Sashe 4
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shima cikin nuna jin daɗin adu'ar tata yake ta amsawa da amin. Yana daɗa gaya mata yanda tsarin shagon nasu yake, kayan kwalliya ne da kayan jarirai a ciki. A ɓangarena kuwa bayan farin ciki har da tausayinsa naji ya kama ni, don kusan wata uku kenan yana fafutukar neman abun yi don tuni jarinsa ya karye, yanzu babu sana'ar da yake, yana gida kullum sai dai ya fita ya sha iskar gari. okacin da Abbaa ya siyowa Yaya Al'amin ice har da shi ya raba musu, amma shima yanzu babu, idan yana bani tarihin rayuwarsa a irin gwagwarmayar da ya sha har ƙwalla na ke yi masa saboda tausayi, namiji ne shi mai ƙokarin neman na kansa sai dai ubangiji bai saka masa nasibi a nemansa ba, yana da jajircewar neman amma kuma da ya fara sai abu ya lalace masa, in jari ya zuba sai ya karye, haka idan kasuwa ya fara zuwa sai wani abun ya gifta kasuwancin ya lalace, idan tafiye tafiye ya soma zuwa garuruwa itama sai tafiyar ta tsaya masa, sau tari wani aikin shine silar nema musu shi da ƴan uwansa amma kowannensu sai ya samu ci gaba shi kuma sai dai koma baya a kullum, kai a taƙaice ma idan yasa hannu a kasuwancin da ba nasa ba sai kasuwancin mutum ya lalace, shiyasa yafi gane duk abin da zai yi ya kasance nasa ne na kansa, har ya kan ce ina ma ace yayi karatun boko ko da iya sakandire ne wataƙila da ya rage zafi, to amma a hakan ma Alhamdulillah tun da a ɓangaren addinin da zai je lahira da shi babu ta inda aka barsa, kuma ya san komai lokaci ne yana adu'a haka iyaye suna masa.
Bayan sun gama magana da Ummani ta miƙe tana ce masa,"Bara in yi na kammala girkin nan ka tafiwa da Ƙawata tuwon nan kaima kuma ka samu ka ci".
Har ta nufi kicin kuma sai ta dakata tana ce masa,"Kaga kuwa ma yau idan ka ci gyaranta a karatu wallahi ka zaneta don jiya yawo ta kaÉ—a suka tafi da Æ´an islamiyarsu, taja min faÉ—a a wurin Abbaanku".
Da sigar tsokana na ce,"Ai Yaya da har zamu biyo maka ma sai Safiyya tace muna zuwa zaka fara mana wa'azi".
Sai naga yanayinsa ba kamar yanda muka saba da shi ba, banda haka da yanda nayi maganar nan ai ya bani amsa daidai da maganata, haka yake shikam wajen zaro maida martani, ka faɗi ɗaya ya faɗa maka talatin, ga iya baƙar magana me saka cikin mutum ya ƙulle saboda dariya. Gyara zama nayi na fuskance shi sosai, domin kuwa idan har na gansa a irin wannan yanayin to akwai matsala, domin shi ɗin mutum ne me raha, in har ka gansa saɓanin walwala to tabbas akwai damuwa babba, imma ciwon ƙafar Iyam, imma kuma a gida babu abin da za'a ci sai idan kuma ya fita yay buga bugarsa ya rasa abin yi.
Kallonsa na ke sosai da nazarin son fahimtarsa, na san babu ɗaya daga cikin abubuwan da na ke tunani, idan Iyam ce jikinta ya tashi shigowarsa za su yi maganar da Ummani, aikin yi kuma yanzu yake murna da mana albishir ɗin ya samu wajen sana'a. To mene matsalar? Hannu na saka na firfita idonsa ya ƙirfta daga kafe wuri ɗaya da yay.
"Yaya lafiya dai?".
Yasa hannu ya shafi fuskarsa yana cewa,"Lafiya lau, É—auko kayan karatun na ki da sauri ina da uzuri".
Kallonsa kawai na tsaya yi, sai ya juyo yana kallona, fuskarsa babu wani annuri ya ce,"ba ki ji ba ne?".
"Naji Yaya, kawai na damu ne da canjawar yanayinka cikin ƙalilan ɗin mintuna, kuma sai zuciyata yau duk bata yarda da lafiya ɗin da ka ce ba".
"Yanzu dai É—auko littafan muyi abin da ya kamata".
Na miƙe jiki a sanyaye na wuce ɗaki, na dawo da jakar littafaina sanye kuma da hijabina. Dardumar da na zo da ita na shimfiɗa nayi zaman karatu ina mai fuskantarsa. Bismillah ya fara muka shiga karatun, ina jin daɗin karatunsa sosai, duk daƙiƙancin mutum ya ɗauki darasi a wajensa sai ya iya kuma sai ya zauna a kansa, bai yi min wani ƙari me yawa ba naji yana rufewa da adu'ar tashi, nayi saurin cewa.
"Yaya ko rabi fa bamu yi ba, kuma yau littafi É—aya za'ai?".
"Ehh gwara muyi kaɗan ba zan so shiga lokacin wani". Sai kuma ya kalli agogon ƙurƙurar wayarsa da nake tsokanarsa da ita, ba tare da ya dube ni ba ya ce,"Ƙarfe Biyar da rabi yanzu, duk inda ya ke yana kan hanya sai ki shirya".
Furucin nasa yasa na ware ido ina kallonsa da kyau, sai duk naji zuciyata babu daɗi sam, na san yana yi min tuni ne, domin tuntuni yace na ɗaukar masa alƙawarin ba zan tsaya ina bawa wani namiji fuska ba, ba zan tsaya kule kulen samari ba, kuma ba zan tsaya zance da duk wanda ya zo wajena ba. Kuma waccan shekaranjiyan kawai sai ya zo ƙofar gida ya taradda ni da baƙo, dama tun a lokacin da naga yanayin yanda suka gaisa da baƙon na san bai ji daɗin ganinmu tare ba, nima kuma bai san ba'a son raina ne har na ke tsaye da baƙon ba.
Hasalima ranar ne na fara ganinsa kuma bisa umarnin Kaka, shi ɗin Yaya ne a wurin Safiyya don ɗan Yayar Ummansu ne, Saurayi ne ba wani babba ba, Air force ne yanzu haka yana cross river can yake aiki sai lokaci zuwa lokaci yake leƙowa ganin iyaye, Wai ya ganni ranar mun je gidan su Safiyya, shine maimakon ya fara tuntuɓata kawai sai ya tafi wurin su Kaka kai tsaye, kuma zuwan ma ba shi kaɗai ba har da manyansa, Abbaa ya gaya masa cewar yay haƙuri ya sanar da su gaskiya akan ba yanzu zai aurar da ni ba, amma sai ce yaji ya amince zai jira zuwa duk lokacin da aka ɗiba masa, shima dama ko da auren aka yi yanzu zai barni nayi karatuna ba zai hanani ba ko da ace aiki ne ma, Kaka yace to shikenan sun ba shi, amma da sharaɗin babu waya babu zuwa zance har sai lokacin da aka ba shi izini amma ya san da cewa kam sun basa Sa'ida, Ya ce ya yarda ya amince, Wan mahaifinsa ya dage akan za su bada kuɗin aure, dole haka aka karɓa naira dubu ɗari ba don son ran Abbaana ba sai don amincewar Kaka.
Shine ranar ya zo gida wai na gansa, Safiyya sai wani faman koɗa min shi take wai na yarda ai auren ana yi sai ƙasar da na zaɓa, kuma mahaukacin kuɗi ne da shi, yay bala'in iya soyaya, waye waye ɗinta dai, ni har ta ban haushi ma na ce ita me ya hana ta aure shi, sai ce tayi ai don bai ce yana sonta ba ne, da yace yana sonta da naga yanda ake auren miji na kece raini.
Ni dai ranar da kukana na fita, fuska babu yabo babu fallasa muka gaisa da shi, tashin farko kuma tambayar da yay min wai in faɗa masa yayi min zan iya aurensa? Idan ba zan iya aurensa shi ba zai shiga hakkina ba zai haƙura yabawa wasu dama, ko da naga ya fara magana da iyaye saboda hakan shine mutuncinsa, amma ko kuɗin aure da aka bayar dama an bada ne bisa sharaɗin idan nace bana sonsa za'a mayar masa da kayansa.
Ni dai kai na ɗaga masa na amincewa kawai, don ko fuskarsa ma ni ban tsaya ƙare mata kallo ba, abu daya zan iya cewa fari ne me matsakaicin tsayi, muka gama gaisawa sama sama yana ta faman gabatar min da kansa da tarihinsa, yana aikin min tambayoyi. Ni da ina ta jinsa kawai zuciyata a matse babu daɗi, to amma ya zanyi! ni ko da naji waye shi na kuma gansa a gabana ko kaɗan ban ji bana sonsa ba, haka ban ji ina sonsa ba, ni dai kawai na san da cewa ina ƙaunar zaɓin Abbaana, kuma zan koyawa zuciyata son zaɓin Abbaana ko da ace zan cutu, ko da zan mutu ta silar hakan. wannan alƙawari ne da na ɗaukarwa kaina ba tun yanzu ba, na shirya zama da duk wanda Abbaana ya zaɓa min matsayin mijin aure ko da ace ina da wani wanda na ke mutuwar so a gefe, to balle ma yanzun babu kowa da na ke so a zuciyata, babu wani da na ke hasashen aure, don haka na san da sannu zuciyata zata amshi soyayyar lieutenant Salim Sadiq Oluwa.
Idanuwana suka yi nayi narai narai na shiga wallacewa Yaya Nazifi,"Allah Yaya ko ranar da ka zo ka taradda mu ni ban san da zuwansa ba, ina zaune ne fa kawai Kaka ya ce naje waje ina da baƙo, ina jin nauyin faɗa maka ne shiyasa amma na san Ya Imam zai maka maganar".
Kansa ya gyaɗa alamun yaji, bai ƙara cewa da ni komai ba nima nayi shiru ina jin kamar zan saka kuka. Sai bayan wucewar kusan minti goma kana ya kalle ni ta gefen ido yana sosa gemunsa ya ce,"Ki yiwa Ummani magana zan wuce?".
Na maƙe kafaɗa ina cewa,"To Yaya ai kana fushi da ni".
"Fushi kuma akan me".
"To Yaya idan ba fushi ba, ɓacin ran saman fuskarka na menene?".
"Kar ki damu Ƙanwata, kawai dai banda muhimmanci ne yanzu a wurinki, matsayina kuma ya canja tun da kin samu abokin rayuwa...".
Ji nayi kamar in kai hannu na toshe masa baki, amma babu damar hakan.
"Kayi haƙuri don Allah Yaya, kai fa Yayana ne muna tare har abada, kai me aurar da ni ne, kuma ni wallahi Allah matsayinka bai canja ba a wurina...".
"Ya kike wallacewa bayan ga zahiri, idan da ne ai duk yanda ake ciki kafin ki fita wajensa ma sai kin kira ni kin faÉ—a min, karo na farko da ba ki nemi shawarata ba, ai shikenan na gode".
"Kayi haƙuri Yaya don Allah, ba ni da wani zaɓi ne. Amma ai kace kai zaka tayani zaɓar mijin aure, idan bai yi ba shikenan".