← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 225

Sashe 212

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Dan uwa kuma bawan Allah yana hannu kidnappers masu bukatar a basu 20million kafin asake shi Yan uwa muna barar addu'ar ku Allah ya toni asirin su ya kuma kubutar da shi a hannun su lapya@hauwababa.* *Page 81 82* Dan fulani..dan fulani? Allahu akbar dan fulani har zamu ga juna ..ashe har zan ganka a raye... Wanda aka kira da dan fulani kukan kawai yake duk saje ya rife mai gefe da gefen fuskan sa bai iya cewa komai ba. Yanayin jikin sa da hawayen sa ya na nuna tsananin nadaman rayuwa boro boro har karkarwa yake Ogah rabiu ya jawo sa suka shige cikin gida.. Da kyar suka daina emotional draman su "Yace majeh? Duniya labari in baka zo ta ba tukun kaicon ka,, in kazo kuma halin ka ta ficce ka.. Naga rayuwa rabiu... rabi'u naga jarabawa naga karshe na...ya dada fashewa da kuka. "Kayi hakuri ibrahim ka dena daga min hankali zuwan ka nan ba karamin babban abu bane..yanzu dai ka samu ka sauya ka yi wanka kaci abinci ka huta ..in kaji kamar kana gida ne yanzu wani takaicin ma ai zai ragu "ya gyada kai kamar karamin yaro ya tashi ya aikata duk wayannan abubuwan Ogah rabiu bai barsa ya huta ba sai da ya dan zaga da shi yayi fes yayi aski ya rage gemun sa ya dawo dai dai suka dan zaga suka sha iska bayn sunyi sallah kafin nan suka samu waje a nan a cikin gidan oga suka soma hirar duniya... Oga rabiu yace" har yau hankalin na bai kwanta ba ibrahim..tunda ka samu zuwaira ku ka maida aure ban tashi ganin ka sai ranar da aka kaika kotu akan maganan nan daya kai ka prison..meya faru ne wai kam? Dan Allah ka fada min na dade ena zaune da ciwon nan araina Cikin jimami Yace hmmmmmm abun ba a magana majeh.. Amma bari na baka labarin abun talunda ga tushe. Kana sane dai na bar maryamu da yata suhan achan kaduna na zo nan lagos da dukiya mai tarin yawa da na karbe hannun inlaws dina. "Yace tabbas.. Yawwa ai bayan nan na zo na samu zuwairah da yaya guda biyu nasha mamaki ..nidai na barta da daya ne wato garba amma sai ga wani wai shi mati tace min ai dana tafi da cikin sa na barta nidai bance komai ba... dama ni nace zan nemo mana kudi na bata irin life din data ke so... kasan ta fa ita ta rika azalzala min azaba da fitina akan nemo kudin nan kamin ta zauna da ni Kuma a lokacin gaskiya ena son zuwairah Yana maganan ne idon sa sun gama cikewa da ruwa...ya danyi shiru ya jinjina sannan yace " tabb,... Allah sarki maryam yanzu hala Da kyar ta yafe min na cutar da ita na cuci kaina.. Ogah rabiu ba abunda yake sai girgiza kai cikin jimami... Ya cigaba" yace toh nazo na saida mutuncin yata arha na kuntata ma matata mairo na tafii na mance da su don na faranta ma zuwairah.. Da farko dai data ga uban kudin dana zo dashi rimi rimi take bina tana mun irin biyayyah da kundunbalan su na mata Na sake na rika zuba mata suna ci da yayar ta Kai... wani namiji ta kawo daga baya ya zo yana zama damu shine wannan joseph da akayi case dina da shi wai aka ce na kashe shi... oga rabiu yace but how comes? What happend meya maka ka kashe shi Baba ibrahim ya maida murmushin takaici" Su dai su ka lashe ni kaf suka maida ni akuya wawa jaki.. .sai da kudin nan ya kare kaf na dawo banda ko abinci da sutura da nake sawa wallhy a 1omillion din nan ban more ta ta ko wani hanya ba... Ya ja ajiyan zuciya cos da kyar yake fidda maganan suna masa daci a baki Yace" amma da kudin ya kare meye zuwirah bata sani nayi ba ..wanki shara.. markade.. tallan doya da kwai ma sai da nayi...ga masifa da cin mutunci Wallhy rabiu wata rana da tsintsiya take zama tana duka na tana zagi na a tsakar gida ta uwa ta uba ban isa kuma na tanka ba... Kuka ya fashe da shi anan gaban yace " wohoho _sakamakon_ abun da na aikata ma maryam ke bina wallahu a lokacin nadama ke dawainiya dani ga tunanin ya ta suhan yadda na cusa mata bakin ciki na rabu da ita ban taba zama mata uba ba" sai na dawo shasha bana ko iya hana zuwairah ci min mutunci wani irin bakin izaya ne ban gani ba? matar nan Ta tayyara mutunci na ta tona mun asiri har aron sutura na yi kai satan abinci ma sai da nayi aka shafa min toka aka ci min mutinci kororo kororo A layin kasuwa... Daga karshe shine na kamata turmi da ta barya da dan iskan da ta jawo min gida wai dan uwan ta shi wannan joseph din ashe shine ma baban yayan nawa dabnake buga kirji akan su...wallhy duk ba ciki na bane na shi ne Ranar na kasa daurewa raina ya baci matuka zuciya ta debe ni nayi musu kaca kaca jina jina daga ranan na soma tunanin komawa kaduna ko da kafata ne na tuba na nemo gafarar iyali na ama its too late..ni dai nasan ban kashe kowa ba Suka hade min baki kawai sai naga an zo an kame ni aka laka min laifin kisan kai wai na kashe joseph..na rasa yadda zanyi gashi na shaida da baki na na buge su kaji dalilin da ya sa na nemo ka ranar kenan ko? Oga rabiun ya kasa tsayar da hawayen dake bin kuncin sa yana kuka mai dauke da tausayi da jimamin rayuwa... Yace abokina tabbas wannan shine _sakamakon_ mun dau rayuwa mun daura bakar kanya akan mu .. Amma Nagode ma Allah da ya sake bamu damar da zamu sake yaye wani shafin mu daura wani kafin ya amshi ranmu.. Me ya faru aka fito da kai?baka gaya min ba..kuma me kake tunani yanzu zamu sa agaba naka ra'ayin Ya jin jina Yace"ikon Allah kawai nagani rabiu.. wato naje prizon din nan ena nadama amma Allah bai barni haka ba ya hada ni da wanda suka san addini suke koya min abubuwan da na watsar..hankali na ya tashi sosai ga mafarke mafarken maryamu da nake yi a haka na shiga tsundum ena neman yafiya da adu'an samun Sauki da sauyi a al'amura na ai gawan zuwairah aka tsinta shi joseph din da akace na kashe shi ya kashe ta "wai ya ce ta kwana da uban sa akan gidan gado da yake so ya karbe ya hana yanuwan sa sai taki shine ya mata dukan mutuwa Bayan nan Ai bai samu yayi escape bane aka kama shi nikuma aka bada izinin Asake ni.. Ya sa hannu ya dauko wani ledar poly bag daya Zo da ita a dunkunkune yace ka ga wai compensation nan dubu dari biyu an bani daga kotun bayan gari.. .naji kana tunanin me zamuyi nan gaba kaga sai mu nemi nakan mu muyi sana'a mu cigaba da rokon Allah ya yafe mana.. Sai dai kafin nan zanje kaduna na dubo su maryam koma yaya ne na nemi gafarar su kafin nasan matsayin rayuwa ta... Ogah rabiu yace wannan duk yayi Allah ya shige mana gaba.... Anan suka zauna hira sosai sukayi daga bisani ya na dan karfafa masa gwiwa har suka kwanta bacci.. duk kwanakin nan suna gida suna shan labaran duniya da suka fuskanta da nadamar su suna kuma dada kawo shawara ma juna yadda zasu kai kansu next level After 3 days suhan bata fito ba baba rabiu ba shima bai ganta ba sai ranar bayan ya raka abokin sa ibrahim dan fulani tasha zaije kadunan kafin ya hango ta riki riki da aikan nika zata kai engine surfe sai ja take da cikin ta gwanin tausayi Ya zo ya karbe daga hannun ta yana mayar mata irin murmushim data saba sakar masa mai alaman gaisuwa... Its seems like yana mugun ganin kamar ta da matar abokin sa maryam amma he cant say" Shi ya taimaka mata as usual ta kammala komai sannan ta shige gida.. Tun daga nan sai Shiru shiru baiji labarin suhan ba bare mahaifin ta da yaje kaduna nemo du da ummah.. Baba ibrahim Ya sha wahala sosai cikin kwana ukun don Babu su babu labarin su gashi mutanen da ya sani kowa na jan jiki da shi suna wulakanta sa da kyar aka masa kwantacen shamud residence yaje nan ma akargame sai uban securities Their personality Is higly confidential musamman ma da capt majeed ke wani halin tashin hankali yanzu iya bayani yayi akan yar sa ce suhan .kuma ya zo nema amma sam suka ki ma daukar maganan sa serious bare su gaya ma har aje ga fada ma majeed Duk sun dauka irin mutanen banzan nan ne da ke zuwa da karareyan su don sunga kullum majeed na doubling millions akan wanda ya samo masa matar sa a media.. Da baban suhan ya matsa sojoji suka kama shi suka zane shi tsaf da dorina suka bashi purnishment da kyar wani ya tausaya masa ya fitar da shi daga wajen ya kaisa har tasha Yace masa wallhy bazan maka karya ba..yata na aura ma mai gidan ena so ne nagan ta dan Allah.. Securityn yace baba babu wanda zai yarda da kai saboda akwai matsala yanzun da aka fuskan ta Ita wanda kake neman ta bace yau wata guda kenan kuma ansa kudi mai tsoka ma duk wanda yakawo ta da rai ... mutane dayawa sunzo nan da karya kala kala Wasu ma na nan akulle ka rufa ma kanka asiri ka tafi kawai Allah ya baka sa"ar abunda kake nema Wani irin Shock baba ibrahim ya shiga" suhan taba ce? Ya daura hannu akai yana salati hawaye ne na ban mamaki ke masa ziriya akan fiskan sa "yace shikenan ni na salwantar da yata gashi ance maryamah ma ta rasu ba san inda makwancin ta take ba
Chapter 212 · 0% Book details