Sashe 10
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ana haka kuwa yazo min da zancen mahaifiyarsa ta ba shi aron gidanta da ta zuba ƴan haya a ciki, sai dai akwai gyare gyare a gidan sosai don ko masai sai an ƙara haƙansa, ban da gyaransa rufin kwano da su simintin ƙasa da duk ya farfashe. Amma yanzu dai zai yi iya duk ƙoƙarinsa yaga ya haɗa lefen kafin sati biyun da Abbaa ya yanke, in ya so ko wurin Hamisu ne sai ya ari kuɗin, Ranar yay ta bani haƙuri da lallashina akan in kwantar da hankalina komai zai zo cikin sauƙi, kuma in sha Allahu ko don hallacin da na masa ba zai bani kunya ba....
_____________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ÆAUNA*
Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA*
Halimahz
*LOKACI NE*
Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo
*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200
*Biyan KuÉ—i Ta*👇ðŸ»
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇ðŸ»*
09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR05FT5*
_Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._
__________________________________
Tun daga ranar da Nazifi ya buƙaci da na siyar masa da kwanana ya ɗauke ƙafarsa daga gare ni daga inda na ke, rawar ƙafa kawai yake a wurin amaryarsa, sai shan soyayyarsu suke hankali kwance, wani abun ma na lura da gayya yake min shi, yanda yake faman rawan kai ka rantse aurensa na farko kenan.
Sam ba ya ko waiwayena balle tunanin sauke hakkina, bai damu da ya lafiyata take ba haka bai damu da dukkan wata buƙata tawa ba, ya barni kawai da ɗawainiyar gidansa, yaransa da ɗawainiyar mahaifiyarsa da ke mini kallon baiwa, wacca kowanne kalar kashi ta kwaso ni take watsawa, gaba ɗayansu basu ko tunawa da hakkin cutar da ni da suke yi.
Haka har aka cika wata guda ɗin da na ɗibar masa amma mutumin nan bai yi aiki da hankali da tunanin ba, bama za'a sa ilimi ba don yanzu ni bana saka shi sahun masu ilimi kam, ranar da naje ɗaki na same shi ya na ta faman ɓata rai da cin magani saboda ya baro ɓangaren Amaryarsa, abincin ma da na kai sai ce yayi ai ya ƙoshi, ni dai ina ta bin hanyar da zata sa ba zamu samu saɓani ba amma shi neman hanyar ayi tsiya kawai yake, ni kuma ganin hakan kawai na bar masa ɗakinsa na koma nawa, tun sannan na fita sabgarsa na ce idan anyi duniya don manzon Allah bani ƙara zuwa inda yake sai idan ya neme ni, ashe shi hakan ma yake so don bai ko nuna bi ta kaina ba, ganin na fita harkarsa ya tattara ya koma wurin amaryarsa gaba ɗaya, maganar dole idan ta kama zai aiko min message ne kawai, ni kuma idan ina buƙatar abu mahaifiyarsa na ke faɗawa wanda kafin a bani ma ko a faɗa masa sai na sha jiki.
Wannan abubuwa suka ƙara gwada min da gaske Nazifi ba ya buƙatata a rayuwarsa sam, zaman dole kawai yake da ni, wanda kuma na ke ta nazari da tunanin dolen da ta gagare shi fitowa fili yace da ni ya sallama auranmu, domin kuwa yanda ya gaji da zama da ni haka nima na fishi gajiya da zama da shi.
Gaba ɗaya ya mayarshe ni wata banza shara a cikin gidan, ya gama tsinka darajata da mutuncina a wurin matarsa, Munafukin miji wama ya san me ya gaggaya mata akaina, tun da ta kai ta kawo yanzu tsakanina da ita ma kallon banza ne musamman idan ta fita aiki ta dawo, da zarar ta ganni sai kallon raini da ƙasƙanci saboda mijinta ya nuna mata ni ɗin ba komai ba ce a gare shi, don haka take wani nuna isa da gadara matsayinta na wadda miji yake so yake bawa kulawarsa, yake kuma ji da ita.
Ni dai basa ko gabana tuni na É—auke ido akan su, harkokin gabana kawai na ke yi. Abinci ne zan girki iya cikina da na mahaifiyarsa da yara, shi da ita kuwa dama takeaway yake musu ne oho ni dai ya min text yace na bar girki da su.
Kuma tuni na yiwa kaina karatun tanatsu, na kira Ummani muka tattauna akan shawarar da na yanke, ya kamata na kama sana'a wacce nasan in har Allah ya saka min albarka da ganin ina samu ma kaɗai Nazifi ya rage wulaƙanta ni, yanzun ma ai har da ganin cewa shi yake min komai shiyasa, kuma duk abin da na ke buƙata sai na jira shi dole kuwa inga walaƙanci kala daban daban.
Saboda haka na tattara duk gwala gwalaina guda uku muka je kasuwa aka auna aka siyar da tsada sosai, ina batun saro kaya irin su atamfofi da danginsu Maman Yasmin tace a'a tunda kuɗin har za su kai a siya fili to gwara a siya min filin na ajiye shi zuwa wani lokaci sai a ɗaga a siyar tunda ba kuɗin gini gare ni balle na gina, amma wannan zan ta iya juyawa da ribar ma sai in dinga ƙara siyan ƙasa ina ajewa, amma idan nace kasuwancin cikin gida zan yi to Nazifi zai iya min muguntar da zai dakusar min da shi, wannan kuwa bai ji bai gani ba kuma kar ɗokin soyayya wataran tasa nayi suɓutar bakin faɗa masa.
Ai kuwa da wannan shawarartata ne Ummani tasa Yaya Al'amin ya samo dillali aka siya min wani fili can unguwar rimin auzinawa, da yake can akwai arhar filaye, tace da shi ko Abbaa kar ya bari ya sani zata faÉ—a masa idan lokacin hakan yayi, nima kuma naja bakina nayi shiru ko da wasa kar Nazifi ya san da zancen siyar da gwala gwalai balle siyan fili, takardun filin kuma zata ajiye min su a wajenta.
Ranar da farin cikina na dawo gida, ko babu komai yanzu ina da kadara a ƙasa, karatuna kuma da ya tauyen hakkin ci gaba, ya kuma hana ni kuɗaɗen da mahaifina ya bani domin biyan kuɗin makaranta yaje don kansa Allah ai ba azzalumin bawansa ba ne. Sai dai na samu ajin online da ake koyar da turanci da kuma ajin biology, nayi register na shiga domin hakan zai fiye min alfanu, gwara na nemi ilim ta waya akan ya zama kullum sai dai na saka data na hau nayi chart da kalle kallen tictok a banza a wofi ni ban ƙaru da komai ba, ga shi kuma koyawar da ake babu mugunta darasi ake sosai in har ka natsu ka mayar da hankali ba zaka ce a online ne ka ke karatu ba, jinka zaka yi tamkar a cikin makaranta zaune a aji gaban Malami.
Yau ina ɗaki da yamma zaune ni da Rumana, yanzu kam ta zama ƴar ɗakina, Atika kuma ta zama ƴar ɗakin Zahra'u. Ganin lokaci na miƙe na fita don zuwa haɗa abun shan ruwa, ina sakkowa Nazifi na hayowa shima wanda ya dawo daga kasuwa. Nayi kamar ban gansa ba don tuni na ƙuduri aniyar zai sha mamakina, tabbas ko magana ce idan ba shi yay min ba ba zan masa ba, gaisuwa ma bana so ta haɗamu.
Hanya na ba shi don ya wuce sai na ga ya tsaya, ganin bai da niyyar wucewa naci gaba da takawa ina sauka ya dakatar da ni.
"Me ke damunki ne Sa'ida? Za ki ce ba ki ganni ba ne da sannu da dawowa zata gagara fitowa daga bakin ki, kina nuna tamkar ni ba mijinki ba ne".
"To Nazifi sannu da zuwana zata ƙare ka da wani abu ne da ka damu da ita? Ko ba'a faɗa maka ne a inda ka nufa".
"Ni kike faÉ—awa haka?".
Ya faɗa yana ɗaga murya sama, ni ko ganin zai min hargowa nayi masa banza na wuce na barshi anan. Bai san ni baƙin cikin ganinsa ma nayi ba da har yake kiran nayi masa sannu da zuwa, ni kuwa yanzu ina yaga wannan darajar a idona, ai ana zaman jinginar aure ne kawai tsakanina da shi, kuma ban fidda ran zuwan lokacin da zai ce ya raba aurenmu ba.
Har na shiga kitchen ina jin yacca yake bina da kallo, dama kunu na sakko na dama saboda ina azumi, kuma ma sai naji ina sha'awar awara don haka na koma sama na É—auko kuÉ—i na dawo na bawa Æ´ar aikin Zahra'u ta siyo min É—anyar awara a waje. Har aka sha ruwa ina kitchen ina aiki sai sauri na ke yi.