Sashe 220
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* Ayi hakuri da typing error dindt have time to edit *Wannan shafin naki ne sister mrs MARYAM SAEED Allah ya baki sa'ar jarabawan ki Allah yasa kiga sakamako mai kyau ilsm *Page 85-86* Ruwa aka daura ma zarah ta sha na kusan rabin awa sannan ta dawo hankalin ta "Ganin mumyn ta sosai ya girgiza ta tasan har duniya ta nade da kyar mumy zata sake dawowa dai dai in ma zata rayu kenan.. Tace na shiga uku wayyo Allah na" kukan takaicin duniya ya hadu ya mata yawa ta rasa me ke mata dadi Ita kanta abubuwan da suka yi sun dame ta she need someone close to her amma in ta ce majeed tasan he wont even come zai ce baida lpya shima Haka ta daure ta kira mum tana kuka wee wee ta gaya maga abunda ya same mumyn ta... Hankali tashe mum ta iso asibiti Ta same zarah sosai ta tausaya mata saboda daga yanayin yadda zarahn ta kankame ta tana kuka tasan shes very much depressed ,.. sai ta zaune tare da ita duk wani kulawa da lallami wanda zai bata karfin gwiwa tana bata har suka samu suna fuskantar mumy rabi da bata iya komai sai kuka da nadaman zuci.. Da kyar maganan ke fita sabida karkacewan bakin ta Ita kadai ta san hatsarin nan eznah ne musu ba wai haka kawai ya faru ba... amma sam ta kasa furta wa sai rarrashin su mum keyi.. chan bayan wani lokaci Mum ta koma gida don ta je ta samu majeed ta tuhume sa akan al'amarin ranta ne ya soma baci da nonchalant attitudes dinsa akan zarah yanzu amma ai wannnan hatsari ne bai kamata ace ya bar zarah a wannan halin ba ..so ko gida bata kai ba ta sa aka kaita wajen sa . .. Daga nan wajen su suhan kuma sai wajen 6.0 9na yamma motar su ya iso abuja motar baida kyau so duk jikin su yayi tsami sun galabaita ga shi sun kwana sun wuni ana tafiya Ciwon ciki ke damun suhan amma tana kan daurewa Sai suka tsari keke napep zuwa anguwan su mum kankat aka musu da kudin su sabida dubu daya ne da ganan kowani mutum dan dole suma bada 3k aka kaisu anguwar maitama... "Da masifa mum ta shigo..tace kana bani kunya majeed yo ahakan Allah zai ji tausayin ka ya magance maka matsalan ka bayan kana take hakkin wata? Yace mum ban san komai ba nima ba bansan ta fice a gidan ba..tace yimin shiru Dama ai bazaka sani ba i felt soryy for zarah u shud see the way she's suffering over there babu wanda take tare da ita mahaifiyar ta ne fa ta gamu da babban hatsarin mota amma kai kana nan babu ruwan ka" yayi shiru abun sa bai ce komai ba ..amma daga ganin mood dinsa kasan meya ke ayyanawa aransa Tasan yayi nisa sosai bazai taba saukowa ba sai an samu suhan mum don dole ta sauke murya tana duban mood din nasa tace" i know suhan is important amma let bygones please.. ai munyi bakin kokarin mu ko my boy ?sai ka jira sakamakon addu'ar ka bawai kana zama kan hakkin zarah ba .. A sanyaye Yace toh naji mum ita zarahn suna ina yanzu? tace " emergency And bawai nace kaje ka gaisheh su ka dawo bane Ka tsaya mata be there for her she needs supots now ... Da kyar ya amsa don sam baijin karfin jikin sa ko kallon mum bai yi ba ya dau car key dinsa ya fice ya barta... Su suhan na bakin gate din mum tasa riga da zani da mayafi amma baba majeh bai bari ta bude fuskan ta ba complete Security ke interogating din su baba ibrahim na bada amsa... Driver na tuko mum daga hanya take kallon hayaniyan dake so ya tashi awajen... Duk ta kare musu kallo Kirjin ta ne ya buga ganin Mace mai ciki kamar suhan tun kan mota ya tsaya ta soma bada direction ma driver bai gama parking ba ta fito agurguje tayo kansu Ba tsayawa tambaya ko gaisuwa kan suhan taje direct ta yaye mayafin da take kare fuskan ta da shi ta watsar kasa "In shock ta ta tsaya.. suna kallon juna tuni gangar jikin su ya amsa "idon mum take ya kawo ruwa baki na bari ta soma cewa suhan..su..hannn.tana nuna ta da hannu cikin rudani Itakan ta suhan gama rudewa ba abunda take illa numfashi sama da kasa""jin mum na dada ambatar sunan ta ya sa ta gaggawtawa a firgice ta fada jikin mum ta kankame ta tare da sake wani rin fitinannen kuka.... "Kowa ya tsaya yana kallon su mum na kuka suhan na yi..mum muryan ta har baiya fita wajen tambayar ta ena ta shiga ta barsu cikin tsananin jimami da rudewa take shafo crying face dinta tana cewa " na nemeki yata na kasa samun sukuni meya same ki waya dauke min ke? Suhan Bata iya magana ita kam har su baba suka zo nan wajen da su mum suke.. Mum ta juya ta dube su da kyau sai yanzu ta ke gane kamar sa ...ta kamo suhan ta kankame ta daga gefen ta tace dama kaine ka sace min yata? Fushi da bacin rai na so ya soma sauko ma mum don atsawace tafada tana hawaye" tace kaine ka sace ta? ka gaya min ko na sa a harbe ka anan... Sam mum ta birkice "Baba maje ne ya shiga bata baki "yace mata kar tayi haka bata saurare su ba.. ai da ba su so agana ba da bazasu kawo suhan nan ba ..da kyar mum ta kawo fahimta da sanyi ma zuciyan ta ta kyale su Everywhere is alerted sojojin nan kaf sun garzayo sunyi tsege tsege suna jira tace ayi wani abu Aka bude gate suka shigo dukan su Dam ta riko suhan ta hana kowa taba ta sai ma kokarin boye ta take ajikin ta kamar itama bata hankalin ta... "Suka zauna a falo baba ibrahim ya daure sosai amma sai ya cigaba da dauriya don sai da yanzu hankali ta shigo masa yake jin kunyar Mum.. Ogah maje ne yayi bayani mai kama hankali cikin nitsuwa ma mum.. Har sai da tayi sanyi sannan baba ibrahim ya nemi garafa yayi kukan takaici da nadama Sannan suka hadu suka bata labarin kalubale da tashi fadi da sukayi akan suhan Da kuma cikakken labarin abubuwan da suka faru da ita tun daga bacewar ta .. "Majina da hawaye suka hadu ma mum suna sauka lokaCi guda idanun ta suka kumburo tsaban kuka da tausayin suhan.. "Ana labarin tana dada kallon ta tana tunanin duniya cikin kukan tausayi kaf saida zuciyan su yayi sanyi... "Suka shiga bata hakuri suhan kam ba ta magana Cos abun nadada raguwa ne ajikin ta abu daya ya rage ta dawo dai dai wato muryan majeed ... Mum ta sha mamakin da akace mata zarah ne tayi duk wannan abun she grow soo hot and angry bata iya nuna fushin ta ba amma a ranar sai da ta nuna matukar bacin rai da debewar albarka a kan zarah... Ganin suhan yadda ta jeme ta rame ba sai an gaya mata ta wahala ba jikin ta ya bata sosai.... Godiyan ta ma Allah daya sa suhan na dauke da cikin ta har yanzu tana tuno what if ta haihu wani wajen yaron ya bace? "Kan kace kobo aka ba su baba masauki da duk wani convenince ta kama yar ta suka je chan daki..." the first word da suhan ta furta bayan mum ta sa ta wanka da sallah.. Shine mum? Ina majeed dina yake? Pls ki kaini wajen sa kinji ...kamar ba ita ta furta ba ta koma tayi kasakai tana fid da ido mum ta dube ta cikin tsananin tausayi tace " majeed yana zuwa yata ki kwanta ki huta insha Allahu shi zai zo ya tashe ki uuhmm?...mum bata ma karasa rufe baki ba suhan ta mike ta haura gado ta kwanta ta rufe ido alaman baccin jiran majeed take ...mumy ta yi murmushi ta dan girgiza kai Nan ta shirya tsaf zata koma asibiti don itama ta matsu ta sanar da majeed suhan na jiran sa a gida kuma ta samu ta gamu da zarah.. Shi kuwa tunda ya fice baijin komai aransa yau ne rana na farko da ya soma jin zai sassauta tunanin suhan dinsa ya fuskan ci reality har Allah ya nuna masa ita... har ya kai asibiti yana muhawara da zuciyan sa akan haka yana bata hakuri ta barshi yayi adalci.. "Daga cikin dakin asibiti zarah ke amsa waya hawaye daya na bin daya sai ihu take cikin masifa muryan ta har na dishewa " tace karya ne wannan baku isa kuce kun tsige ni akan kujera ta ba i have legal entitles... no ..nooo... take fada cikin azababben firgici da rudani... An kashe wayar ma bata san ankashe ba ta daura a hannu akai ta na neman kwala ihu Mumy rabi dake motsawa da kyar daga kan gado tace me ake ciki zarah?me suka ce miki yata. Da kyar maganan ke fita Cikin masifa ta juyo tace i dont know just shut up mumy...kiyi min shiru .. Tayi nan tayi chan tace" shikenan I lost everything sun cireni a matsayi na a companyn hadin kai da minister .. yanzu duk wahalan da nasha kenan Ya tashi a banza kenan?i gave up my time. my effort.. my marriage ..and even my body To this career amma lokaci guda komai ya barni Zufa ke keto mata ..ohh god ta dafe kai "i got nothing now bani da ko sisi bare wani qaddara wayyyo Allah na na shiga uku.... My life has just finished right now ..ta shiga wailing tana cizan baki cikin tsananin damuwa meyasa basu da tausayi ne i gave my life in this _SAKAMAKO_ na kenan? Wani birkitaccen kuma kuntaccen kuka ta fashe da shi..sai da muryan ta yayi kamar ba nata ba Kukan data keyi ya sa mumy shiga wani yanayin mai