne shirye shirye zata yi?".

Yaya Imam yace,"Ai ina ga abun da zata tafi da su ba zai wuce kayan sawarta ba, idan ma da wani abu dai in taje can É—in ta kira waya ko kuÉ—i ne sai a tura mata".

Kawai sai naji jikina yay sanyi, na fara tunain yanzu idan na tafi sai fa na shekara uku kamar yanda na ke gani rubuce a jikin takardar. Anya ba zan fasa tafiya can ɗin ba duk da nima dama nafi so ta fita ɗin, to amma ya zan yi Abbaa har istikara yayi zaɓin Allah kuma ya nema, Allah yasa zuwana can ɗin babban alheri ne.

Yashaik ya zo Abbaa ya jaddada masa akan kar ya manta yaje can Emorate É—in yaga Director É—in ido da ido sannan yay bincike sosai akan lamarin.
Ina komawa É—aki na É—auka wayana na kira Safiyya, bacci take yi a lokacin amma jin albashiri É—in da na zo mata tuni ta warsteka tana cewa,"Ke ba na son wasa da feelings ena".

Nace,"Wallahi Tallahi da gaske nake yi miki".

Wani ihu tayi tana faÉ—in,"Wow what a great news Beb, admission a germany kuma nursing wow Beb am so happy for you wallahi, wanda yay miki silar nan ubangiji Allah ya haÉ—a shi da dukkan alkhairan duniya, ina ma zan gasa na masa kyauta. Yanzu yaushe ne ake batun za ku tafi don naji wata cousin ena ma na maganar tafiya can?".

"Sati na sama Beb, amma dai za ki zo kafin na tafi ko?".

Shiru ta É—anyi kafin tace,"Da wuya na zo nigeria cikin week É—in nan, kin ganmu muna Saudiya mun je Umrah jiya muka tafi, amma kar ki damu kina makaranta zan kawo miki visiting".

"To ƙawar arziki Allah ya amince sai na ganki, ki faɗawa Umma ma kin ji".

Da yake dai Safiyyar tawa sai a hankali sai ce ta min,"Ke wacce Umman mun yi faÉ—a da ita fa ba ma magana, ki kirawota da kan ki".

Kai na girgiza na ce,"Allah ya shirya min ke wallahi, yanzu da Umman ku ka yi faÉ—a?".

"ƙwarai aure ma zan zuga mijinta ya ƙara, ba dai ganin bata da kishiya ba ne yasa duk take takura min akan sai nayi aure ba, ki ji fa jiya tutsiye ni tayi wai lallai sai na bata lambar My ta kirawo shi ya zo anyi maganar aure".

"To mene abin laifi a ciki Beb, ai da gaskiyanta ke fa da kanki kin faɗa min yanda kike ta shan surutu a family na ku akan kin ƙi aure, kuma kin ga idan ke ba kya damuwa ita Umma dole zata damu, burin kowanne fa iyaye ne su ga sun aurar da ƴarsu wallahi hankalinsu yafi kwanciya".
Chapter 49 · 0% Book details