← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 113

Sashe 41

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR22FT5*
"Kai É—ago fuskarka ka kalle ni".
Ya É—ago yana duban Malam É—in wanda ke jifansa da mugun kallo.

"Ka san dai ni ba shashasha ba ne, kuma ba sakarai ba ne mara tunani irinka, da hankalina kuma ni ba mutumin banza ba ne kamarka, don haka kar ka ƙara zuwa gabana da maganar wani wai kana so ka mayar da tsohuwar matarka...kai ban da ɗan banza ne baka da ta ido mutanen da ka nunawa rashin mutuncinka kace a koma a ƙara nema maka auren ƴarsu, to wallahi ko ji nayi za su sake baka ƴar su sai na hana...".

"Don Allah Malam ayi haƙuri...".
"Dilla gafara rufe min baki bana son jin komai, ka tashi ka bani wuri idan ka san abun da ya kawoka kenan, idan kuwa ka ƙara yunƙurin min magana irin wannan Allah sai ka ga yanda zamu kwashe da kai".

Malam yay ta masa faɗa, shi dai a zuciyarsa bai san haƙiƙanin abin da yake ji ba, amma tabbas da Malam ɗin zai san a halin da yake ciki la shakka zai ji kukansa kuma ya karɓi roƙonsa.
Sallama yaywa Malam ɗin ya fita cikin sanyin jiki, wajen Amarya ya shiga suka gaisa, ta kawo masa abinci ya zauna yaci, ita ma nan yay ta faman roƙo da magiya tace ita fa sam ba da ita ba wannan lamarin, yaje ya samu Ummaa suyi maganar.

Yinin ranar dai gaba ɗaya haka ya wuni sukuku kamar wani mara lafiya. Bai koma gida ba sai sha biyu na dare ya bar asibiti wajen Iyam, lokacin da ya koma Zahra'u ta rufe ko'ina babu yacca bai yi ba akan ta buɗe ƙofar ta ƙi, kuma ba bacci take yi ba idonta biyu, zai kira ta ɗaga sai tace masa ya koma in da ya fito, ransa ya daɗa dagulewa, ga azababbiyar yunwa kamar bai ci abincin rana ba, kuma da zai taho ba yanda Anty Aisha bata yi da shi ya tsaya ya ci abinci ba yace ya ƙoshi domin idan ya zo a ƙoshe wani tashin hankalin ne na daban tsakaninsa da Zahra'u.

Haka dole ya koma mota ba shi da yanda zai yi, ya buɗe baya yay kwanciyarsa. Ko da Asuba ma bata sakko ta buɗe ƙofar ba sai da safe wajen ƙarfe takwas kana, lokacin zata fita wurin aiki ta fito ko kallon wurin da yake bata yi ba, sai da ta shiga mota ta zo daidai wurin tasa kana ta zuge glass tace masa,"Ai yanda ka ɓarar min da aji kasa na hayo motar haya to ka dinƙi kurɓan baƙin ciki a gidan nan, yauma idan kaga dama kar ka dawo da wuri ka kuma zama a can".

Tana ganin ya buÉ—e motam zai fito tayi sauri bawa motar wuta ta fice. A ciki ya samu ta kuma barin Iman yauma sai tsala uban kuka take, ba yanda bai da ita ba akan take tafiya da yarinyar in yaso ta samu me raino tace sam ita aiki kawai taje yi can ba zata dinga É—aukan yarinya tana tafiya da ita ba, tama kusa yayeta na gaji da wahalar shayarwa.

Ko wanka bai iya tsayawa yayi ba kitchen ya shiga ya dafa abin da zai ci, kamar ya san bata ajiye masa ba kuwa, bayan ya gama ya É—ora wanda zai tafiwa da su Iyam asibiti, matan Æ´an uwansa kowacce ka ganta da coolern abinci amma shi ban da tasa.
Bayan ya fito a wanka ya gama shiryawa ya sanya haƙarƙarinsa akan gado, idonsa na kallon sama kana gani ka san cikin harbawar sakan yay zurfi cikin tunani wanda har sai a iya zuwa ma ayi sata a ɗakin bai sani ba.

Ya jima a haka kafin ya fita falo ya karɓo Iman wadda ke hannun Marawiyya tana ta faman lallashinta, ya zo ya zauna yana mata wasa tuni tayi shiru, can kuma sai tayi bacci ya ɗauketa ya kwantar da ita a ƙirjinsa, cikin shirun da yay sai ya tsinci gimlawar tunanin kiran lambar Sa'ida.
Wayarsa ya ɗauko yay dialling numbern, tun ranar da ya saketa dama ya goge duk lambobinta da hotunanta, ashe akwai ranar da riƙe lambartata zata yi masa rana. Haka yay ta gwada kiran lambar bata shiga, sai can a koma ce masa a kashe take, ya jijjiga kai kar dai da gaske kamar yanda aka faɗa masa ta sauya layi ne, aje wayar yay a gefe bayan yanke shawarar zuwa yamma zai je gidan na su, ya san Sa'ida mai haƙuri ce da sauƙin kai, tabbas idan ta gansa zata ji tausayinsa kuma zata yi haƙuri ta dawo gidansa, wanda zai matuƙar son hakan ba don komai ba sai saboda Iyam, domin ya san in ace Sa'ida na nan babu dare babu rana tana kan zaryar asibiti babu gajiyawa babu ƙosawa, kuma cikin bawa mahaifiyarsa kulawa da kyautatawa, kuma atleast zai samu sauƙin damuwar da yake ciki a yanzu na wasu al'amura da ke neman cakuɗe masa, saɓanin Zahra'u da bai ma san ta yanda zai fara sanar da ita ba don babu ta yanda zata fahimce shi, batun sake aure ma kuwa tunanin hakan na zuwa kansa ya ke kaudar da shi amma Allah ya gani ya gaji da halin Zahra'u.

****Muna zaune ne a cikin staff room ɗin makarantar islamiyar da na ke koyarwa. Daga gefe na ke ina bitar littafin muwaɗɗa, ku san awa guda su Malama Mastura na aikin hira akan rayuwar zawarci, dama kusan duk Malamai matan mutum uku ne masu aure amma mu shida duk zaurawa ne, duk san da aka zauna ana hira sai naji suna ta faɗin ƙalubalen da suke fuskanta akan zaman zawarci, cikin gidan iyayensu ba sauƙi haka waje ma babu sauƙi, wasu cikinsu ma faɗi suke har gwara su zauna a gidan auren miji yay ta gallaza musu akan dai zaman gidan da suke yi ana tsangwamar su, ranar da Malama Alawiyya ke bamu labari har ƙwalla sai da nayi wai cikin gidansu kullum mahaifinta sai ya kyareta kuma sai ya goranta mata akan ta kashe aure ta dawo gida ta zauna, haka mahaifiyarta ma bata barta ba tayi ta faɗa mata magana komai nata ta hanata taɓawa har ce mata take tana lalata mata carpet saboda kwanciya, basu san buƙatunta ba komai ita kewa kanta da ƴar ƙaramar yarinyarta da ke hannunta, abinci kawai ake bata shima duk sanda za'a bata sai an mata mita, saboda haka ne ta nemi aikin koyarwar to shima mutane nata surutun yawon ta zubar take yi, Babansu kuma na faɗa mata ai ko aikin me zata yi bata dai da daraja a idon duniya.

Hakan sai yay ta bani mamaki kuma sai naji fargaba ta kama ni, a raina sai na ce to ko dan ni mutuwar auren nawa ban jima ba ne shiyasa hakan bata fara faruwa da ni ba, ni ban san wani abu kyara ko hantara a cikin gidanmu ba, gaskiya idan na buɗi baki na ce nafi jin daɗin gidan aurena akan zaman zawarcina to sai Allah ya kama ni, ƴan unguwa ne ma dai ke ta gulmace gulmacensu, wataran ma idan na dawo haka daga makaranta har na kanji ana ƙusƙus, Abbaa ma ina jinsa ranar suna hira da Ummani yana faɗa mata an fara surutu akaina ƴan unguwa don haka wataƙila zai yarda ne na tafi can school of nursing jigawan tun da ba a samu ta nan kano ɗin ba.

Gaba ɗaya sai na saka damuwa sosai a raina don tunani bai wuce akan masu magana akaina ba, da kuma a zo nan ba da jimawa ba iyayena su fara min maganar aure don wataƙila ganin ban daɗe a gabansu ba ne, amma kuma sai ya kasance ko da yaushe Abbaa nasiha yake min da kwantar da hankali ta yanda damuwa bata da ikon samun muhalli a zuciyata, kuma da hakan na samu natsuwar ruhi da zuciya matuƙa ganin iyayena na tare da ni, Allah har mancewa na ke da wani suna bazawara ji na ke tamkar ban taɓa auren ba. Yayyuna kuwa babu abin da zan ce da su sai Allah ya saka musu da gidan Aljannah ya ƙara musu buɗi, gata dai iya gata da nuna tsantsar kulawa bayin Allahn nan na yi min, duk san da suka shigo gida sa tambaye ni ban dai da wata matsala ko na ce musu ehhh.

Yashaik da kansa ya biya min kuɗin koyon ɗinki tun watarana da ya zo ya samu muna hirar da Ummani, wallahi ba ai sati ba sai kawai ganinsa nayi da form yace na cike anjima na kai gidan Maman Binta, ranar har kukan farin ciki nayi, to yanzu ɗinkuna na ke tayi kuma Allah yasa min nasibi a kaasuwancin. Duk wata kuwa idan aka bani dubu takwas ɗita a islamiyar da na ke koyarwa ba na riƙe ko sisi tawa yaran Yashaik da Yaya Imam na ke wa siyayya, sauran kuma in siyo omo da sabulun wanka da na wanki na aje mana a gida, Abbaa yay ta faɗa wai na ke rike kuɗina ina adanawa ko na ke siyawa kaina abu, ni kuwa banga amfanin kuɗin ba in har ban musu ba, to me ma na ke da buƙata wacca basa min?
Chapter 41 · 0% Book details