← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 225

Sashe 84

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a co encidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Page 29-30* Darajar mum Suhan sai ta maida maganar ta ciki ta dukar da kai kasa take sai ta rusuna kadan tace sannu da shigowa hajiya....ta juya zata bar wajen "mum tace dawo nan suhan... sannan ta kara so itama daf don su zarah su ganta da kyau.. Zarah Dan karamin tsuka ta ja ta kau da kai.. Duka friends inta suka mike tsaye don gaida mum .. Amma mum bata amsa gaisuwan kowa daga cikin su ba fuska Ba yabo ba fallasa tace ku dakata min...."ta jawo hannun suhan ta kawo ta tsakiya gaban kowa Ta nuna suhan"tace this is mrs suhan shamud the second wife to my son majeed wato mijin kawar ku zarah.. why am telling you this is saboda ni kamar uwace ma zarah da kuma ita suhan so dukansu dai dai suke a gidan nan u shud all know.. And next time in har kun san zaku xo gidan nan don kuyi disrespecting dinta then am sory i must have to draw a line bana son wani ya sake kawo min kafar sa anan ..idan ita zarahn naku bata da hankalin da zata sanar daku haka "then i am due i wont take any nonsense in my home.fatan kuma kowa ya jini da kyau?....mum ta fada calm tana binsu da ido mai dauke da kwarjini tare da dakewa Sukayi tsuru tsuru da ido kowa ya sadda kai kasa tsuliya azage cikin jin kunya banda aneesa dake watsa ma mum harara da gefen ido A lokacin Sosai ran zarah ya baci ..sai tafara kukkuni tana cewa U are neva tired of embrassing me.. a gidan nan kowa sai ya takura wa rayuwata nikam ban san mena tsare ma wasu ba.. mum na ji amma bata amsa ta ba Shaheed yayi dan gyran murya yace kiyi hakuri madam ..pls accept our sincere apology maaam Mum ta dan yi murmushi Tace its ok" So Ladies and gentle men if u dont mind u may take your live now pls..mum ta dan musu nuni da hanya tana smiles din karfin hali don kuwa ranta abace yake matuka wani irin firgitatcen ihu zarah ta daka tana cewa" akan me? No one is leaving here tayi sauri tasha gaban su ahmad har tana haki.. as you can see am having a succes party kuma nida gida na babu wanda ya isa ya hana ni yin abunda nake so....ta fada cikin fada kamar zata bugi mum..batayi aune ba sai tau mum ta dauke ta da wani makahon mari mai kara..sai da kowa awajen ya razana Bude baki ahmad yayi zai yi magana mum ta dakatar da shi da cewa pleasse ...ta sake musu nuni da hanyar waje ... baki shiru kowa ya fice madel madel...har suka fita zara bata dago kai ba hannun ta na manne akan kuncin ta .. Suna fita ta juya a fusace zata haura sama mum ta daka mata tsawa tace.." come back here ban gama dake ba..dan dolen ta ta dawo ta tsaya wanda yayi dai dai da shigowar captain shima he was looking tensed ya iso falon cos a hanya suka gamu da su aneesa wanda ba abunda suke yi sai zage zage da masifa koda ya musu magana Some of them ko kula sa basuyi ba suka wuce abun su wai adole suna taya zarah fushi.. Ganin su cirko cirko ya sa shi tsayawa yana bin su da kallo baice uffan ba tukun "mum tace naga kin yi kaurin wuya sosai wato har kece zaki sa yar mutane agaba ke da abokan kina ci mata da iyayen ta mutunci wai ke wacece ma agidan nan na tambaye ki? Zarah Tana shiru ta sauke kai tana huci kallon bacin rai mum ke mata sama da kasa _"auren sadaqa auren bauta ko...why dont u pack your bags and leave i will pay ur pride_ mum ta maimaita mata kalman data fada ma suhan dazun." hmm waht nonsense zarah wato gaki irin ke yar gidan masu arziki ko? mum taja tsaki.. Dadin ta dai nasan asalin balbela don haka bata isa tace daga masar ta fito ba.... nan zarah ta dago kai a hargitse zata ce wani abun har jikin ta na rawa ..mum ta dada dakatar da ita.. Tace "kuma ena gargadin ki Daga yau kar na sake jin kin kira suna iyayen suhan acikin hidiman shashan ki.. don ke ba kisan darajar naki ba aka ce miki kowa haka yake ne?..are you not ashamed of ur self da kike fada ko amsa ki batayi ba? ke yanzu bakiji Alamar zubewar girman ki anan ba? Me ta taba miki da zaki na zagin ta haka who the hell are you if i may asked?wai Me kika dauki kan ki ne zarah Cos to me kam i know u as nothing but an ordinary house wife what else? mum ta fada tana binta da wasu mugayen kallo .....take zarah ta fara hawaye ... Bata dago ba..nan captain yayi dan gyaran murya ya karaso gaba daf da su.. Ya ce mum kiyi hakuri..ya juya ya kalle zarah fuskna sa adan daure yace and what are you waiting for ? C'mon apologize Cikin kuka tace" what? Allah ya kiyaye bazan yi ba..sai dai aka she ni agidan nan bazan ba kowa hakuri ba.. ba dama kenan yarinya tayi min laifi namata hukunci don an raina ni sai ana mari na? Kuka ta cigaba dayi Yana jin ta Sai da ta tagama kaf "ya juya calmly yace "nidai Bana son jin wani magana anan hakuri kuma dole zaki bayar yanzu... Itama Tayi masa shiru ....kamar daga sama taji ya daka mata tsawa yace i said NOW.... Sai da Ta tsora ta Amma taurin kai ya hana ta bin umarnin sa ..mum ta dan tabe baki tace kyaleta son mezanyi da ita bare hakurin ta bayan inada wacce take ganin mutunci na da girma na a gidan nan.. You can go to hell zarah Amma nayi miki alkwari ...mum ta maida kallon ta cikin kakkauran murya mai dauke da fushi. Tace "pim na sake ji ko na ji labarin kin fada mata sai na sa tayi miki tas tas agidan na ..and dont think she's stupid da take miki shiru... tunda abunda kika zaba kenan fine muje zuwa...mum ta juya zata bar wajen Captain baice komai ba cos ranshi abace yake a lokacin wai har shine zaice zarah ta bada hakuri ma mahaifiyar sa taki?.kai this is too much rainin yayi yawa..kafin ma yagama zancen zucin nasa ..sai ji yayi zarahn na cewa " u can go to hell too mum kuma wallhy wata tayi min agidan nan sai na gyara mata zama,.. juyawa da zaiyi ko kallon ta baiyi da kyau ba yace"ohh realyy? Toh get out of this house now zarah...ki fita min agida na nace.. Wani dum ta ji kirjin ta saida ya buga ..jikin ta ne ya soma rawa yana shaking dakan sa ... Jin haka ya sa mum ta dakata ta dan juyo wani tsawan daya daga ma zarah hatta mum saida ta girgiza ..kuka suhan ta fashe da shi don tsoro da gudu ta sabule ta bar wajen .... Mum ta iso da sauri tace son..ta rike sa cos tasan in ranshi ya baci bayi da control botton cikin wani irin yanayi muryan shi yace "mum kice tafita min agida na yanzu i dont want to look at her twice we will both regret this.. Tsoro ne fall cikin zarah ta rasa abunda ke mata dadi" wayyo Allah na shiga uku na debo ruwan dafa kaina tafada aranta tana jimami..she alwys forget that in akan mum dinsa ne baya ragi kuma baya daukan raini Ganin eh fa da gaske yake sai ta bara masa gida ya sa ta juyawa cikin sigar fushin karfin hali ta fita... duk da hakan mum bata ji dadi ba..ita dai tasan zarah bata da hali amma bata son abunda zai na kawo matsala cikin gida har cikin zuciyan ta.. Anan mum ta zaunar da shi don tasan in ya tafi haka akwai matsala zai iya rubuta ma zarah saki she's sure don alamu sun nuna a yanayin sa.. Tace calm down son nifa ban dau abun da tsanani ba pls relax bana son bacin rai..yace how can i relax mum,a inuwa daya da macen da bata girmama ki ?hauka take yi ne..taje kawai ni nagaji da ita in taje chan aka koya mata tarbiya sai ta dawo i cant take it anymore..ya isa haja mum tace noo ai Ba a yanke hukunci a cikin fushi i know shes wrong amma ka sarara haka go to bed now and sleep gobe zamuyi magana.. haka mum ta lallaba shi ya tafi dakin sa amma tabbas dama yayi niyyar buga ma zarah saki ko da daya ne don tasan ba wasa yake da ita but maganan mum ya sashi kawai ya kimtsa ya kwanta baccin dole ya sa kansa. Suhan ma tunda ta shige daki take kuka ita kanta bata san meya sa take yi ba ..da kyar ta lallaba ta sama makanta sauki har bacci ya dauke ta... 10:56pm a cikin hotel room zarah ta kasa tsaye ta kasa zaune hankalin ta in yayi dubu ya tashi...ta dafe kai cikin bugun zuciya tace "wai har yanzu mumy bazata gama meeting din bane? I need to talk to someone.i need to talk ta yi wurgi da glass cup na ruwan sanyi dake hannun ta..ta fada ta sake maimaitawa tana jeka ka dawo a dakin In not less than 3 second wayar ta ya buga karar video call ne so she quicly pick up..jin muryan hajiya rabiatu bata ma tsaya ta kalle ta da kyau ba ta fashe da kuka Tace "Mummy na shiga uku captain ya ce n fita mai agidan sa he send me out.. "da dai sai kaga kamar abun kamar bai wani dame zarahn ba amma a zahirin gaskiya tana cikin babban tashin hankali.. Dakata...dakata.. zarah mummy ta daka mata tsawa bata ko damu da halin data shige ciki ba.. Tace Kiyi min shiru da kukan banzan nan naki kiyi min cikakkaken
Chapter 84 · 0% Book details