← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 113

Sashe 89

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_"Amincin Allah da yardarsa su tabbata a gare ki, ina mai wannan rubutu ne gareki yayin da idaniya ke zubar hawaye haka kuma zuciya ke cike da nadama da tarin danasani, haƙiƙa tunda kika bar rayuwata na ke ta ganin ibtila'i daban daban, cikin shekaru shidda har yanzu na kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali, babu jin daɗi babu farin ciki, sai daga baya na ankare da dukkan laifukan da na aikata miki sune ke dawowa gare ni, tabbas hakkinki kaɗai ba zai bar ni sukunin rayuwa ba, ni na sani na zalunce ki, zaluncin da sai dai Allah yay miki sakayyya kawai, na so ace na samu wata dama da zan maido da ke cikin rayuwata domin na gyara kuskurena sai dai lokaci ya ƙure min, bakin alƙalami ya riga ya bushe...na samu labarin kin je kin duba mahaifiyata, na gode Allah ya saka miki da aljannah, kuma naji an ce kin yi aure da irin mijin da kika aura, tabbas har zuciyata naji miki daɗi na kuma tayaki murna, Allah yasa albarka ya tabbatar da alkhairi a rayuwan aurenki, ina me yi miki adu'a tare da fatan samun rayuwa ingantacciya a gidan aurenki, ya dawwamar da ke a farin ciki da kwanciyar hankali, kazalika ba zan ƙi sanar da ke cewa rashinki a rayuwata wani babban giɓi ne da ba zai taɓa cikuwa ba sai da ke, na soki, ban kuma san ranar da zan daina sonki ba, don Allah ki yafe min, ki yafe min ko na samu sassaucin bala'in da na ke fuskanta a rayuwar da babu ke a cikinta, ki yafe min ko na samu salama a lahirata, na rasa da idon da zan iya fuskantarki, ina jin kunyar ganinki, ina kunyar haɗa idanuwa da ke...tsohon mijinki Nazifi Bala Mai Kalwa"._

Tun farkon fara karatun naji zuciyata tayi rauni, kafin na gama karantawar tuni hawaye ya jiƙa rabin takardar, na shiga rera kuka a hankali hanci na ta zubda majina, hawayen da ban san dalilinsa ba, kaina jingine da bango idona a rufe hoton Nazifi kawai ke haska min, hoton da na ke ganin laɓɓansa suna karanto min wannan rubutun. A gefe ɗaya kuwa zuciyata ta matse da tausayinsa da wani abu da ke harbawa a cikinta wanda ban san menene shi ba, kuma kamar an tsikare ni haka na miƙe na ɗauka mayafi, ina fitowa nayi kiciɓis da Ummani wadda ke ce min,"Ke lafiyarki kuwa? Naji ma kaman kukan ki shi ne na taso".

"Ina zuwa Ummani". Na faɗa da karyewan harshe, nayi saurin fita, haka na gama leƙena a ƙofar gida, har ɗaya ɓangaren na tsallaka amma banga ko da inuwar Nazifi ba, me yasa zai yi min haka? Me yasa zai zo ɗauke da wannan kalaman a cikin takardar da ke ɗauke da rubutunsa kuma ya kasa jirana? Ban san me zan ce ina ji a tare da ni ba, kamar yanda ban san yanda zan kwatanta yanayin da na tsinci kaina a ciki ba, Ummani na tsaye inda na barta, ta ruƙoni ganin irin yacca na ke zubar da hawaye.

"Ke menene wai, wani abu ya faru ne?".

Kaina na kifa saman kafaɗarta ina cewa,"Ummani Nazifi ne, Ummani yana cikin wani hali, kuma ya zo ƙofar gidan nan ya tafi bai bari mun yi magana ba".

Ƙumm naji kaina ya ƙwalu da bangon tagar ɗakina, haka murfin tagar ta doko min fuska. Sautin tsakin Ummani ya shiga dodon kunnena ta wuce ta barni tana faɗin,"Allah ya shigo da ubanki ki yi masa wannan zancen, saboda wulaƙanci saura kwana biyu ɗaurin aurenki ki tayar da maganar tsohon mijinki, shi algungumin da can bai san da zuwa neman yafiyar taki ba sai yanzu? Ke kuma da babu cikakken tunani da hankali shi ne har da iya barin kalaman ƙaryansa suyi tasirin da za su ɗarsa tausayinsa a zuciyarki, mtsswww".

Bayanta na bi da kallo kawai har ta wuce ɓangaren Baba Sabi'u, yanzu kenan laifi ne don halin da Nazifi ke ciki ya taɓa ni? Ɗaki na shige na silale na zauna daɓas kan katifa, na kalla wayata da ke ƙaran shigowan text, ina dubawa naga sunan Salim kawai sai nayi cilli da wayan, na zuƙa wani irin numfashi, na rufe fuskana da dukka tafukana biyu, daki daki rayuwar baya na dawo min hotonta na haska min, haka daki daki kalaman rubutunsa ke maimaituwa cikin kaina, haka kuma labarin da Lubabatu ta bani na halin da yake ciki na haska min a ƙoƙon ka, duk garin ƙaƙa ya tsinci kansa a cikin mawuyacin hali haka? Halin da na magani ma ya gagare shi? halin da har ta kai shi ga cin bashin banki, halin da har ta kai shi ga gadin shago, duk ina tarin dukiyarsa? Ina tarin dukiyar da har muka rabu ban san adadinta ba? sai naji zuciyata ta ƙara tsinkewa.

"Na manta da komai, na goge komai da ga raina, na yafe maka, na yafe maka, baka da sauran hakkina".

Haka na zama sukuku kamar wacca aka yiwa mutuwa ko take rashin lafiyan da yaci ƙarfinta, Abbaa ma da ya dawo sai da ƙyar na iya miƙewa na fita yi masa sannu da zuwa saboda jikina da na ke jinsa ya mutu, ga ƙirjina bugawa kawai yake yi, ban san meke damuna ba, ban san dalilin sauyar yanayin farin cikin da na ke a ciki ba, Salim ya kira ni ya kuma kira amma ban ɗaga ba, bana jin kuma ina da buƙatar jin muryarsa...

*B3ƘR11FT5*
Washe gari kiran Safiyya ne ya farkar da ni, na manta ma da batun zamu je ƙunshi da gyaran kai, jin ina bacci ta kama masifan dama ta san halina, sai mun je kuma mun daɗe acan ita na cikata da mita, na bata haƙuri na ce sai ta ƙaraso kafin ta zo ma na gama shiryawa. Zaune na miƙe ina murza idanuna da ke cike da bacci, on period na ke ko da asuba ban farka ba, nayi azkar ɗina na tofe jikina, sai a lokacin abinda ya faru jiya ya shiga dawo min, na kalla gefen filona ina kallon takardar da Nazifi ya yo min aike, wani mugun haushi da takaicin kaina ya kamani, lallai akaina na yarda mutum na haukan gaske na ɗan wani lokacin, ban da hauka da na fita neman Nazifi uban me zan masa? Kukan da nayi kuma na uwar menene? gwara da Allah yasa ma bamu haɗu da shi ba don ina ga da sai na kusa kashe kaina saboda baƙin ciki, takardar na ɗauka na yayyaga nayi gutsi gutsi da ita, akanta dai na huce takaicin rashin tunanin da nayi jiya.

Wayata na duba na ga uban misscalls ɗin Salim, tunda na ke da shi bai taɓa bari min miscalls irin haka da yawa ba, kuma na san duk ya damu ne da yanayin da ya tafi ya barni a ciki, lokacin ma da yana da dama ba zai tafi ɗin ba, sai naji ya bani tausayi, haushin kaina ya ƙara kama ni, ban kyauta masa da abinda na masa ba, kawai dai na san duk wanda yaga halin da Yaya suke in har kana da zuciyar imani sai zuciyarka ta karye, lokacin da zaka taimaka musu ɗin ma ba sani zaka yi ba, amma abin takaicin da akan tausayin Nazifi na ƙi picking call ɗinsa, hannu nasa na mari fuskata. Ina shiga message ma naga messages ɗinsa har biyu, ɗaya na lallashina ne da kwantar da hankali, yana faɗin in bar yawan saka damuwa a raina, marasa lafiya ne kamata yay nayi musu adu'a, ɗayan kuma yana faɗa min ya koma tun a daren jiyan sai ranar ɗaurin aure zai biyu jirgi da safe ya taho kafin lokacin ɗaurin aure, kuma za su shiga daji ne ba lallai in sameshi a waya ba ko da na kira shi, raina ya ƙara ɓaci da rashin kyautawar da nayi, na tura masa text ɗin adu'a ina aje wayar na tashi, ban basa haƙuri ba tun da dai ba laifi nayi ba.

Yau ɗin sai na ke jina na tashi da wani ƙwarin jiki, lokacin da na fito tsakargida rana ta ƙwalle nayi mamakin irin baccin da nayi, na yiwa su Anty Lami sannu da aiki, gaba ɗaya tsakar gidan ya zama babu masaka tsinke sai ka tabi kana zaka wuce ana baka hanya, gaskiya mu ɗin ƴan dangi ne, Ummani na da tarin ƴan uwa masu karamci da haɗin kai.

Ummani bata ɗaki muka gaggaisa da mutanen cikin waɗanda ke ta tsokanata Amarya ƴar hutu. Na wuce ɓangaren Baba Sabi'u can na samu Ummani suna aiki ita da Umman su Hindatu, muna cikin gaisawa da su sai ga Hindatu ta fito a guje ta faɗo jikina tana murna, nima murnar na kama yi ina tambayarta zuwan yaushe tace min ai ƙarfe takwas ma anan tayi mata, ta zo tana ta buga ɗakina ina can ina baccin mutuwa.

Jin ta ambaci ƙarfe takwas na waro ido ina faɗin,"Wai har takwas ta wuce kenan". Don ni ko da na ɗau wayata hankalina bai kai kan lokaci ba. "Ummani bara naje na shirya zamu wuce wurin Lalle, Safiyya zata biyo ta ɗauke ni tana kan hanya, tsammanina duk bai wuci takwas ɗin ba yanzu wallahi".

"To Allah ya tsare, kin dai gama haÉ—a kayanki kin kwashe ko?".

Goshi na dafe don gaba ɗaya na mance ma da sauran aiki a gabana, shashancin da na buga daren jiya yasa ni baccin da ban shirya ba, don wani zazzafan ciwon kai na kamu da shi, Abbaa ma da ya dawo ban samu damar fita nayi masa sannu da zuwa ba, kuma a lokacin ma na ɗan ji tsoro ne kar Ummani ko ta yi masa wancan batun, in je yaci mutuncina Abbaa ne bai ƙi ya buge ni ba ma.

"Zan ƙarasa haɗa su Yanzu kafin Safiyya ta ƙaraso".

"To ni dai ki tabbata kin gama duk abinda za ki yi da wuri Sa'ida, kinga jiya Abbanki sai da ya jaddada min ya zamana kin gama komai, goben ana ɗaurawa za su wuce da ke, ƙunshin nan ba lallai ne ku dawo da wuri ba kuma shi ma sai da ya bar min sallahun in sanar miki kar kije ƙunshi ki dawo masa da daddare".
Chapter 89 · 0% Book details