Sashe 34
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
as kanwar mahaifin suhan.. Suka gaisa mum tace bari na dubo ta, ku zauna pls Nan ta haura sama jim kadan saiga ta agaba suhan na bayan ta... Tum daga sama ummah kebin ta da kallo tana Duban yanayin ta tsakanin jiiya da yau gaba daya sai tayi kalar tausayi ganin su ummah ne yasa ta rugo a guje tafada jikin ta tana hawaye tace ummah na ashe ke ce kika zo? Hope dai lpyar ki lau ko.. kinsha magani?ya jikin naki? Ta karashe a shawagbe cikin kuka.. ummah ta shiga rarashin ta "tace lpya ta lau suhan tashi ki zauna ni ba abunda ke damu na da kyar suhan ta mike takoma gefen aunty jamila wacce ke kallon ta da sigar tausayawa nan suka gaisa ta riko hannun ta tana saisaita ta a hankali batare da tace uffan ba Mum tayi gyaran murya tace ..alhmdullhi yakamata muje mu karya kumallo ko? dama danku yasa nace ajira suhan din ma yanzu ta tashi.. da kyar ummah ta amince ta taso da acewar ta ma da sun tafi kawai cos she wanys nothing to do woth arzikin gidan shamuf damuwar ta yarta ne kawai.. Bayan sun zauna kan dinning Mum dakan ta ta sa aka shirya musu break kowa akayi servung dinsa anan ne mum ta samu daman fada ma su ummah tunbdaga farkon labarin haduwar ta da suhan har da dan tsabanin da suka samu da captain bata boye ba magana tayi cikin dabara hikima da dattako jar sai da ta tabbata su ummah sun fahimce ta sosai ummah har tayi ma suhan nasiha, "mum tace ai ba laifin ta bane ..kuma komai ya wuce Nan ta gwada musu hoton captain daga jikin wall sanye da unifom dinsa anan tayi musu bayanin ay baya kasar yau da safe ya tafi amma yana dawowa har gida zai zo ya gaishe da su.. Haka suka cigaba da hira jifa jifa daga bisani mum tayi izini ma maids da ta kai su suje suga dakin yar su Ummah tace tohh" jamila ki fara zuwa ni ena da maganan da xamuyi..ba shiri mum ta koma ta zauna sannan suhan da anty jamila suka nufa sama.. Itakam suhan dama abunda take so kenan don haka maids na fita suka dada rungume juna da aunty jamila....suhan tace anty nikam na shiga uku yanzu haka rayuwata zai kare anan? Cikin sigar tausayi anty jamilah "tace baki shiga uku ba suhan in har ena nan bazaki taba shiga uku ba.. Nan ne ta dan soma saukar da hawaye ahankali anty jamila ta dafa kafadar ta" Naji duk abunda suka fada dazun na fahimce komai suhan kiyi hakuri kinji?..ita kam bata iya cewa komai ba sai ta dan girgiza kai alaman abun na mata ciwo a ranta matika... anty ta kamo hanun suhan ta dube ta""nasan zaman nan zai miki wuya wannan al'amarin bana wasa bane cos na lura auren nan naki duk akan makauniyar hanya aka daura ta su kuma iyayen naki gani suke wai suna lazimi da alkharin dake cikin sa nan gaba babu wanda ya damu da ra'ayin ki...kiyi hakuri ta dada damko hannun ta softly ..ni ma yanzu haka shawaran da xan baki kenan suhan... ki daure ko xauna anan din tunda yanzu ba yadda mukayi iya da su Kar naje garin nema maki yancin ki ki tafka irin kuskuren danayi a rayuwa.. Nan anty jamila ta sauya fusaka kalar damuwa tare da sauke ajiyan numfashi "suhan tace kuskure kuma wani irin kuskure kenan anty? dariyar takaici tayi a takaice tace suhan kenan " shiyasa nake son anty maryam mahaifiyar ki..tasan halaye na na boye tasan ni wacece amma bata taba gaya ma kowa ba..hmm tasha min magana na daina amma naki na bari har yau..sai inaga kamar har yanzu laifin rashin karban qaddara na ne ke bi na..suhan in baki manta ba shiyasa wata rana da chan zakiga bata son ki cika zuwa waje na. nima kamar ke nake..aka aura min wani mutumi mai suna alhj sule batare da na amince ba bayadda iyaye na basuyi ba don na zauna amma naki firr don na fahimci auren nasan duk su baba sunyishi ne don suna karban kudin sa basu damu da mutunci na ba amma nikam na damu sai naki karban qaddara na turje akan sai na rabu da gidan alhj sule Wanda ba shi kadai ba hatta uwar gidan sa hajiya sumayya ta rike ni amana amma bana son shi a haka na rike buri na na barin gidan sa har sai da ya tabbata ....gashi na fito iyayena duka sun rasu yaya na mahaifinki ya guje ni rayuwa yayi min zafi na dawo bazaura kinko san illaj da kalubalen dake cikin zawarci? Da ana fada nakan ce sai dai in baka kama kanka ba amma dana fada ciki sai naga abun ya wuce tunani na..wani bin sai kinji kamar ko da cizon ki ake agidan miji zaki so ki zauna than kiyi zaman zauran ci ..mafi yawan maza sam basu daraja ki kowa kuma zai na miki kallo da kim saba da namiji koda baki saba ba.. Don na taimake kai na gashi Yanzu na fada yawon banza ma dauki kazamar rayuwa don nayi surviving. nan suhan ta dago ta kalle ta cikin mamaki" tace yes.. shiyasa nake ji miki tsoro kinga rayuwar mu kusan iri daya ne wawan mahaifin ki yabi duniya ya barki...pls in har ba cutarwa anan ki taimaka makan ki kar ki fada irin nawa rayuwan Ni zan taimake ki suhan babu abunda zai fi karfin zaman ki anan gidan insha Allahu! shima mijin naki kamar uwar shin haka yake? naga matar tana da mutunci sosai tasan darajar dan adam.. suhan tayi ajiyan zuciya mai nauyi tace..hmm anty anan ne matsala ta yake ... nan ta shiga bata labarin yadda sukayi da captain gaba daya bata boye komai ba Anty ta nitsu tana jin ta bayan tagama sai tayi shiru "chan tace ..wannan duk bakomai bane suhan ashe ma baki da wani matsala sosai. Cikin zaro ido waje suhan Tace kashe ni fa zaiyi kuma kice banda matsala anty?..kuma fa yace kar na fada ma kowa Dariya anty jamila tayi "karyan sa ya kashe ki shidin wa?kedai.. Duk wannan salo ne dayake bi don ya tsorata ki kuma yaci nasara ne don yaga kina tsoron sa... Ni Bance kiyi masa rashin kunya ba amma da zarar ya gaya miki sharudan da yace zai fada miki ki tabbata kin sanar dani ko da ta waya ne..suhan na zaga duniya naga maza .maza sun ganni babu wani namiji da bazaki iya da shi ba koda kuwa qanin fir'auna ne ..nayi miki alkwari muddin zaki bani hadin kai ba mai tada miki sense. Suhan ta dan murmusa tana share tears dinta" tace of cous my anty har kinsa naji karfin gwiwa..dan Allah idan zuby zata zo ta kawo min waya na fa uniform din aiki na.. tace toh shikenan Anan mum da ummah suka turo kofar dakin minti 10 ummah batayi a dakin ba tace to zamu tafi Tuni suhan ta sauya fuska..mum ma ta nuna rashin jin dadin ta har saida tasa aunty jamila tayi alkwarin zata sake dawowa a haka suka rabu Bayan kwana biyu da zuwan su ..mum ta sa anty jamila ta kawo zuby saboda zaman suhan shuru na mugun damun ta gashi taki sakewa da ita sosai.. Daga nan mum ta yi nazari cikin satin sai ta jawo shirin ta na gyaran jikin amarya data shirya shi na musamman tun kafin aure akan za'a ma suhan idan suka sa lokaci..ganin yanzu the enviroment is convenient sai ta yi magana masu gyaran nata suka iso. Mata uku ne kasaitattu wanda ganin su ma babban aiki ne don kwarancewar su akan aikin su..anan mansion din shamud zasu zauna don haka aka basu site don gyaran kwana 12 za'ayi ma suhan wanda ya hada da komai da komai na fatar jikin ta.. A lokacin auren zarah mum ta so tayi mata hakan amma haka taki firrr tace ita na spa na zamani take so bata son anything traditonal Bayan kwana hudu da tafiyar captain aka soma shirya shiryen fara gyaran amarya agidan kamar biki haka aka tsara babban daki ne aka tsara shi tamkar wajen bikin kamun amarya an shirya shi tsaf cikin dark red curtains masu shegen kyau da manyan pillows a jere akan tsari "shining gold colour ko ena an tsara shi tamkar fadar sarauniya A tsakiyan wajen aka sa tubalin wajen zaman ta dan carpet ne mai laushi da taushi ja da baki wanda ya dan ban banta da sauran floor decor na wajen gaba daya a gefe gefe aka jere manyan adudun turaren wuta wanda aka kunna aka barsu suna fidda qamshi ko ena ya gauraye cikin tsumayi. Daga nan Mum kullum sai tayi inviting din su zuby da anty jamila saboda su zama mata suna debe mata kewa.. it was lively saboda ba karya kowa na fadan albarkacin bakin sa a wajen musamman anty jamila ..ga safaran kayan ciye ciye masu aiki nayi ba sauki Ranar da aka fara mata na farko tayi mata jagora zuwa bathrum tace ki shiga wannan ruwan... tayi mata nuni da damammen ruwan da alredy sun shirya shi yaji hadi kam ya sauya zuwa launin pink colour sai bada turirin gamshi yake.. Tace ki cire komai ajikin ki ..ki shiga ciki ko ena ya samu ruwan amma bansa fuskan ki..sannan Kar ki fito sai kinji nayi knocking sai ki daura wannan... ta ajiye mata white yard mai dan shararara amma ba sosai ba iya gwiwa sannan ta fice.. Suna daga ciki dayan matar na kan dame kwabin dilka a wani kwarya su zuby da anty jamila ma ba a barsu abaya ba..kowa na sha'anin sa ..bayan kamar 20 minutes matar ta fito da suhan daga ita sai wannan kyalle dan fari babu komai a jikin ta nan wajen da aka shirya mata aka ajiye ta.. Daya daga cikin matan kuma ba bata lokaci ta soma warware suman kanta ta shiga aikin gyara sa tsaf tana sullube sa da nashi sinadarin hadin sannan ta nade mata shi cikin hair steamer.. Aka shafe dukkan jikin ta da kwabin dilka dayan kuma na faman turare ta da ta ko ena sai dai