Sashe 93
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin aji da takun nustuwa mahaifiyarsa da Kakarsa suka shigo falon, fara'ar da ke saman fuskar Maa kaɗai zai tabbatar maka da ita ɗin macece mai ilimi da iya zamantakewa, haƙoranta duk a waje, ashe itama me kyau ce, na ganta a hoto don ita ce akan wayarsa amma sai naga a fili ma tafi kyau nesa ba kusa ba, tun daga nesa Safiyya ke ce min gulmamman ga surukar ki nan, har da Umma don na jiyo muryarta itama, dama ita tun jiya ta taho.
Nayi saurin zamowa na duƙe a ƙasa, Maa ta kama ni zata maida ni kan kujerar sai na kasa zama don gaskiya ba zan iya zama gani gata ba, da nauyi kam. Ta dubi Umma tana ce mata ta faɗa min ita uwata ce, Umman su Safiyya ke cewa ai halinmu ɗaya da Kudrat. Maa tana ta saka min albarka da nuna jin daɗinta, itama har da adu'anta na Allah yasa na shigo family ɗin na su da ƙafan dama.
Kakarsa wadda suke kira da Mommi itama muka gaisa da ita tana ta saka min albarka, wata cikin ƙannensa wadda suke cousin ta zago ta bayana tana haɗa gefen fuskarta da tawa tana cewa,"Aunt Dimple you are highly welcome to Chibuzo family". A hankali cike da kunya na ce mata,"thank you". fuskata na fitar da murmushi. Gaskiya family ɗin su Salim mutane ne masu karama, sun karɓemu hannu bibbiyu cikin girmamawa da mutuntawa, babu nuna wani ƙabilanci, kowa haba haba yake da mu, Mommi sai faɗa take yi me yasa sauran matafiyan suma ba su biyo mu a jirgin ba.
Aka ce za'a kai ni can ɓangaren Maa na zauna sai Mommi tace a'a a kaini wajenta, can muka tafi muna zuwa duk muka yi alwala muka yi sallah, su Maman Yasmin suka rarrashe domin hutawa sai ga shi ana shigo da flask flask na abinci da lemuka iri daban daban, wani wawaken tray kuwa me zurfi cikinsa aka zubo wasu daƙwala danƙwalan kaji kamar sayi magana, kana kallo yawunka zai tsinke, Mommi ce take muci mu ƙoshi namu ne dukka kar mu rage ko saura.
Muna nan zaune tasa aka kira direbobin da suka taho da su Umman Batula, ta ke tambayarsu suna dai tafe lafiya ko. Mun yi waya da su Ummani na faɗa musu mun sauka lafiya, Abbaa yana ta ce min na yi haƙuri a inda na tsinci kaina, za su zo wataran insha Allahu, sai duk jikina ya ƙara yin sanyi kewarsu ta ƙara kama ni.
Bayan mun yi sallar magriba ne Mommi tayi min rakiya falon Kakan su Salim, Allah sarki shima ya tsufa tukuf kamar Kaka, yana daga kishingiɗe akan wata kujera, Ƴaƴansa na kewaye da shi ciki har da baban su Salim wanda sai yau shima na taɓa ganinsa, shi ko a hoto ban gansa ba kuma da shi ne dama bamu gaisa ba, ina ganinsa na gane shi saboda zubin ingarman jikinsu ɗaya da Salim hatta sautin muryarsu.
Ai ko da fara'arsa shi ma kamar Maa ya karɓe ni, na lura dai family ɗin na su dukka haka suke, babu wani me damuwa a cikinsu Allah ya ba su kyakykyawan zuciya, yana kan kujera a zaune Mommi ta kai ni har gabansa ƙasa gaban ƙafafunsa, sai gani nayi ya miƙo min hannu mun gaisa, naji na kasa sai Mommi ɗin ce ta kama hannuna ta sanya cikin nasa, "Allah yay miki albarka kin ji daughter nah, kuma ina miki barka da shigowa cikin mu, ki ɗauke ni tamkar mahaifinki kin ji, idan kina son wani abu ko kina da damuwa am here for you dont feel shy, babu kunya tsakanin uba da ɗiyansa, kina son ko menene ki neme ni, idan Salim ya miki ba daidai ba ki sanar da ni, amma kema kar ki yi masa ba daidai becouse he is ahead of you, shi mijinki ne aljannarki na ƙasan kafafunsa".
Haka Mommi ta dinƙa zagawa da ni ina shiga ina gaida iyayen gidan, muna tafe tana bani labarinta itama freely babu ruwanta, har tana bani labarin asalinta ba musulma ba ce kaman yanda dai Salim ya bani labari.
Ashe haka tafiyar garin take da nisa, mu da su Maman Yasmin muna ta zuba idon ganin su Umman Batula sun sauka zuwa bayan isha'i sai ji muka yi Safiyya na faɗin ai tafiya da saura, su da isowa sai cikin dare wajen ƙarfe biyu da rabi zuwa uku, tafiyar tafiyayya ce awa sha uku da mintina, na jinjina kai dole Salim yace ba zai bari a taho masa da ni a mota ba, ashe haka aka kwaso ni gari me uban nisa, ni ƴasu idan zuwa mutum zai yi nawa zai kashe kuɗin mota? Ai kuwa duk tsada insha Allahu ma kuɗin jirgi zan biyawa mahaifana su zo su ga gidana, da inda na faɗa sabuwar rayuwa, Allah dai ya bamu aron rai da lafiya.
[2/2, 07:48] Hlm: *B2ƘR13FT5*
Zahra'u ce ta taso cikin gigitar yanayi, duk da halin da na ke ciki na tashin hankali sai da nayi matuƙar tsorata da yanda tayo kaina, nayi gefe don bata hanya a tunanina ko zata bi bayansa ne sai ji nayi ta shaƙi wuyana da dukkan ƙarfinta, ta maƙure ni jikin bango tana faɗin,"Wallahi sai na kashe ki kema, tun da kika kashe min yarinya ba zan barki ba, saboda kina baƙin cikin ke ba ki haihuwa shine kika kashe min yarinya".
Kiciniyar ƙwatar kaina na shiga yi, Innarta ta taso don ƙwace ni saboda yanda take yi ɗin kamar ba ita ba, amma ina Innar ta kasa taimakona haka nima saboda jikina da ke a mace bani da wani ƙarfi. Ganin zata illata ni muka koma dambe, ni dai ƙwace kaina kawai na ke so nayi, amma ita burinta tayi min rauni, wani ƙarfe da ke jikin bangon ɗakin nata ta ciro zata soka min, har na saddaƙar sai Allah yasa Inna da su Marawiyya suka rufar mata, nima na tattaro kuzarina na fizge su kuma suka riƙeta zuwa ciki.
A sannan Iyam ta iso wajen da salati tana cewa,"Wai me yake faruwa ne, menene na ke ta jin hayaniya, ba dai fitina kika tayar ba".
Ta faɗa tana kallona kafin ta buɗe ƙofa ta shiga ɗakin, na waiga ina kallonta idona na sauka kan ƴar da ke kwance kan gado tamkar mai bacci. Kasa yarda nayi da cewar ta mutu don haka na faɗa ɗakin na isa gadon na kai hannu zan ɗauketa, aikuwa sai ji nayi an kwashe ni da zazzafan mari, marin da yasani ganin ƙyallin wuta a idona wanda tunda uwata ta haife ni ba'a taɓa min irinsa ba, cikin gigita da ɗimauta na dubi Iyam da bama na iya ganinta da kyau.
Nuna ni take yi da yatsa tana so tayi magana, ban san me ya hanata ba sai ta fashe da kuka tana zama wuri ɗaya. "Wannan yarinya Allah ya isa tsakaninmu da ke, Allah ya isa ba zamu taɓa yafe miki ba wallahi, ke annoba ce aurenki musiba ne, aurenki jaraba ne, ban san mummunar ƙaddarar da ta haskawa Nazifi ke a rayuwa ba, tun da kika shigo rayuwarsa yake ta ganin jarrabawa iri daban daban, kin hana shi sakat kina so ki toshe masa duk arziƙin da zai kusance shi, na tabbata dukiyar da Allah ya ba shi ma da kina da iko sai kin ga bayanta, yanzu shine saboda mutuwar zuciya da tsantsar zalunci irin naki na mahassadiya ki ka kashe masa ƴa, ke kin san irin wuyar naƙudar da baiwar Allahn nan ta sha kafin haihuwarta kuwa, amma kika rabata da abin da ta haifa saboda ba ki san zafin haihuwa da daɗinta ba. To da yardar Allah abin da kika yiwa Shalele kema sai ya faru da ke".
Inna tana dubanta ta ce,"Don Allah wannan maganar bata kamata ba Hajiya, idan kun duba dama yarinyar nan ai bata da lafiya...".
Iyam ta ce,"Kinga Zulai kiyi shiru babu ruwanki a wannan lamarin, ki bari ni da ya shafe ni nayi magana, ba ki san wacece Sa'ida ba ne, ta hana kanta haihuwa da shi, kuma ya auro an haifa masa amma ta raba shi da ƴarsa, dama ni ta tsane ni shiyasa ta kashe me sunan nawa. To wallahi lamari nan sai mun danganta shi ga hukuma, sai Alƙali ya karɓa mana hakkinmu don ba zan yafe kashe min jika da tayi ba, yanda ta kashe itama sai an kasheta".
Ƙafafu na rawa nayi gaggawar fita a ɗakin, ɗakinsa na shiga sai na tarar da shi zaune a kan kujera, yana riƙe da Iman a hannu ya kafe yarinyar da idanu, kai kana ganinsa ka san a fusace yake Allah ne da ikonsa kawai yake riƙe da shi a zaunen. na rasa me zanyi, hawaye kawai na san da yana sakko min masu zafin gaske, sai kuma hoton tsautsayin ɗaukar Noor da ke ta haska min a idanu, abin kamar almara! Na ɗauki yarinya lafiya ƙalau kuma ace ta mutu a hannuna, tabbas tsautsayi ba ya wuce ranarsa, sai mai tsantsar imani me zai karɓi wannan mummunar ƙaddarar.
Sama na kalla a fili na furta,"Ya ubangijina ka yafe min zunubin da na aikata a gareka da na ke fuskantar hukunci".
Duk ashe bai san da shigowata ba sai yanzu, ya É—ago rinannun idanuwansa yana kallona, na zube a gabansa zan buÉ—i baki nayi magana ya É—aga min hannu alamun ba ya son jin komai.
"Ba na son ganinki, bana son ganin ko da inuwarki, na tsane ki Sa'ida, ki tashi ki fice min a É—aki, ki bar gabana Sa'ida".
"Don girman Allah ka tsaya ka fahimce ni Hub...".
Uwar tsawar da ya doka min yana tasowa kaina ita tasa nayi shiru na kare kaina da hannayena. Cikin ɗaga murya yace,"Fita a in da na ke, kar ki ƙara zuwar min ɗaki, kije ki kira ubanki da ya saba yiwa gawa sallah ya zo ya sallaci ƴar da kika kashe...Har yanzu cikin kaina na rasa mummunan matakin da zan ɗauka akanki Sa'ida, kar kiyi tunanin saki a wurina domin ba za ki kashe min ƴa na barki ki tafi kiji daɗin rayuwa ba".