← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 113

Sashe 50

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga yanda naji tayi shiru na san jina kawai take, ma'ana in gama mu É—ora da wani zancen. "Kika min shiru".

"Ina jin ki ai, ni an faɗa miki irinki ce da maganar mutane ke damuna, wanda ya fasa cewa nayi kwantai yaci uwatas, idan mutum shi ke ci da ni ko a makwamcinsa na ke kwana duk ya ƙwace...ni na faɗa mata ta toshe kunne daga duk abin da zata ji, aure lokaci ne idan ya zo duk ƙina da shi fa sai nayi kamar mutuwa yake, ni dai kawai a min adu'a don wallahi tun a kanki na ke tsoron maza Sa'ida, Nazifi ya girgiza duniyata, amma ɗan bantan uba ai very soon zan girbe abubuwan da ya shuka, Allah ubangiji ya kawosa gabanki yana kuka".

Murmushi kawai nayi ban ce komai ba. Sai na kwantar da murya ina mata nasiha ina bata shawara akan dai ta tsaya ta fidda mijin auren shi yafi, tun da tana da masoya masu sonta tsakani da Allah, kuma tayi karatun nan har ma tana da aikin yi to me ya rage mata kuma? Fitar nan da take tayi a har business É—inta sai surutu ake akai to baka san bakin wani ba.

Mun daɗe muna wayar da ita kafin muka yi sallama bayan ta haɗa ni da Ummaa a confrence call, wallahi Safiyya ƙawar ƙwarai ce muna gama wayar sai ga alert ɗin 30 tayi min wai gudunmawarta na tafiya makaranta.
To cikin satin gaba É—aya sai na zama cikin shire shirye, Abbaa kuwa kace zai min sabon aure sai faman siyo min atamfofi yake da shadda yana cewa na É—inka abina duk da ba masu tsada ba ne, sai yace wai dai idan naje can aga Æ´arsa fes fes da ita. haka Yaya Imam ma da yake yanzu turaruka yake saidawa da kayan kwalliya ya kwaso min kaya ni duk sai na ke jina ma kamar nafi kowacce mace gata da samun dacewar family, Yashaik kuwa shi ne da siyo bandir É—in littafai da biro da É—inko min hijabai.

Hajiya Ummani kuwa ina gefe ina mata dariya, ta jidi uban shinkafa kusan rabin buhu tasa aka yo taliya ƴar murji kwano biyar wai na tafiyata, har da su ɗauko tsohon risho da muka daina amfani da shi tun da kalanzir yay tsada, ta wanke shi tass ta saka a bakko leda. sai da Yaya Al'amin yace mata ai duk ba'a tafiya da su tun da ni cikin hostel zan zauna ba gida zan kama ba, ko su man abinci ma duk ba'a tafiya da su, yaji ne da maggi kawai, sai ta siyar da shinkafar dama da cuku cuku ta haɗa kuɗin ta siya, ta aika kuɗin ƙauye a auno mata barkono kwano goma za'ai farin yaji da na daddawa, ni dai dariya kawai na ke yi, a gefe guda kuma ina ta jin tausayin iyayen nawa, ba damar suji kuɗi hannunsu sai su ce na tambayo me ake tafiya da shi a siya min, Ummani da taji kuɗi hannu sai ta ban tace sauri je ki rimi su ba ki haɗin maggi, haka ta daka min maggi kusan toba biyar irin manyan nan na zuba spices.

Ana saura kwana uku tafiyar tamu Abbaa yace na shirya naje ƙauye muyi sallama da ƴan uwa na can, tare da shi muka je muka yini acan sai dare muka dawo, wallahi ranar duk sai naji tamkar sallamar ƙarshe na ke da mutane.
Ana gobe zan tafi na jajje gidan ƴan uwanmu na amana suma na musu sallama, maƙota ma duk na shishshigaa su duk tare ma muka shiga da Ummani, kowa muka je sai ya tayani murna yay min adu'a.

Da daddare ina ɗaki kwance na gama haɗa komai nawa nayi lamo ina ta tunani daban daban, sai naji ƙwala kiran Yaya Imam, na fito na same shi ya miƙo min leda baƙa babba, na buɗe naga takalma ne masu kyau da ƙarko guda huɗu ya siyo min, na gwada duk suka min nayi ta masa godiya har da ƙwallata.
Bayan sun yi sallama da su Ummani zai wuce gida yace min,"Goben kin ga ƙarfe bakwai suka je jirginku zai tashi, don Allah sai ki daure ki kammala koma daren yau da kin yi asuba ki fito da kayan ki, na yiwa wani me adaidaita maƙocinmu magana daga masallaci zamuyo nan ko gida ba zan shigo ba".

Na ce,"To Yaya".
"Kar fa sai mun zo ki dinƙa tsaye tsaye".

Da haka ya fita. Ummani tace,"To tun da haka ne kinga shiga kiwa mutanen gidan sallama ba'a zo ana tashin su da sanyin asuba ba".

Wucewa nayi ƙafafuna a matuƙar sanyaye, na fara shiga ɓangaren Baba Sabi'u na jima a can shi da Umman su Hindatu suna ta min nasiha, wacca ta ƙara sanyawa jikina ya mutu duk nayi la'asar, kafin na fito na tafi ɓangaren Baba Tijjani, nan dai Baban ne yay min faɗansa da nasihohinsa, Umma kuwa kyaɓe baki tayi kawai tace Allah sa ayi abin da aka je yi, ƴaƴanta kuwa babu wanda yace min ci kan ki, saɓanin ƴaƴan Baba Sabitu da naga ƙauna cikinsu har da masu kuka.

Kaka ma a daren muka yi sallama da shi, daren dai ni ban wani runtsa ba, kamar yanda zan ce Abbaa da Ummani ma duk basu runtsa ba don ina jiyo sautin maganarsu cikin dare sanda na fita alwala.
Da asuba ana idar da sallar asuba Abbaa ko shigowa gida bai ba sai ga adaidai na horn a ƙofar gida, cikin sauri kuwa na fita gudun mita irin ta Yaya Imam, Yaya Al'amin ya bani wani agogo yace amma idan na tashi dawowa na taho masa da na ƴan gayu nace an gama Yayana, lokacin Abbayo ya kira waya shima muka yi sallama da yake ya koma can Ibadan ɗin tuni.

A ƙofar gida muka tsaya sai da muka jira Abbaa ya dawo wai ya tsaya ne ayi sadaƙa. Haka muka ɗunguma muka tafi airpot, Yaya Imam a adaidaitar da Kayana suke, ɗayar da Yashaik ya aro kuma shi ke tuƙa mu da ni da Ummani da Abbaa da Yaya Al'amin, Ummani dai tun da muka taho take ta matse hawaye, nima kuma kukan bai zo min ba sai da muka je aripot ɗin.

Duk ƙin tafiya suka har aka gama clearing ɗinmu, lokacin da aka kiramu na tashi kenan sai naji wayata tayi ƙara ina dubawa naga an turo min saƙo ta gmail ɗina daga wani banki wai suna taya ni murnar buɗe doller account da su. na aje mamakina a gefe na tafi wurin ahalina muna sallama, nan kuka ya ƙwac e min sosai har da su majina, da ƙyar na iya juyawa na bar wajen shima sai da naji ana ta sanarwar nan da mintu biyu jirgi zai tashi, Abbaa yace,"Sa'ida je ki Allah yay miki albarka ya tsare hanya, kina sauka ki kiramu ɗin kin ji, Imam yay miki canjin kuɗi yace suna ƙaramar jakar da Babarki ta baki babu yawa dai duba ashirin ne daga baya in sha Allah za'a karo miki, Allah yasa ki dawo ina da tsawancin kwana".

Ƙafafuna naji suna neman kasa ɗaukata su tafi da ni, saƙo ya kuma shigowa wayata, cikin gudu gudu saurin tafiyar da nake na duba sai naga saƙo daga wata lamba ta ƙasar waje, cikin harshen turanci da cewa. _"Safe flight, Allah ya tsare hanya, a maida hankali a karatu first class muke so, a kula don Allah, amanar kanki"._

Har na shiga cikin jirgi ina murmushi don na san bani da wani me min messge irin haka sama da ƙawata Safiyya, sosai na ƙara jin sonta da ƙara ƙudurin kyautata mata idan har Allah ya ida nufi burina ya cika.
Awan mu shida zan ce keman a jirgi muka sauka a ƙasar Germany, lokacin da na fito daga jirgin na kalla garin na shaƙi iskar sai naji tamkar komai mafarki ne, Allah kenan, ko da wasa, ko a tunani ban taɓa haskowa kaina zuwa irin wajen nan ba. Hatta tsohon mijina da yay kuɗin bai taɓa lissafin cewa zai kai ni saudiya ba ma, dama ita kawai na ke da burin ace yau na hau jirgi na ziyarci ɗakin Allah na kuma kai ziyara ƙabarin manzona. Kawai sai naji sabbin hawaye sun sauka a kuncina, ba na baƙin ciki ba ne ko damuwa ko kewar ahalina, a'a kawai ji nayi nasa rai da rabon zuwa makkah, kuma ina ji a jikina nan kusa ubangiji zai kira ni.

Muna zaune ka wasu kujeru mu da muka zazzo daga nigeria ƴan makarantar, sai ga wani farin mutum dogo gashinsa kamar na larabawa, ya duba ƙaramin katin hannunsa yana tambaya wacece Sa'ida Salman Madobi, sai na ce masa gani yace an ce ya zo ɗaukana ne, sai na dubi sauran ƴan uwan tafiyar tawa, na ce su taso mu tafi sai yace ai ni kaɗai ɗin dai. Kamar ba zan tafi ba duba da cewar ya za'ai mun zo tare kuma duk makaranta ɗaya can zamu nufa ya zaman ni kaɗai ace an zo ɗaukana, sai wani Saurayi cikinmu yake cewa naje kawai ai ba wata matsala ba ce. Nace to nan na nunawa mutumin kayana, ya kwasa sai rawar jiki yake yana kirana da Madam, yana saka kayan a both ɗin mota zai haɗa da wata green ɗin jaka sai nace masa ba tawa ba ce, sai yace min a'a tawa ce an ba shi ya taho min da ita, amma gata ma na riƙe a hannuna.

Na karɓa na shiga motar da adu'ata, duk na ƙosa na samu sarari na siya sim na kira gida na sanar musu mun sauka, ai ko ina cikin wannan tunanin sai drivern ya juyo yana bani layin waya yace na saka, na karɓa na saka da murnata ina ta masa godiya kuwa, ni dai a tsammanina tun da ya bani ai ƙila kyauta ne ake rabawa ɗalibai.
Ba'ai minti biyar ba da ɗora layin naga shigowar saƙo da cewar,_"Fatan an sauka lafiya, Allah ya bada abin da aka zo nema"._

Wani sanyayyan murmushi na yi a fili na furta,"Zan kira ki ƙawata, ina son ki Allah ya bar mu tare".
Chapter 50 · 0% Book details