Sashe 51
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wayar na aje gefe na buɗe green ɗin jakar da na ke ta tantamar tawa ce, sai dai ina buɗewa mamaki ya kamani matuƙa da uban kuɗin da na gani a ciki wanda aka rubuta Euro a jiki, sai na ɗauko kai zan wa drivern magana na ce masa wannan ba tawa ba ce, sai maganar ta maƙale dalilin shigowar wani cikin motar wanda ya zauna a gaba, kansa da p-cap fara kansa a ƙasa ya kuma sanya face mask.
Gabana naji ya yanke ya faÉ—i ba tare da sanin dalili ba, ina aikin zare ido naji an jefo min abu jikina, É—aga idon da zan yi na duba sai naga face maske ce, Drivern kuma sai ya katse tunanin da na ke da cewa,"Madam kisa face mask saboda zamu tsaya ne a shopping mall makaranta ta ba da umarnin haka".
Fuskata a ɗaure na ke duban drivern, so na ke nayi magana to amma ina tsoro tun da ba hausa zan yi masa ba, kar nayi turancin nayi kwaɓa, to amma haka dole na dage na tattaro guntun turancina na ce masa,"Shi baƙon da ka ɗauka bai san darajar ɗan Adam ba ne da zai wurgo min abu jiki, ko ba zai ba ni da hannu ba ai sai yace na ɗauka".
Sai ya kama ba ni haƙuri, ni kuwa duk da haka naƙi ɗauka sai ma cilli da nayi da shi gefe, muka iso bakin wani babban mall motar tayi parking, motar ma bata gama tsayuwa ba na gaban ya fita cikin sauri ya shiga mall ɗin, ahi kuma drivern yace na fito na shiga ciki duk abin da na gani na ke na ɗauko makaranta ta riga ta biya kuɗin.
Na fito ina jin ƙafafuna na harɗewa, haka na tsaya kusan minti biyu ina ƙarewa wajen haɗaɗɗan mall ɗin kallo kafin a hankali nayi bismillah na fara takawa. Ina hawa kan step na biyu na duba saƙon da ya shigo wayata wanda ke cewa _"Mace me daraja bata yawo a ƙasar sai da face mask, ki ke rufe fuskarki kin ji"._
Murmushi nayi kawai na juya motar na É—auko face mask É—in yayin da na ke bin bayan kiran lambar Safiyya.
____________________________
₦500
07018098175.
*B2ƘR24FT5*
Nazifi ne zaune a ƙasa kan carpet, gefensa mug ne da ruwan tea a ciki wanda yaji haɗin kayan ƙamshin shayi yake kurɓa a hankali a hankali, yayin da laptop ke kan cinyarsa sai takardu a gafen hannun hagunsa duk a barbarje.
Wayarsa da ta yi ƙara ya dakatar da danne dannen da yake cikin laptop ɗin, ya ɗaga kiran bayan sun gama gaisawa yace.
"Wallahi kuwa ka ganni na kusa minti ashirin akanta na dai kasa fahimta, amma kuma na yi ƙoƙarin shigar da wancan document ɗin na dukka bayanan kamfanin, na samu Madam tayi min aikinsa, shi wannan ɗin ne dai na ke so zuwa anjima idan na fito sai ka duba kuma ka koya min saboda gaba ko".
Daga can ɓangaren aka yi magana kafin shi kuma ya ƙara cewa,"Oak oak tom shikenan babu matsala duk yanda ka gani ɗin dai zai yiwu, tun da ni ba sanin harkar na yi ba kuma na yarda da kai ɗari bisa ɗari, na san ba zaka jefa ni hanyar da zan cutu ba. Amma kamar nawa ka ke ganin zasu iya ba ni bashin?".
Shiru na ƴan sakanni yace,"Biliyan ɗaya! amma Alhaji Sunusi kana ganin zan iya requesting hakan kuwa? Basu yi yawa ba? Ka san yanda sha'anin kasuwancin yake duk ya taɓarɓare kar azo in karɓi kuɗi masu uban yawa ba fata ba azo a samu matsala".
Ya kuma yin shiru na kusan minti uku yana sauraron na cikin wayar kamin yace,"Ehh ai shi ne abun dubawar da na ke faɗa maka. Ka san girman Allah Alhaji Sunusi kwata kwata ba zan ce maka ga ta inda nayi asarar waɗancan kuɗin ba, duk buge bugen lissafi da bincike wallahi na rasa ina miliyan ɗari da hamsin ta shiga, to amma ka san kowanne bawa Allah na jarabtarsa, na bar hakan matsayin ƙaddara sai adu'an Allah ya mayar min da alkhairi, ƙila wani mugun abun ne ma yake shirin faruwa da ni sai Allah ya kare hakan lamarin ya sauka akan dukiyata".
Ya ƙara yin shiru sannan yace,"Amin ya Hayyu ya Qayyum, kaga har yanzu wallahi cikin iyalina da iyayena babu wanda na faɗawa, bab na so su shiga damuwa, ni kaina haka dai ina rayuwa ne kawai, tunda ka san duk wata ɗawainiya ta ahalina akaina yake, ƙannena da kowa nawa da ni suka dogara, idan suka ji cewan na rasa komai nawa zasu shiga tashin hankali...Amma dai mahaifina zan sanar da shi a yau ɓoyewan bai da amfani, muna da su a raye dole mu buƙaci adu'arsu, ta hakan Allah zai ɓullo da mafita. Yanzu ka nemi waɗanda zaku yi maganar sayan waccan plazar ta Kabuga, ka san ita kaɗai ta rage min dama, a ciki na ke so na fitar da kuɗin da za'ai wa mahaifiyata aiki sauran kuma kaga sai a wari wani abun da ko shago ne a buɗe kafin su banki su bamu aron kuɗin sai a tayar da kamfanin shinkafar".
"Yauwa na gode fa, ina godiya sosai da sosai Alhaji Sunusi, Allah ya bar zumunci. A gaida iyalin".
Daga haka wayar tasa ta ƙare ya ajiyeta gefen gado, laptop ɗin ya kashe kana ya shiga tattara takardun gabansa yana shirya su. Sai bayan ya gama ne ya ɗauki wayarsa ya danna lambar Yaya, ta ɗaga yake tambayarta sauƙin jikin Iyam tace masa kamar dai kullum don yauma ko buɗe ido bata yi ba, yanzu ma take shirin ta kira shi sun jisa shiru yau bai leƙo ba.
Da muryan bayyana tarin damuwa yace mata,"Na ɗa tashi ne da uzuri amma jimawa kaɗan zan leƙo, ko da Iyam ɗin zata farka ta tambaye ni kya ce mata lafiya lau ba wani matsala aiki ne ya ɗan tsare ni".
Yayan tace,"To shikenan".
"Jiyan da ta farka ta samu taci abinci kuwa?".
Yaya da ke kusa da Iyam tace,"Wallahi bata ci ba, ta dai ce tana son ferfesun kifi to kuma kaga dare yayi a lokacin, ka ma fa san likita É—azu da ya zo ce yay sai an saka mata robar abinci".
Ya furta kalmar innalillahi yana jin wani gumi na tsatstafo masa, duniyar gaba ɗayanta yaji ta ƙara yi masa nauyi aka. a sanyaye yace,"Allah ubangiji ya kawo mata sauƙin da ba za'a kai ga hakan ba, yanzu bara na kira Lubabatu sai na tura mata kuɗi tayo cefane ayi mata ferfesun, ƙila idan ta farka ɗin ta samu ci, yanzu ma dai zan gaggauta na taho".
Tace,"To shikenan. amma ya ku ke ciki da maganar iyayen Zahra'un?".
Ya sauke numfashi kana yace,"Yaya lamarin na su dai sai haƙuri, amma ni na faɗa musu ina kan bakana babu wanda ya isa ya raba ni da abin da Allah ya bani".
Itama ta numfasa murya a hankali tace,"To Allah ya kyauta, amma lamarin nasu akwai son zuciya da rashin addini, yanzu dai kai zaka ta iya bakin ƙoƙarin ka shawo kan matarka kasan mu mata akwai daru idan lamari irin haka ya tashi, sai an ta faman lallashi tukunna".
Ya shafi kansa da cewa,"Ai Yaya Zahra'u ma gaba ɗaya bata jin wani rarrashi wallahi, shiyasa na faɗa mata idan ta gaji ne to ta faɗa min kawai na sawwaƙe mata, ni ba zan iya da wannan tashin hankalin ba, rabona da samun kwanciyar hankali a cikin gidan nan wallahi Yaya har na manta, idan na tuna ma abin da na miki kan sharrin da tayi miki kar kiji yanda raina ke sosuwa".
Yaya tace,"Allah ya kyauta wancan kuma ai ya wuce, hannunka bai taɓa ruɓewa ka yar, ciki guda muka fito kuma na fika hankali da shekaru da sanin yakamata, kaga ni ba zan bari zumuncinmu ya taɓu ba.... Yauwa jiya muna magana ma cajin wayar tawa ya ƙare sai yanzu zancen ya faɗo min, Kai Nazifi me ya shiga cikin kanka har kake tunanin dawo da Sa'ida gidanka?".
Yay shiru bai ce komai ba. Ta sake cewa,"Magana na ke maka, kai kace kana neman shawara ko ba haka ba".
Ya murza goshinsa kuma haka kawai sai yaji wani abu ya motsa a ƙirjinsa kan yace,"Kawai dai Yaya na ji ne ina so na dawo da ita ba tare da sanin dalili ba".
"To wallahi ka sauya tunani ka yiwa kanka faɗa, me ya kai ka? Allah ya rabaka da ƙaya kuma ka ke neman sake janyowa kanka masifa, yo masifa mana zama da wadda bata haihuwa duk da Allah ya baka me haifa maka yanzu, to ni dai in har na kai na baka shawara ka cire tunanin dawo da ita, in ba haka bayan kashe maka ƴa da tayi ta dawo wannan karan zata ƙarasa kashe maka mahaifiya ne kaima kuma ta kassaraka ta barka gaya, don ba zaka yi aune ba zata kwashe duka dukiyarka tun da dai bata haihu ba".
"Tom shikenan Yaya, dama daÉ—in shawarar kenan, ni ban yi wannan tunanin ba. sai na shigo asibitin".
Suna gama wayar ya kwantar da kansa jikin filo yana kallon saman ɗakin, zuciyarsa cunkushe take yana ta aikin tunanin yanda zai samu mafita, mafita akan abubuwa da yawa da suka tsaya masa yanzu ciki kuwa har da son dawo da Sa'ida, ita ɗin kuma hr yanzu ya kasa gane dalilinsa na so ya dawo da ita gidansa, duk da cewa da yaje yana faɗawa Yayan Shago cewa ya taimaka ya shige masa gaba kan shawo kan iyayen Sa'ida ta dawo gidansa, Kai taye Yayan Shago yace shi kam ba da shi ba, ai dama ba'a sanin darajar abu sai an rasa shi, ya kasa gane Sa'idan na da muhimmanci a wurinsa sai yanzu ne saboda bai da kunya bayan duk irin wulaƙancin da yay mata sannan zai ce zai dawo da ita.