Sashe 90
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kalaman nata suka sanya jikina yin sanyi. "To an aje min abin karyawa?".
"Sai dai ki leƙa gidan Yusra idan kin samu to, in ba ki samu ba kuma ki siyo indomie ki dafa, kunun ma da aka yi babu inda yaje, kinga sai Umman Hindatu ce ta kawo awara aka ƙara da ita".
"Bari kawai idan mun je can na siya wani abun".
Umman su Hindatun na cewa ko zan shiga kicin na dafa wani abun nace mata a'a bara naje gidan Maman Yasmin ɗin ba za'a rasa a can ba, muka wuce ni da Hindatu, naji daɗi sosai itama ta kawo min gudunmawar zannuwan gado guda biyu da jug ɗin roba. Ita na bari tana kimtsa min wasu kayana da zan ƙarasa haɗawa, lokacin da na fito a wanka ma har ta kammala, sai ga ɗakin yay fayau, jikina ya ƙara yin sanyi ganin da gaske dai barin gidan zan yi, ina son ɗan ƙaramin ɗakin nan nawa fa, na gama shiryawa na fito na tafi gidan Maman Yasmin ni da Hindatu.
Ai tun a ƙofan gida yara suka tsare ni Anty Sa'ida kuɗin party, sai arar kuɗin nayi hannun Hindatu na ba su don ko sisi bana magani, sauran kuɗin da na ke tattalawa na rabarwa dangin Nazifi jiya, na nemi suna hankalina ya kwanta, ko da yake ba faɗuwa ba ne taimako nayi har zuciyata saboda Allah, kuma Allah zai ninka min ya kuma bani lada.
Ban samu abincin ba sai wata guntuwar taliya na dafa naci da mai da yaji, ina gama ci kuwa sai ga Safiyya, faka faka na wanke hannu na fita muka tafi. Kasa ɓoye mata abinda ya faru jiya nayi ina bata labari, da ta lailayo wata ashariya me zafi ta yarfa min sai da na kusa buɗe motar na faɗa waje, har Ilham sai da ta tsorata nayi saurin cafo yarinyar da ta saki. "Safiyya za ki yarda da yarinya taji ciwo".
A fusace ta bige hannuna a jikinta,"Dilla Malama banza shashasha yi min shiru, Sa'ida ba ki da hankali ba ki da shi sam, ji na ke kamar na shaƙe miki wuya ki daina moruwa a duniyar nan, ke yanzu har wani kiga irin Nazifi ne kima tsaya ki saurare shi, wai har kina faɗa min kin je kin duba Uwarsa yen yen yen, Allah da ina wurin sai na ƙwaci bindigar Brother na harbeki gwara na rasa ki in huta da takaici da baƙin ciki, idan ma ba ki mutu ba ƙilan ƙarar bindigan yasa ki razana ki dawo hankalinki don naga alamar ƙwaƙwalar ki babu komai a ciki sai dusarar asara, shegiya ƴar bura'uba da ma da kika fito neman Nazifi kin zame a ƙasa kin yi targaɗe kinga sa dawo su taimaka miki ai".
Tagumi na zabga kawai ina dubanta, wannan masifar yanda take ɗaga murya tana faman huci da tada jijiyoyi idan a adaidaita muke ai sai me motar ya sauke mu, a hakan ma bata huce ba sai da ta figo wuyan rigana ta dudduke ni nayi saurin ƙwacewa kar tasa mu buga accident.
"Haba Beb sorry mana, ba dai ya wuce ba, kuma nima sai letter na ke ta jin haushin kaina wallahi, don ina ga da na samu ganinsa ma kukan baƙin cikin da zan yi sai na iya haɗiyar zuciya".
"Dilla can rufe min bakinki me warin tsiya kafin in ragargazo miki haƙoran gaba, kuma sorry for your self don ni da kika ganni ban sallama kaina wa wasu asararru ajina da darajata sun zube ba, shegiya gwarama a kwasheki a kai can garin inyamuran ai don idan kika zauna nan satan hanya za ki ke yi kina zuwa wajensu tunda karen su ya cinye miki zuciya".
Na musamman tayi parking tana faɗin,"Ai yanda kika ga wannan shegiyar Yayar tasa kamata yay ki fakaici idon jama'a kisa ƙafa ki kwarfe asararriya a ƙasa, ki bi ta kan ƙafarta ki wuce, akwai uban da ya isa ya biyoki ne a yanda kike? Sai dai ma ta ɗaure kanta idan ta nemi ta ɗora miki, kai Allah nah ka bawa banzar nan ta kusa da ni hankali, doluwar banza da wofi kawai, a haka kamar ba shashasha ba, ina ji kamar na buɗe motar nan na tankaɗa ki waje ne".
"To aikata mana Yayanki kika yiwa asara ai".
Sai kuma taci gaba da jarabata, yi take yi bata ko numfasawa. "Idan da ina nan na rantse miki da Allah sai na fita na yiwa Nazifi ihun kwarto, kashh, yanda za'a rugurguza shege a ƙofar gidan nan ai ko ni sai na shiga na ɗakko murhu".
A hankali na ce,"A ke dai manta baya".
Harara ta watsa min, kuma har muka isa beejay bata ƙara yi min magana ba, ni ɗaya na dinƙa maganata ina wa Ilham wasa. An mana ƙunshi me kyan gaske, ni bana son wani na salatep na zane aka min, duk wanda ya shigo shagon kuwa sai ya tofa wow amma dai ke amarya ce, ƙawar arziƙin nawa ce dai bata ce ƙala ba, da ana kwancewa ma na nuna mata kauda kai tayi, kuma ita ce me nanatawa mai lallen ta ƙure basirarta akaina ko nawa ne zata biya.
Gaskiya wajen sun iya aiki babu ƙarya, hatta gashina da aka wanke aka gyara sai da nace anya kuwa nawa ne, sai lokacin Safiyya ta samu damar magana tace ayi min ƙanan kitso nace a'a ba zan iya zaman ba, yanzu kafin a gama ma sai mu wuce bayan isha'i, ina gudun faɗan Abbaa, nan kuwa ba kitson ne ban so ba, Salim ne yace kar nayi kitso yafi son gashina a haka.
Bamu koma gida ba sai daf da isha'i, har ƙwalla nayi wajen yiwa Safiyya godiya, ita ta biya kuɗin kitso da ƙunshi har spa da ta dage sai anyi min, kuɗi ba kaɗan ba kuɗi masu yawa. A daren bayan dawowata Hindatu ta raka ni na shiga wasu gidaje da suke mutunci da Ummani sosai aka zama kamar ƴan uwa, kowanne gida na shiga kaji adu'a me daɗi ana yi min, muka dawo nan ma aka saka ni gaba da ƙarasa shanye wasu magunguna da wanda har wanka nayi da shi, ni da kayan sawata duk sai da aka yi mana turaren ƙaiƙayi koma kan masheƙiya.
Ban samu zama ba sai ƙarfe goma tukunna, lokacin kuma kewar Salim duk ta cika ni, yau na kira wayarsa yafi ƙarfin a ƙirga bata ko tafiya, na masa text har sau uku sai dai na san da ace ya gani zai min reply wajib ne, amma ban san ba ko jiya yayi fushi ne shi ne zai rama shima, na kasa daurewa sai da na tura masa text na ban haƙuri ina faɗa masa yau nayi kewansa musamman golden voice ɗinsa.
Duk sai nayi wani sukuku bana jin daɗin raina, yana ta ɗokin nayi lalle na tura masa ya gani, to a online ɗin ma ba ya kai, rabonsa da hawa tun safiyan jiya, na rasa meke min daɗi, na rasa natsuwata ina ta saƙe saƙe cikin raina, har Safiyya sai da na kira tace min in kwantar da hankalina inda suke ne babu network ɗazu ma da ta biya gida taji Baba na faɗin yana ta neman wayarsa bai samu, amma Sir yace masa sun yi magana da shi ta oba oba irin wannan abar da sojoji ke magana da ita.
Yau kam ba batun kwanan ɗakina don anan aka jibge miyar abinci gobe, da kayan abinci da kayan gara. Na fito da zummar tafiya gidan Maman Yasmin na ji inaa yau a kusa da uwata zan kwana, dolen dai haka na wuce na tafi don tun da baƙin nan suka zo ta bar musu ɗakinta ta koma ɗakin Abbaa, to ina ni ina batun shiga cikin su na kwana.
Washe gari tunda wuri kafin ɗaurin auren ma sai ga mutanena ƴan amana sun zazzo, Hassana Tijjani ce farkon zuwa don ita ƙarfe tara ma anan tayi mata ita da yaranta, can sai ga Maimuna itama, ƙawayena dai tun na secondry school waɗanda ake tare har yanzu, Safiyya sarkin kishi tuni ta haɗe rai tana aikin ciccin magani, faɗa take wai akan mene Hassana Tijjani zata rigata zuwa, haka ta dinƙi mitarta har sai da suka taɓa da Hassanar don dama sun saba indai akaina ne, suyi ta rigima da juna kamar yara, ni da Maimuna muka zama ƴan kallo don idan suna yi ni bana saka musu baki.
Lokacin da na ke fitowa daga wanka lokacin ƴan asibitinmu suka zo su Maman Nana da su Sister Khady, su dai shidda haka suka yo zuga suka taho, suma sun yi min kara da na su gudunmawar na frame da aka sa hotona da na Salim, ni da uniform na asibiti shima da uniform na sojoji, wanda na rasa ma ai na suka samu nasa hoton, merging aka yi wanda yay editing ɗin ya iya sosai ba zaka taɓa cewa haɗa hotunan aka yi ba, da 25k ɗin su da aka haɗa aka ce a bani, nayi ta musu godiya kuwa, sosai naji daɗin kyautar tasu, ban ma shirya ba na fara kai su gidanmu suka gaisa da Ummani, dama Abbaa na ƙofar gida da shi suka fara gaisawa, sai ce min suke sun ji daɗin adu'an da aka musu.