Sashe 98
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nima na jijjiga kai cike da gamsuwa da shi, duk da irin abinda nake ji a zuciyata sai dai ban nuna ba domin haka kawai kalaman nasa na ji suna sanyaya jikina, duk da a ɗaya ɓangaren ina jin kamar a nasihar tasa yayi son kai.
Ya sake cewa,"Allah ya bamu zaman lafiya, yasa mu sake maimaita wannan zaman a aljanna, Ya kawar da dukkan abun ƙi a cikin zamantakewar mu, ya kau da sharri ya shigo mana da dukkan alkhairi, zan iyakar yina wajen zama adalin miji a gare ku, please duk wacca ta ga na kauce hanya tayi ƙoƙarin ankarar da ni da wuri".
Ni da ita muka haɗa ba ki wajen ba shi tabbacin da yardan Allah ba zamu ba shi matsala ba. Ya amsa da good yana sake faɗin,"Kowaccenku tana aikinta, Sa'ida Kudrat ma'aikaciyar banki ce, tana fita aiki 7-4, Kudrat Sa'ida ma'aikaciyar lafiya ce, aikinta zai kasance morning and evening, so a ɓangaren girki ina shawartan kowacce da ta dinga girkinta, in yaso in kayi niyya kuna iya bawa junanku, alkhairi yana da daɗi komai ƙarancinsa. Dalilina na yin hakan shi ne; kar yanayin fita aiki yasa a zo a fara samun saɓani, ga yara a gida azo ana complain".
Kudrat ta ce,"Hakan yayi sosai".
Ya sake cewa,"Sai maganar raba kwana zance ko?". ya cigaba da faɗin,"Al'ada ta tanadar da kwana uku ga Sa'ida bayan wannan kuma ya ku ke ganin za'ayi? Bana son ayi abinda wani zai cutu a cikinku, kar a yanke hukunci wata tazo tana ce min ai ita bata so ba wancece tace haka ba ita ba. Dalilina na maimaita muku bana son ƙananun magana ne Allah ya sani shiyasa gwara ayi komai a gaban kowa. Ku yanke da kanku in ma waje ne zan baku kuyi shawara kwana nawa kuke ganin za'a raba a tsakaninku wanda babu wacce zata cutu a cikin ku?".
Kudrat na murmushi tace,"Wai sai ka bamu waje, to in ka bamun ma ai zaka dawo".
Yayi murmushi shima yace,"Ai wai kar kuji nauyina ko kunyata".
"Ba wata kunya, ni dai ta ɓangarena sai na ke ganin kamar kwana biyu yayi. Amma Sisi ke ya kika gani?".
Shiru nayi ban iya cewa komai ba, sai guntun murmushi me ciwo da ya sauka akan leɓena tunawa da ranar da aka zo min da batun in siyar da kwanana. Ta sake ce min,"Sisi abu ne da ya shafe mu gaba ɗaya, ki faɗi abinda yake ranki, lamari ne na fahimta ke kin fi kowa sanin kanki ko ba haka ba".
To ni in ba yanzu zan canja ba ai ina iya riƙe kaina ko za'a shekara, wanne horuwa ne ban yi ba a sanda na ke da mijin, na sauke numfashi na kalle shi kafin na kalleta na ce,"Ni bani da matsala ai, abinda kika yanke yayi min".
"A'a dai ki faÉ—i na ki ra'ayin zai fi".
"Na amince da naki tsarin".
"Kin tabbatar?". Kai na É—aga alamun eh. Kudrat ta kalle shi tace,"To kaji, kwana biyu yayi mana".
"To Masha Allah. Allah ya bani ikon yin adalci a tsakaninku. Kamar yanda na faÉ—a É—azu kar aga nayi ba daidai ba a zagaya ana gulmana, dan Allah a faÉ—a min ko da zanyi faÉ—a na tabbatar in na nutsu zan gano gaskiya aka faÉ—a min. Sannan ba zan dinga yawon bin É—akunan ku ba gaskiya, duk wacce ta san girki a hannunta yake zata zo inda na ke ne bani zanje inda take ba".
Kudrat ta amsa da insha Allah. Ya gyaÉ—a kansa da cewan,"Madallah, shikenan iyaka abinda zan ce kenan".
Miƙewa tayi ta ɗauki Rofi'at da take kujerar kusa da shi wacca ma ni ban lura da ita ba. "Tom Amarya da ango sai da safen ku Allah ya tashe mu lafiya".
Tashi yayi shima ya karɓi yarinyar yace,"Muje na kai miki ita, Myy ina zuwa".
Ya faɗi sunan Myy kansa tsaye, sai na ɗago ina kallonsa, hakan ba zai taɓa zuciyar Kudrat ɗin ba? tunanin da na ke ya yanke sa'ilin da yake ce mata. "Derling gobe a samar da break fast da wuri saboda baƙi".
Ya faɗi hakan suna jerawa, ohh shi bai da wani shayi kenan? A gabana yake kiranta da sunan soyayya, duk sai naji na raina nawa sunan da yake faɗa min, mene wani My? Ita fa Derling yake ce mata. Nan take raina ya sake ɓaci kishi ya mamaye min zuciyata, a fusace na miƙe na koma ɗaki zuciyata na bugawa da sauri, idanuna sun ciko da ƙwalla. A fili na furta,"Mene ma amfanin auren mijin wata?".
Jin shiru bai dawo ba ya sake ɓata min rai zuciyata nayi min hasashe mara kyau akan jimawarsa, ji nake kamar na fashe da kuka sai kuma naji ya shigo da sallama, nayi saurin kawar da kaina ina faman cin magani.
Bai kula da yanayina ba ya ƙaraso ya sunkuya gab da fuskata, ƙamshin turarensa ya daki hancina wanda ya motsa ni, haka sautin murmushinsa har cikin zuciyata wanda kuma take naji fushin da na ke da shi ya gushe, cikin murya mai sanyi yace,"Myy muyi sallah ko?".
Sai a sannan na juyo na kalle shi muka haɗa ido, ya ɗaga min gira ya ja da baya, dole na miƙe ganin ya tsaya a kan ƙaramin carpet yana ƙoƙarin tada kabbarar harama, hijabina na ɗakko, na tsaya daga bayansa muka tada sallar.
Bayan mun idar ya gabatar da duk abinda addini da al'ada ta tanadar sannan ya tashi yace,"Ina zuwa".
Yana fita na miƙe na isa closet na zuge, kayana ma duk ba'a shirya min ba, haka na janyo ƙaramar trolly na zuge na zaro doguwar rigar bacci mai haɗe da hula na saka, a sannan ya dawo shima jikinsa sanye da kayan bacci marasa nauyi riga da wando.
Waigowa yay yana kallona, ya wuce ya aje abu kan dressing mirrow, sannan ya ajiye ledan da ya shigo da shi ya zauna saman carpet yana faÉ—in,"Baby ina jin yunwa".
Ban saurare shi ba na haye kan gado na zauna ina ɗakko ɗan ƙaramin ƙur'ani, ya kalle ni yace, "ki zo kici abinci, bana son wannan cin maganin da kike yi, miskilancin na menene? ban san daga inda ya samo asali ba haka kwatsam".
"Haka na ke dama, abincin kuma na ƙoshi". Na bashi amsa da muryan ɓacin rai ba tare da na kalle shi ba. Tasowa yayi ya dawo inda nake yace,"tunda nake jin yunwa kema kina ji dole kici". Ya faɗa yana karɓar qur'anin hannuna ya mayar da shi ya aje. Na kalle shi cikin jin haushinsa na ce,"Na ce maka bana jin yunwa ko". Nayi maganar da tsiwa.
Sai kawai ya sakeni daga ɗaukata da yake niyyar yi, ya ɓata rai yanayinsa na canjawa ya fito sak a sojansa yace,"Kina ji, tashi muje bana son musu, ke ba yarinya ba ce ai kin sa me ya kamata".
Shagwaɓe fuska nayi kamar zanyi kuka nace,"Nima bana son takura".
Ai sai ya koma min zam Salim ɗin da bai taɓa wage haƙoransa ba. "Kar ki bari na ƙara mamaita kaina tashi na ce".
Ba yanda zanyi dole na tashi muka ƙarasa kan carpet, ledar da ya shigo da shi ya buɗe, packs na abinci guda uku ya buɗe yana kallona. Abincin na kalla duk da pack ɗaya ne na shinkafa sauran kaza ce gaba ɗaya, sai wani da ya buɗe shi kuma soyayyen dankalin turawa ne an zuba masa sauce a kai sai ƙamshi yake yi. "Bismillah".
Na sauke numfashi ba tare da nayi yunƙurin ci ba. Rai a haɗe ya kalle ni yace,"Allah zan miki ɗura, kuma ina ƙara maimaita miki bana son musu".
Kallonsa nayi sai naga yana neman ya shareni, dama neman wuri ne irin nawa, ba niyya na kai hannu na soma ci, ina mita a ƙasan raina na dalilin da yasa ba zai ciyar da ni da kansa ba. Dankalin kawai na ci shima ban wani ci da yawa ba na zare hannu, sai ce yay,"ita kazar hararar ki tayi da za ki ƙi taɓa ta?".
Ina kumbura murya na ce,"Ni fa bana son cin abu mai nauyi in dare yayi, bana son ajjiye tumbi kamar kai".
Na faɗa ba tare da na kalle shi ba. Dariya yayi, ya shafa shafaffen cikinsa, in banda sharri irin na Sa'ida ina shi ina tumbi, ko dan training ɗin da yake sha wajan aiki ai dole ma tumbi yaƙi zama a jikinsa.
"Ba fa yarinya ba ce ke da zan ta fama da ke, Allah sai kin ci kazar nan". Jin yace Allah ya saka na É—auka na saka a baki, raina na daÉ—a sosuwa, da can bai san ni ba yarinya ba ce sai yanzu da ya kawo ni gidansa zai ta maimaita min ni ba yarinya ba ce, to ya rabu da ni mana ya ci gaba da zama da yarinyar, mtssww.
Ina jinsa yana cewa,"Kuma za ki nuna min a inda kika ga tumbi a jikina".
Shareni yayi har ya gama nasa cimar, a cup ɗin da ya sha yogot ya zuba ya miƙo min gabana, ya miƙe ya fita ya barni na bi bayansa da kallo. Har ga Allah da kukan da na ke ji zai samu sakkowa da na rage raɗaɗin da ke raina, bayan kusan minti biyar lokacin agogo ya buga ƙarfe ɗaya saura sai ga shi ya dawo, ya ce na taso mu wuce ɗakinsa, ina ciccin magani na ce,"Me ya samu nan ɗin? Ko kayan ciki ne ba su maka ba".
Harara ya galla min, na ɗauka hijabina na saka na wuce, yana riƙe da hannuna muka fita a ɗakin bayan yasa key ya rufo ɗakin. Ta falo muka shiga wata ƙofa sai gamu a ɓangarensa mai ƙaramin falo mara kayan hayaniya, sai award da hotunansa duk yayi kyau sosai cikin kakin soja. hannuna ya saki yace,"Ki shiga zan kulle ƙofar".