Sashe 85
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tasowa yay ya zo gaba daf da ni ya tsaya, nayi saurin sunkwi da kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuna, idan na gansa gabana irin haka daf daf duk sai na nemi na ruɗe in kasa fassara irin yanda na ke ji a tare da ni.
Ban ankara ba naji hannunsa cikin nawa, da sauri na nemi na zare ya hana hakan, nima kuma sai na tsinci kaina da hana ƙwacewar, sai dai murya can ƙasan maƙoshi nace da shi,"Kasan fa babu kyau, idan kayi haƙuri kwanaki kaɗan suka rage".
Bagarar da maganar tawa yayi da cewa,"Baby ina kika je aka sauya min ke haka? Kinga kyan da kika yi kuwa, ga rigar tayi fitting ɗinki, Baby faɗa min sirrin me kika samu da a kwana tara kika ƙara fidda shape".
Sai yay shiru yana cewa,"In faɗi wani abu?". Sai na masa wani kallo don idan yayi irin wannan muryan na tabbata zai min katoɓara ne, ile kuwa sai ce yay,"Naga twins ɗina ma sun ƙara cika, ko wani abu kika sa suka ɗago don ni dai ba a haka na tafi na bar su ba".
Dukan wasa na kai masa yay saurin ja da baya yana dariya, ya tsare ni da tambayan lallai alalla sai na faɗa masa me na sha na daɗa cika gaba da baya, ƙwayar idona ma har haske ta ƙara yi. Ban iya cewa da shi komai ba kamar yanda na kasa wani ƙwaƙwkwaran motsi dalilin yanda na ke jin yana kewaya babban yatsansa akan tafin hannuna, sai naji ina neman fita a hayyacina na haɗiye yawu ina rumtse ido.
Na ƙware wajen buɗe baki nace masa,"Salim ka bari".
Ai ban ida rufe baki ba ya sauke min mintsine a weast ɗina. "Ya sunana?". Dariya na ƙyalƙyale da ita dalilin cakulkulin da ya sakar min, na manne jikin bango ina cewa,"Salim sunanka". Ganin yana neman yi min rumfa na rumtse ido da kyau ina marairaice murya da cewa,"Kayi haƙuri ba sunanka haka ba, sunanka Lieutenant Onochie, kuma fa kaga kar wani ya zo wucewa".
"Ina ruwana ke za ki ji kunya ai, ni dama a ƙage na ke a bani abata na tafi, dama hotel ɗin da muka sauka idan za ki kwana kina ihu babu me kawo miki agaji".
[2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR08FT5*
Na aje wayar saman fuskata ina faman fitar da murmushi kamar sauna, sai daga bisani kuma naji raina ya ɓaci na kama jin haushin kaina, sai kace wata shashasha ma a soyayyar, ina neman zaƙewa daga ance ana sona sau ɗaya, to shi dama haka ma yake no text no call? Soyayyar ce bai iya ba ko kuma salon tasa kulawar kenan? Ko kuma ya gamata akan matarsa ta farko? Rashin nemana da bai yi ba fa tun zuwan farkonsa ya bani haushi sosai, don har ce nayi yana da girman kai, yana nufin kenan ma ba zan ja ajina ba tunda ni ba budurwa ba ce, sai yanzu da wani karkataccen bakinsa zai kira ni yana Baby, a'a Bebo.
To ni ina son miji me raha da zamu zama abokai bana son me ɗagawa, in ma zai sauke abinda ke kansa ya sauke, idan ba zai sauke ba yaje can ya nemi ƴar uwarsa ƙabila ko wadda zata iya da halinsa, Numbernsa na ƙara kalla da kyau don ko ya kira ba zan ƙara ɗagawa ba ehe, kar yaga ya kira ina ta wani zumuɗi ya zaci sonsa na ke yi.
Ummani tace,"To ke ya kike ganin za'ai da waɗannan kuɗin? Dukka lefen miliyan ɗaya da rabi za'a haɗa miki? Ni fa kawai nayi shiru ne gudun faɗan Abbaanku, shi yana batun gwara ayi miki kaya na gani na faɗa kar su ce sun bada kuɗi masu yawa an riƙe. amma ai kuɗin ne sun yi yawa, a dai haɗa ko na miliyan guda ne, ke ni miliyan ɗin ma a wajena tayi yawa wanne sutturu za'a siya har na miliyan, ba gwara a raba biyu sauran a haɗa da wancan a bawa Sale kafinta yay miki kaya masu kyau".
"Kawai ma da zai dawo ya karɓi kuɗinsa da yafi". Na faɗa cikin muryar da ke shaida faɗa faɗa, ina ta gungunin masifa na ƙorafin yanda ma ya raina ni.
Ta ce,"Uhmmm daga baya kenan, ni bana son gulma".
Sai na sami kaina da ɗagowa in kalleta, na buɗi ba ki nace,"To Ummani sai ka kama auren wanda bai san kulawa ba balle haƙƙinta, kuma ba zai ke nuna maka da gaske yana sonka ba saboda yana ji da kansa". Harar da ta galla min yasa na sauke kai ƙasa ina ci gaba da masifata ƙasa ƙasa.
Lokacin Maman Yasmin ta shigo tana tsokana na da,"Amarsu".
Gaisheta kawai nayi ban ko ɗaga kai ba, Ummani tace,"Ƙyaleta". Suka shiga gaisawa Maman Yasmin ɗin na cewa,"Abban Yasmin yace min kina nema mana".
Ummani tace,"Ehh dama ce nayi ke da Nafisa ku zo ku shiga kasuwa ku haÉ—o kayan lefen nan, kunga wata guda kamar yau ne gwara ayi abu a tsanaki, gata nan ita É—in kuma idan zata biku to".
Maman Yasmin tace da Ummani,"Tom shikenan, amma kinga ko za'a yiwa Mrs Arab magana a faɗa mata ga na iya adadin kuɗin da ake so ta haɗa, mu bar mata zaɓi nan da kwana uku za kiga ta haɗo su har akwatuna, kuma wallahi tayi masifar sanin makamar iya haɗa lefe, mayan bikin nan da ake duk ita ake bawa kwangila".
Ummani tace,"To idan kin san dai babu wata matsala ai sai ayi mata maganar ko".
"To shikenan bari a kirata ma yanzu, ke Sa'ida rubuta lambar wayata babu kuÉ—i, ai shegun kaya zata haÉ—a miki, da muka je bikin Surayya duk shegun less É—in da kika ga tana sakawa ai ita ta haÉ—a lefen".
A ƙasan raina na ce ehh fa shigar Amaryar tayi kyau babu ƙarya. Na ɗau wayata ina,"Karanto lambar". "Oak, 07037599677". Ina gama dialling nayi saving da Mrs Arab Kano.
Kiran lambar ya tafi na miƙa mata ina tashi na fita, ruwan wanka na ɗora kana na koma ɗaki na ɗakko wani ɗinki da zan ƙarasa haɗawa, masu shi na ta kirana na gagara ƙarasa musu.
Ƙarfe uku na fito a shirye don tafiya wurin aiki, tun uku saura na ke ta ganin kiran Salim na shigowa nayi biris naƙi ɗagawa, har aikowa yayi nayi saurin kora ɗan aiken kar ma Ummani taji. Na shiga ɗaki na yiwa Ummani sallama bayan ta min adu'a na fito, da zuwana soro kiran Maman Khairi ya shigo tana tambayana su siya min jugs ɗin tangaran yafi yawa ko kuwa? Nace ni na bar musu zaɓi kawai, tun ɗazu ta zo suka fita ita da Maman Yasmin yo siyayyan kayan kitchen lefen kuma kamar yadda ta faɗa ne sun gama magana da Mrs Arab zata haɗo komai ta kawo, ina jin Maman Yasmin na faɗin don Allah ta haɗa akwatu set uku, ni dai kam mun yi dacen sirikai don Matan Yayyuna kamar ciki guda muka fito, yanda Ummani ke yabon su haka suma suke yabonta ko ina suka shiga sai sun ce su kuwa babu abinda zasu ce da Allah sai godiya domin ya basu suruka ta ƙwarai wadda ta ɗauke su babu banbanci da abinda ta haifa, kuma babu takurawa sam a al'amuranta, to nima dai bana kukan rashin Yayyu mata don sun maye min gurbinsu, sai dai nayi kukan rashin ƙanne mata kawai.
Ina fita ƙofar gida nayi kiciɓis da mutum tsaye bakin mota shi da Yaya Al'amin, yadi ne jikinsa baƙi yay masifar masa kyau, duk yanda na so nayi masa kallo ɗaya hakan ya faskara sai da na ƙara kallonsa, Allah masanin ta inda farinciki ya samu damar lulluɓe ni, a ƙasan raina nace yay kyau kamar ba ƙabila ba, har wani kishinsa naji ya lulluɓe ni ganin ƴan matan layinmu na ta wucewa islamiya.
Na kalla screen ɗin wayata da kiransa ke ƙara shigowa a karo na babu adadi, sai na ɗaga ido na kalle shi naga ni yake kallo yana jijjiga kai, hakan yaso ba ni dariya amma na fusge, hankalinsa ma ya dawo kaina gaba ɗaya ya bar Yaya Al'amin can yana ta faman zuba shi ɗaya.
Na sha murr na ɗauke kai kamar ban gansa ba, na ɗaga ƙafa zan tsallake na wuce a sumame kar Ya Al'amin ya ganni, aikuwa daidai nan naji yana cewa da ni,"Ke Sa'ida ba ki gan mu ba ne".
"Yaya kaina na ƙasa ban kula da ku ba". Na faɗi sa'ilin da na ke ɗaga ido na kalle shi zan harare shi, sai kuwa na kasa aiwatar da hakan dalilin ƙayattacen murmushin da ya sakar min wanda ya samu shiga har cikin ɓargon jikina, ga wani munafukan dariya da ya danne a saman leɓe.
Ina ta ciccin magani haka na shiga motar, wai wai tunda uwata ta haifeni ban taɓa shiga mota me haɗuwa da tsada irin wannan ba, sai na zama kamar ƴar ƙauye har wani taɓa kujerun na ke yi da ko cire su a leda ba'ai ba, duk yanda aka yi sabuwa ce fil ma.
_"idan kika yi fushi da ni masoyiya hankali zaya tashi idanuwa su yi kuka, ki taimakawa soja kar ya zamo ragon namiji ai masa dariya"._
Haka ya shigo motan yana rera waƙar, da zummar in caccake shi da tsiwa amma ba shiri dariya ta ƙwace min har da sarƙewa, sai tari kwaf kwaf yay saurin miƙo min ruwa, na karɓa na sha idona har ya cika da ruwa tsabar dariya. Na miƙa masa goran ya galla min harara da cewan,"Kina wa me dariya?". Sauran dariyar na danne ina ɗauke idona a kansa idan ba haka ba tsaf zan ci gaba da dariya na zama kamar zararra.
Ganin bai da niyyan tashin motan na karkata ina dubansa na ce,"Please kar na makara".
Fuskansa a ɗaure yace,"Ba kina wa waƙana dariya ba".
Nace,"Ayya sorry ba waƙanka na ke ma dariya ba".
Sai ya jijjiga kai yace,"Akwai ranar ƙin dillanci, tara ki kawai na ke za ki shigo hannuna, har ni za kike ganin kirana ki ƙi picking, kuma ma tsawon sati guda ba za ki iya kirana ki ce kin yi missing ɗina ba kina sona".