Sashe 216
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* Tunatarwa I dont like writing on top my page amma zan daure: Ena Masu cewa idan kana azhkar,karatun qur'ani da sauran su sihiri bazai kama ka ba pls be informed ba haka bane .. Da gaske ne Allah ya shimfida mana hanyoyin kare kan mu daga shaidanu da mugayen aljanu da tsafi da sihiri da komai ma amma don ya nuna muku komai a duniya bai da iko sai da izinin sa ya sa ya gaddara ma daya daga annabawan sa sihiri kuma ta kama shi ku duba tarihi. and i dont think akwai wanda yafi annabin Allah bin dokokin Allah a duniya shiyasa muke ma karkashin su ..akwai na sakaci kam amma ku sani fa akwai na qaddara kuma in tazo dole ka yi facing. Sai kuyi addu'a da fatan Allah ya kare mu ya kuma saukaka mana kundun qaddaran mu baki daya. amma wai don ka sa rai cewa lallai mai azhkr da sauran su bazai kamu da sihiri ba to bari kuji shi mai yi ma yama fi kusa da su saboda Allah na son jarabatar wanda yake so kuma yafi kusanci da shi don ya karfafa imanin sa da hakurin sa Sai ka tsaya ka tambaye kan ka arna musulmai ne ko suna azhakr ne?to acikin su fa sihiri baya kama wasu su din waya ke kare su? A kula pls nagode. *Thanks for the wishes nagode.* *masu nema a pc stop wasting your time fa ena kokarin gamawa ne don nayi facing abun da ke gaba na so, i wont even open ur messges kuma naga ana turawa a grups i wonder why u wont just ask pls* *Page 83-84* Suhan Tana isowa ta samu ogah maje na kan dube dube hankali tashe da shike bai san ma ta bar wajen ba kallon shi kawai take saboda ita kanta bata san a gangan jikin ta ba ita kadai bace so somtimes tana abubuwa masu dauke hankali wanda ba kowa zai sani ko ya lura ba... Shikuma Wannnan bafulatani yana da tabbacin jakar sa aljanu ne suka dauke amma ita kadai tagani kuma ta dauko ta biyo sa da shi.. "Yata ena kika je?. Kar ki sake barin nan kinji? Ogah rabiu ya dan mata fada...tayi murmushi tana gyada kai bafulatani na shiru yana kan zuba mata ido.. Daga bisani yace wai shim kam" yarka she? Ogah ya dago yace" eh yata ce tayi maka wani abu ne? Yace ah'a Wannan ba yarka bashe.. A lokacin Suhan saial taki ta juya ta sake sallon bafulatanin.. Ogah majeh ya mike tsaye yace" to in ban da kai fulani meye ruwanka tunda kace ba wani abu tayi maka ba? Baice komai ya matso kusa da oga yace wannan yarinyar tana cikin masifa ya akayi kuka yi sake haka... oga ya kalle sa sigar mamaki yace kamar ya fa?Allah ya raba mu da masifa Ya dada jawo sa suka koma gefe anan ya zauna ya zayyana masa Cewa matsalar suhan sihiri ne kuma koda zasu kai nam da shekaru 10 in har ba a karya dokokin sihirin ba bazata warke tarwal ba... Abun ya dame ogah maje sosai amma bai nuna kulawar sa sai ya ce dan fulani toh ya masa kwantacen ruggar sa shi zaizo da mahaifin ta a duba musu da kyau sai ayi musu bayani..a hakan suka rabu Ya dauki suhan suka koma gida. "anan gida Shi da baba ibrahim sun dau kwana biyu suna yanke shawaran gwada sa'ar su ta wajen bafulatani "Ranar da yamma suka shirya su ukun su suka tafi har rugan fulani "Sai dai fa da kyar suka kai saboda suhan na matukar tsorata hka kawai sai tana firgita wani bin sai ta fara kamar zata balle da gudu su kamo ta abun har ya soma basu mamaki.. Lokacin da suka kai gidan ba fulani ma a hannu suka riko ta tana neman guduwa kamar wance za'a kaita wuta.. A Hakan Tana hawaye suka ajiye ta kan tabar ma Shiko bafulatani tuni ya sa hayaki irin nasu na masana maganin jeji da aljanu ya dau lokaci yana bunkawa ako ena a fadin rugar sa kafin suhan ta samu ta nitsu Suka gaisa ...bafulatani ya sanar da su shi waye ne..sunan sa jabboh A cewar sa ya dade yana bada magani shikan sa yakan yi sihiri da bokan ci amma ya zo ya tuba ya koma ga Allah ya daina yi da dadewa... Amma sai yace" zan taimake ta... saboda ta sha wahala sosai yana kallon ta sigar tausayi da jimami.. Baba ibrahim yace mum gode jabbo"ai nine asalin mahaifin ta toh ko zaka sanar da ni meke damun ta?kuma shin waye ya mata wannan sihiri da kake fada... Yayi shiru na dan lokaci kafin yace in kun yarda yau zan sa abunda ke jikin yar ka suyi magana Dakan su kar ma kigana yi ya musu karya Su kace toh bisimillh Matar fulanin amina ita tazo ta rike ta suka zaunar da ita da kyau ta shiga wanke mata jiki da wani ruwan su na hade haden itatuwa da danyen ganyen magarya da sauran su... Kuka kawai take yi tana zare ido waje kamar mai jin kashi Sai Chan da abun ya dan lafa fulani ya dauko wani turare a gwalba ya sa kadan a hannun sa ya je setin hancin ta ya manna mata ta shaka... A take ta shiga hamma akai akai tana runtse idanu tana matsewa Tana daga kai sama channnn sai ta sake hannuwan ta suka watsu suka kangare bazata ta dago kai tana kallon su duka " Sai dai hallitar da ta sauya ne a yanzun ya so ya tsoratar da su baba ibrahim na kawo salati aransa ..jajayen idanu mai kama dana kyanwa sannnan sunyi layi na babban bakin fenti har wani gurnani take tana numfashi sosai kamar ba mace ba.. Fulani ya kunna wani hayaki ta anan ta soma tsanan ta gurnani irin na aljanu ...ta shiga magana cikin tsawa da bacin rai mai tsanani tace:sai na hallaka ka jabboh.... jabboh... babu ruwan ka akan wannan harka ka fita daga ido naaaaa....ta zaro jan harshen ta waje abun tsoro tana zuba wasu irin nishi mai firgitar wa Dan fulani bai ji ya bari ba ya cigaba da sheka musu magani har sai da suka gaji suka soma magana" jabboh Yace kayi gaskiya shedani bani da hurumi anan... amma yau ena bukatar ka sanar da wayannan bil adaman me wannan yarinya tayi muku me kuke mata ajiki kuma su waye suka saka ku? ... wani muryan mai tsoratar wa don bibbiyu ma yake fita yace aikin mu kawai muke yi Kishiryar ta ta kawo mana dukiya mai yawa murabata da mijin ta... Babu ruwan ka nace jabboh ka sake mu zamu koma... Jabboh yace sam bai gamsu ba. anan ya cigaba da azabtar da aljanu sai da ya sa su asalin shedanun suka yi bayani dallah dallah ma su baban suhan tun daga ranar da zarah ta je neman taimako har zuwan ta niger wahalan data sha da duk abunda ya faru da ita tasss sai da suka fada babu ragi Sannan suka jaddada ma jabboh cewa komin maganin da zaiyi ma suhan in har majeed bai kirata ta amsa ba bazata samu cikakken waraka ba har ta mutu... Baba yayi kuka sosai da irin labarin daya gama ji yanzu na rayuwan da yarsa ta ke ciki ..abun yayi mugum damun sa A cikin ransa He blame himself akan duk wani digon wahalar da suhan ke sha... ya san yau da a dadi ya zo ya same ta bazai ji nadaman da yake ji yanzu a ransa ba Da shedanun suka sake ta a kasa ta zube ta shiga bacci kamar yadda ta saba kalar mahaukata.. Fulani jabbo ya so yayi mata maganin tsakani da Allah amma sam matar sa ta ki" tace sai dai ayi musu na kudi saboda mutanen duniya ba yarda yanzu..wanda ka taimaka shi zai nemi ya tona maka asiri... Badon ya so ba ya gaya ma baban suhan in dai maganin za'ayi mata a barta anan tare da su Sannan zasu kawo dubu 30 kudin jinya da abinci da sutura.. "Hakan akayi su baba ibrahim suka kai gida ya dauko nan ya dauko chan har suka hada kudin chas suka kawo.. A Kullum sai yayi hawaye musamman in yaga suhan na kukan zata bisu gida.... Yanzu ne yake jin asalin son yarsa a zuciyan sa sai ya gode ma Allah da ya bashi daman shan wahalan da yake yi don ita da kuma nadaman zuci dake damun sa akan watsar da hakkin ta da yayi tun da.. Tsaban damuwa da rashin barci yake fama da zaazaabi amma hakan yake fita nemo kudin jinya na abun da baza'a rasa ba Sati guda suhan tayi ta soma warwarewa a hannun fulani jabboh ana tsinka sihirin kowani rana ana warware kulli ajikin ta sometime har aman kwalabe (broken bottles)tana yi.. "Daga chan abuja aljanu sun sa zarah a gaba don ranar da aka soma cin nasara akan shedanun jikin suhan wani sudden gobara ya tashi da katoton stay classy boutiqe din ta ko tsinke ba a fitar ba ga asaran millions of naira da akayi Karamin hauka sai da ya kusa kama ta gashi yanzu aljano ya dena fita mata a dream tana zaune ma cikin mutane sai ya fara bayyana yana mata kukan zai sha jini... A cewar su wai Ana ji musu ciwo suna neman jini. ..ga kudi na neman karewa tarwal Ga shi bata gane ma gaban majeed ma bare bayan sa Anan office kuma sun sa mata ido sosai da sosai tun bata ganewa har ta soma lura Abunda ke bata mata rai wai Da Ahmed ake budirin mata bincike ana neman asan yadda take yi da kudi. Karshe ma aljanu suka sanar da ita fa su idan bazata iya ba ta dena biyan su kudi tana kawo musu jini kawai Don suhan na samun kyakkywan kulawa kuma asirin su ya kusa tonuwa.. Wannan abun in ta tuna na daga mata hankali Amma bata so ko kadan tayi harkan kisan kai... Sai