Sashe 56
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kunya na É—anji na rissina ina gaida Yaya Imam, kallonsa na ke ina cewa,"Yaya naga ka zama babban mutum".
Hararata yay da cewa,"Malama ina kayan na ki, kar muyi dare a hanya".
Tare muka nufi inda kayana suke, muka ɗauko muna tafe sai ga mota baƙa ta faka a gabanmu, Safiyya ta leƙo tana cewa,"Yaya Imam shigo mu tafi ku barta anan".
Da mamakinsa yace,"A'a Ƙanwata ke da wa?".
Tace,"Kawata na zo tara ai, da ba ku zo ba wallahi Yaya kun barta ta taho da kanta".
Gaisawa suka shiga yi, ya karɓi Babyn hannunta, kusan miti biyar ana tsaye sai hira ake. Wata mota fara ta faka gabanmu, na ciki ya fito saurayi ne baƙi ya zo wajenmu, muka gaisa da shi, yana dubana yace,"Don Allah ku ne ƴan makarantar da ku ka dawo yau?".
Na É—aga masa da cewa ehh. Sai ya ce min,"Please ko kin san wata Sa'ida Salman?".
Safiyya tayi saurin ce masa,"Ehh ai ita ce ma, lafiya dai ko?".
Sai ya miƙo ticket yana cewa,"A'a dama wannan aka ce na bata".
Ta karɓa tana duba kafin ta miƙawa Yaya Imam tace,"Laa Yaya kaga ma ashe har da kuɗin jirgin masu zuwa ɗaukan su an musu, bamu sani ba. Ke ba'a faɗa muku ba?".
Ina kaÉ—a kai na ce,"A'a zai iya yiwuwa kuma an faÉ—a É—in ina can sakaraftuna na murnar tahowa ban sani ba".
"Ga shi ma yanzu jirgin na ku zai tashi, sai mu koma ciki ai".
Safiyya na tare da mu bata tafi ba har sai da ta ga tashin jirginmu. Tun da muka shiga na ke tawa su Yaya Iman dariyar fama zare ido da suke a cikin jirgi, ba sa banba ɗan kauye yay abin hannu, shi kuma daɗi duk ya cika shi yana faɗin yau ata sanadina ya shiga abin da bai taɓa zato ba, ina ma ace har da Abbaa da Ummani suka taho, gaskiya wannan makarantar tamu sai dai Allah ya biya su kawai.
Haka muke ta hiranmu ina ba su labarin can, du da na ƙosa naga mun sauka burina na ga Abbaa da Ummani kawai.
Lokacin da muka sauka a airpot ɗin Malam Aminu Kano messge ya shigo wayata, ina dubawa naga an sa,_"Saura nan ma ki tsaya tsakiyar titin jirgi kina ƙauyanci...gaisuwana ga Abbaa da Ummani".
Dariya na saki ina jinjina lamarin ƙawata, ni na mant ma na tambayeta ko kamfanin sim card ta buɗe ne da duk message ɗin duniya in zata min da sabo take yi, duk da ma first visiting da taje min tana ta rantsuwa ba ita tayi min messges ɗin nan ba ni kuwa na ƙaryatata, to idan ba ita ba waye?
_________________________________
*Alhamdulillah! Ƙarshen littafi na jiyu kenan, Littafi na uku zai fara sauka a ranar ɗaya ga watan December insha Allahu, zan ɗan huta na kwana biyu, kuma littafi na uku shi ne ƙarshen littafi na labarin Ƙayar Ruwa, Nagode, Nagode da Soyayyarku, masu siya Allah ƙara buɗi da arziƙi, Allah ya bar zumunci, Ameen*
_Kuma kafin mu É—ora zan so jin ra'ayoyin ku, Fitattu Biyar na maku fatan alkhairi.._
*28/11/2023*
*Halimahz*
07018098175
*B3ƘR01FT5*
*_Bana jin zan iya fara rubutun ba tare da na ambace ki a wannan fejin ba Takwarata Sadiya Rabi'u, Alkhairin Allah ya isa gare ki da ke da ahalinki, Ya kare ki da kariyarsa, taimakonsa, salamarsa, ya azurtaki da mafirin ciki madawwami. Na gode na gode sosai kuma ina kan yin godiya._*
*_Haka dukka mabiya wannan littafi musamman waɗanda suka nuna min ƙauna wajen sanya kuɗinsu su mallaka Allah ya mayar muku da ninkin abin da ku ka kashe, ya azurta rayuwarku da albarka da kariya tare da farin ciki._*
________________________________
Tafiyata kawai na ke tun saukarmu, na bar Yaya Imam da Yaya Al'amin can baya da uban kayana a hannun su, zumuɗina da ƙosawata duk bai wuci na ganni a gida ba gaban Abbaa da Ummani. Adaidaita sahu na tsayar mana, na faɗa masa unguwar makwarari zai kai mu ya faɗi kuɗin da za'a ba shi ban tsaya ciniki ba na ce masa to, Allah ya sani bana son in tsaya ciniki ana kaza ina a'a kaza, musamman ma na kuɗin mota, ga dai shi ni ba ƴar wani ba kuma ba me kuɗi ba, amma a hakan iyayena da suka san halina a wannan fannin duk sanda za su ba ni kuɗin mota da duk iya ƙoƙarin su sai sun nema min wanda su ke ganin zai ishe ni.
Da sauri na buɗe hand bag ɗin hannuna na ɗauko dubu ɗaya da ɗari biyar da yace na miƙa masa, ba na so Yaya Imam ya ƙaraso na ɗora masa nauyi, tun da akwai kuɗin a hannuna gwara na biya, bayin Allahn nan tun da na tafi suke ta ɗawainiya da ni, ban da abin biyan su sai dai adu'an Allah yay musu sakayya da gidan aljanna.
Ina tsaye jiran isowar su sai na tuna ma ashe ba guda ɗaya zamu yi ba, dole sai dai biyu, na ƙara tare wani shima ya faɗi abin da wancan ya faɗa take na basa kuɗinsa na ce su ɗan yi haƙuri ga su nan ƙarasowa.
Ni da Yaya Imam muka hau É—aya, Yaya Al'amin da jakkunan kayana a É—ayar. Da yake Yaya Imam shi ba gwanin hayaniya ba ne shima irina ne, duk sai muka yi wani dunkum a motar, sai ma ni É—in ce da duk na ke a cikin farin ciki na ke É—an jan sa da hira, ina cewa Yaya sai naga garin ya sauya min, me adaidaitar da ya ke jiyo hirar tamu shi ma ya sako baki.
Muna isa ƙofar gida yanda ku ka san an jefo ni haka na fito daga cikin adaidaitar, Abbaa na ƙofar gida zaune kan tabarma yana jan carbi, ya kafa ya tsare yana jiran dawowarmu, dama Yaya Al'amin sai da ya faɗa yace Abbaa fa ba zai wuce mu same shi ƙofar gida ba ko bakin layi.
Kafin na karasa ga in da yake har ya miƙe cikin tsananin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a gare shi, jikinsa har wani kyarma yake, na tafi da saurina ina duƙawa a gabansa, ƙafafunsa na kama na riƙe ina jin wani irin sabuwar ƙauna da jin ƙan mahaifana, hawaye ya cika kwarmin idona, ban san irin godiyar da zan yiwa mahallicina ba da ya bar min su a raye tsawon wannan lokacin, duk da cewa me tafiya dole tana nan zuwa, haka ban san irin godiyar da zan yi a gare shi da ya bani iyaye nagartattu waɗanda a ko ina ɗa ya shiga zai bugi ƙirji yace shi ɗan wanene ba tare da wani shayi ba, kuma jin hakan yasa a kalle ka da daraja da martaba duk kuwa da cewa su ɗin ba masu kuɗi ba ne.
"Miƙe! Miƙe mu shiga daga ciki ƴar albarka, likita bokan turai madallah, sai godiya ga lillahi".
Tuni ƙofar gidan mu ya ɗinke da jama'a ƴan kallo, yara da manya duk an yi curko curko ana faɗin ƙasar waje taje ta dawo, ta zama likita yanu, duk sai na rasa ma me na ke ji a tare da ni, kalmar Alhamdulillahi ce dai ba zan daina faɗinta ba har na kai ga kushewa.
Maƙotanmu kuwa su Malam Sani da Malam Auwal duk suka zo wurin Abbaa suna masa murna nima suna min murna da sanya albarka gami da adu'a.
Abbaa ya ciro ɗari biyar a aljihunsa ya kira Yaya Al'amin ya ce,"Kaga ba wa waccan me awarar ka ce ta rabawa yara sadaƙa".
"Na nawa Abbaa?".
"Sadaƙa ce Al'amin na dukka zaka ce, niyyar na tare da ni da ɗiyata".
Ya karɓi kuɗin ya tafi, lokacin kuwa matar ke kwashe na cikin kasko, da yake duk magriba ana idar da sallah ta ke fitowa ta fara suya, kuma kafin ka ce wannan an siye ta tashi.
Tuni har an gama kai kayana cikin gida, muna shiga daga soro na samu Ummani tsaye na doka tsalle na ɗafe jikinta, itama Allah sarki uwa sai na ji tayi ihun murna har da su guɗa wacca ban taɓa ji tayi ba tana faɗin Alhamdulillah, Allah mun gode maka, muna godiya gare ka da ka kai mana ƴar mu lafiya ka dawo da ita lafiya ka kuma bamu aron rai da lafiya ganin lokacin da bamu tsammaci zamu kai ba.
Daga cikin gida muka shiga in da duk ƴan gidan mu suka firfito, suma carko carko a tsakar gidanmu, dama dai ɓangarenmu tsakar gidan hanya ce don kowa ta nan yake wucewa ya shige sauran ɓangarorin, kowa sai taya ni murnar dawowata yake, kuma kowa ya zo bai min kallo ɗaya sai ya ƙara ya kuma ƙarawa, bayan kallon kyau har da na burgewa ganina sanye da kayan ma'aikatan lafiya.
Sai ga Umman su Hindatu ta taho da tafinta tana,"Lale lale oyoyo oyoyo da mutanen ƙasar wajen, ohh ni Haule Sa'ida ke ce kika koma haka, Allah azimun wallahi kamar an canja ki, sannu da dawowa sannu sannu, shikenan abin acas cas mun yi likita a gida".
Ina ta murmushina bakina yaƙi rufuwa na rissina na gaida ita. Yaran ma duk ina murmushi muka gaggaisa da su ina musu godiya da yanda suka nuna min kulawa, sai yau na ke jin ina ma ina da ƙanne da muke ciki ɗaya.
"Sai kika ji haihuwar ƴar uwarki, na ce da Sa'ida na nan ai ita zata karɓi haihuwa". Cewar Umman su Hindatu.
Na ce,"Ai Umma ji nayi kamar nayi tsuntsuwa na taho wallahi, wai ace Hindatu ta haihu bana nan".
"To ya za'ayi, ai kun yi É—a shima sai yanzu zai ga Babarsa".
Haka dai muka ɗan taɓa hira anan tsaye kafin taja yaranta suka koma sashen su, ina duban Ummani na ce,"Umma fa?". Tace,"Kema kin san hali, ai tun da kika tafi ta daina min magana, ko zata wuce ta tsakar gidan nan sau ɗari ƙala ba zata ce min ba, to ni dai da na fita ilimi bana fasa yi mata sallama, yanzu leƙa can wajen na ta kar dai ki jima balle ranki ya ɓaci, Aniyarta ta baƙin ciki ta tsaya iya kanta".