Sashe 155
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Page 60 continued* Murmushi kawai yayi ya mike tsaye tare da dauko ta duk da bedsheet din suka nufi wajen wanka... Washe gari da safe zaune take gefen gado ta kumburo fuska ta harde hannu don tun da suka tashi ta ta lura tun bayan sallahr asubahi yake ta waya da mutane daban daban wanda bata gane ba.. Wani bin sai taji Abun na bata haushi Ba wani Abu bane kuma illah tana mugun jin tana bukatar attention din sa.. gashi bata ma fahimtar me yake fada hira ne oder ne oho abubuwan sa duk a hade..shikuwa meeting yake da su mahmud tun daga US akan wata muhimmiyar operation. Yana lura da ita sosai Sai ya dauke kai ya share ta.. Daga bisani ma daya ga 10am ya kusan yayi sai ya fice waje alaman yana bukatar privacy.... Ranta ya sosu sosai..har tana neman ciko hawaye sai ta mike ta shiga hade chokolate ko zata na hadiya yana maida mata haushi.. Bayan ya gama meeting din su kayi magana da mahmud akan cewa a abuja zasu hadu nan da sati guda.. Yace ba komai shi ma yau ko gobe zasu koma nigeria ya lura mum dinsa ta matsu su dawo gida... Yana katse wayar ya sauke ajiyan numfashi ya kamo hanyar shigowa tun daga bakin kofa ya hangota ta dau katon ear phone dinsa ta kwama a kunne babu ko dankwali akan ta sai rawar kai take tana latsar chokolate din don dole..kallo daya zaka mata kasan da gayya ta ke yi sai ya sha mamaki shi dai yasan babu music sai dai in gidan radio take ji... besides wannan abun ma yafi alaka da alerts din harkokin sa na wajen aikin sa..so whats is she hearing? Ya tabe baki gashi ta sa hankali kamar da gasken wani abu take ji...dariya ne ya so ya kufce masa sai yayi wani tunani..ya shigo ciki daf da ita yace preety girl yau ni bazan ci komai bane yunwa fa nake ji... Tana jin sa sarai cikin ranta sai ta soma kukkuni"tace ace kusan 4hrs mutum yana waya baisan da yunwa ba sai yanzu" ai ba ruwa na ehe...ta dauke kai kamar tana jin abu tayi shiru ta kyale sa.. Yasan tana jin sa amma sai Ya cigaba da magana tana shiru fuska ba yabo ba fallasa yace toh shikenan Wayar sa ya sa a kunne ya ci fuska ya juya mata baya ta bisa da kallo har ya zauna kan gadon nata.." bakin sa na motsawa yana kuma sauke killer smiles kamar yana magana da wata amma bata ji ko kadan.. kallon sa kawai take ta ba bada lokaci taga ya shiga magana cikin salo yana dariya kamar ana bashi joke ko hira mai dadi... ajiye cup tayi ba tace uffan ba ta harde hannu.. Yana kula amma Ko ya nuna ya jawo pillow cikin shauki kamar baisan da ita ba anan ne ta soma zagowa inda yake a hankali don ma taji ko da 1 word ne..ya dan kyallero da gefen ido ya dube ta lura da reaction din ta ya sa yace ' naji sarauniya ta ki bari anjima zamu cigaba yanzu na gaji a kasale ya fada murya kasa kasa sosai .. Wani haushi ne ya balbale ta kawai sai ta yanke a ranta maybe ma da chan da wata yake ta magana .cikin rantan tace tab di jam Ace tun sassafe??? wannan wata irin tsinananiya ce haka" don ita kam tama mance akwai wata zarah duniya bare ta kawo masa uzuri Kawai sai zuciya ya debe ta fuuuu tayi waje cikin fushi.... tana bashi mamaki amma sai ya fashe da dariya ya ajiye wayar gefe har yana tuntsirewa... sai da ya dau kusan mintinuna 10 sannan ya biyo bayan ta da chokolate din a hannun sa.. Gaban ruwan ta zauna tana sa hannu aciki tana debawa tayi zugum ita kadai.. Dadi ke masa yawo a brain dinsa yanzu..yasan ko ba komai hes important to her yanzu tunda shes becoming more protective of him.. Ya ajiye chokolate din gefe har yayi yunkurin zai zauna daf bata lura ba sai da ta shako qamshin jikin Sa...ta dada daure fuska tana kokarin kaucewa din kar yaga tears din ta.. Cikin nitsuwa da sanyin murya yace nayi miki wani abu ne ? Why are you crying preety girl..cikin rarrashi ya sauke murya Maimakon taji fushi sai taji sanyi a ranta daya mata magana amma sai ta daure fuska tace im not crying ..me ma zai sa ni kuka..ya juyo ya kalle ta yace to meye ne?gaya min ...dazu Nayi miki magana baki amsa ni ba kuma kin fito nan.. Bazata hawaye suka soma sauko mata cikin wani yanayin shagwaba tace kar ka ma fara gaya min hakan ai kai ka fara share ni....ace tun safiyan safiya kana ta waya ita din bata hakuri ne ka kula mutane kuma ai ko kallo baka yi ta fashe da kuka mai dauke da takurrren kishi.... he likes that amma hankalin sa yayi mugun tashi daya ga suhan da gaske take har zuciyan ta abun yayi mata zafi... sai ya kau da wasa ya dan ja hannun ta zai goge mata tears din ta tashi cikin masifa tace noo dont touch me.. Yace hey listen...ta mike a fusace kamar wacce zata masa masifa amma bata san me zata ce ba.. Ya ce ohh bazaki saurare ni ba ko? Ta kumbura fuska ta hade rai tayi shiru ..ya jawo chokalate din ya taho gaban ta ya sa hannu ya Zare head phone dinsa ya damka mata wayar sa da cup din ta yace have fun...ya juya ya koma ciki. Kamar ta jefar akasa dan haushi don ta so ya jawo ta jikin sa ne ya rarrrashe ta . Amma me zatayi masa da waya..? Sai wani abun yace ta bude mana taga munanan yan matan da yake bi har yake waya da su...kishin ke deban ta ko chokolate din bata kula ba ta shiga kokarin bude wayar.. Gashi nan dai ta samu ta bude ciki amma akwai security akan contacts ... Ta rasa ya zatayi ta kai 30 minutes tana neman shawara da zuciyan ta Chan ta zaburo ta shigo dakin ta same shi ya gama parking kayan su tsaf..har ya koma gefe kan mat yana press up.. Cikin shagwaba ta zo gaban sa ta tsaya ...kallo kawai ya bita da shi suna hada ido ta dada bata rai..ya kamo hannun ta zuwa jikin sa yace wai meye ne kam..ta noke tana rigima murya kasa kasa tace ni dai ka bude min... yace mene? Ta masa nuni da contacts din sa bai sha mamaki ba ya sa hannu ya bude mata ko thanks din bata gaya ba ta tashi ta fice... Tun kan tayi nisa ta soma dubawa da wa yayi wayan taga duk jeren call daya 6am to 10am Mmerah sai few of secret numbers figures ne ma ...but who is this mmerah.? Sunan yayi mata kama da indian cud it be wayancan yan matan ne tace nooo wani abun ya ce mata yess kawai garin kiriniya tayo dialing number take ya shiga ringing... A firgice ta shiga rudani bata iya katsewa ba...kwata kwata sai ta shigo dakin da Gudu ta ajiye masa wayar sa kusa ldashi ta ja ta tsaya tsuru tsuru... Ya mike cikin mamaki yana duban ta..ya koma kan wayar sa ya dauka lokacin mahmud ya dauka har ya soma magana yana lura da abunda tayi sai ya ce oya zo nan ki amsa tunda dama ke kika kira. Tace ahm ahm ni fa ban san na kira ba juma ena so na kashe yaki mutuwa.ta marairace ko ya kula ya dauko wayar ya damka mata yace oya talk now...dan dolen ta tasa a kunne..muryan ta har na rawa tace salam hello... Mahmud yayi murmushi don ya saurara yaji maganan majeed din yace waslam amarya bata laifi...sai ta kasa cewa komai ta dago wayar a hankali ta ga eh fa mmerah din ne..amma ashe namiji ne ma. Da kyar ta sake suka gaisa da mahmud altho shikan tsokanan ta kawai yayi..majeed ya karbe wayar sa ya fita..mahmud yace kuna sha'anin ku majeed shiyasa baka da problem. Yayi murmushi yace fitina dai fushi take don meeting din dazu shine taje ta danna kira hmm mata fa sai a hankali..mahmud yayi dariya abunsa yace ai yanzu ka fara ..talk later suka katse wayar ya dawo.. Kunya take ji sosai amma sai ta fuske after oll ai ko ba din ma shi mijin ta bane shi bestfriend din ta ne so dole tayi fushi ko kishi... Cikin tsokana yace wai ma wayace ki kiramin aboki na...tace ai na gaya maka mistake ne... yace mistake ?shi mistake din Sai ya rasa wanda zai kira sai namiji meyasa baki kira yan mata ba....masifan neman tsokana yake amma kamar dagaske..a ranta tace what yan mata..? Ta juyo tace ban kira su ba ni shi din zan kira ki ta karashe kamar mai shirin fashewa da kuka... yace toh ba da waya na ba ni bana so Tace saboda me? Ta zaro mai ido shima ya zaro mata nashi yace saboda ena da kishi gaskiya bana son double friendship ni nika dai nake so kar ma a hada ni da wani if not nima zan nemo wata kawa kuma mutum bai isa ya ji kishi ba ....tace iyeeeee da chan na san shi ne ma? Wa ma zaiyi kishi Da kai ni bana kishi.... yace ohhh da safen nan waya yake hura fusakn dan aboki na ya kira ni Ta shagwabe tace lie.. ba shi bane ai cewa kake sarauniya mene mene zaka kira ta anjima kai kaji..... ya fashe da dariyan tsokana mai ban haushi yarda ta fada kamar an sata dole hannu ta kai masa kan kirji zata maka masa ta sa kukan shagwaba tana bubbuga kafar ta a kasa.. Abun na dada bashi dariya suka shiga zaga waje har waje chan ya jata suka tsundumo cikin ruwa.. Gaba daya sai haki take ya gajiyar da ita shikuma bai gaji ba ya shiga watsa mata ruwa a face din ta