← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 225

Sashe 35

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

dakin ya soma gauraya yayi dim.. bayan kamar 2hrs lokacin da shike da safe aka fara wajen 12 saura kenan aka kankare mata dilka aka durje shine lightly akayi mata wankan madara da ga kai har kafafun ta.. A Haka rayuwan suhan ya kasance na kwanakin safiya da maraice ana mata irin haka har na kwana 12 chas kafin kace kobo fatan jikin ta ya tande ya gogo fes har na ban mamaki Sukan su masu gyaran sunyi enjoying companyn su duk dama daga baya ummah ta hana su anty jamila da zuby zuwa gidan tace "su saurara haka kar su biye ma mum tana so ne kawai ta faranta ma suhan and den yakamata su tsaya su kare mutuncin su dan a daraja su nan gaba.. Sun gamsu da hakan shiyasa yanzu sai dai suyi awaya kawai ake gaisawa dan ..dole zuby tayi karya ma madam bola cewar baban suhan baida lpya rai a hannun Allah suhan na jinyar sa a chan garin su amma zata dawo soon duk dama tasha masifa kam amma hakan madam bola ta bari.. Dan kwanakin da basu zuwa ne mum itama ta samu daman gwada ma suhan wasu abubuwan daya dace musamman yadda zatayi amfani da highly modernised items na cikin gidan har dakunan su.. Tsaf suhan take yanzu sama samabita kanta tana enjoying new looks dinta..jifa jifa su kanyi hira da mum duk da ma bai kaiwa minyi 20 amma sosai mum take apreciating ladabi da kunya ga kuma sanyin hali irin na suhan.. Ranar da safe Mum tana zaune kan sallaya kira ya shigo ...da murmushin ta ta dauka yace"mum im back...anan ta dakata sai da tayi godiya ma Allah kafin "tace my boy bani labari mai dadi naji..yace aiki san adduar ki bata taba fadi kasa domin kuwa anyi nasara sosai yanzu haka wasu daga cikin yaran sun koma hannun iyayen su wasu an maida su garin su na damka su ma hukuma... mum tace "masha Allah cikin tsananin farin ciki tana sa mai albarka ""Ena fatan kuma zaka dawo gida soon right? Yace yau ma zan dawo mum shiyasa na kira na sanar dake kiyi min irin abincin nan naki mai dadi mum kinji? Dariya ma yabata tace just give me time kamar anyi angama.. dan hira kadan sukayi sannan ya katse wayar sa.. Ko da ba ace ba yadda mum ta fito yau kowa agidan sai da yaga annuri akan fuskan ta .... Suhan already ta gama shiryawan ta tsaf dogon riga ne na kanti mai guntun hannu kunya ya hana ta lekowa Mum kam bata damu ba sai chan yamma lokacin tasan yana dap da shigowa gari Cikin dabara da hikima ta sa suhan da ita kanta suka shiga kitchen anan suka shirya Masa abincin mai kayatarwa babu abunda ba ayi shi tamkar bana mutum daya ba haka aka jere su tsaf cikin tsafta ... Suhan tace hjiya baki zamuyi ne..tace uhm uhm kije kiyi wanka tare zamu ci abincin nan bada jimawa ba. Daga nan Suka rabu Suhan na shiga part dinta motoci guda uku masu lpya suka dire a compound din... zarah ne da Ahmad da faiza suma sun dawo daga scotland sai suka biyo mata it was almost 7.40pm bayan isha'i.. As usual suit ne ajikin ta bakake kirin kanta a yashe yake da brazillain hair na zamani sai yarfa shi baya take cikin rigima da kasaita Surutun su ya gauraye gidan Babu gaisuwan kowa da ta amsa daga cikin maids har suka kai palor da shike jirgi suka biyo babu alaman ko wani gajiya ajikin su sai suka zauna nan palor su kaci gaba da hirar abubuwan dayabkai su scotland bata damu ta duba kowa a gidan ba.. 30 minute later lokacin mum ne ta soma lekowa tayi dressing irin na yan maiduguri dogon sari mai mayafi purple tasha mamakin ganin zarah a gidan unanounced amma sai ta fuske tayi murmushi fuska ba yabo ba fallasa ta karaso.. Su faiza da Ahmad suka gaisa da mum da kyar zarah ta iya gaishe ta ....mum tace ya jikin hajiya rabia ?zarah Bata ko samu daman amsawa ba sukaji dirin motoci da convoy din security alaman captain ne da tawagar sa suka diro ..mum kam kamar an tsoma ta a aljanna ko ta kansu bata sake bi ba tayi waje tarar danta.. Zarah kam ko ta motsawa batayi ba cos ta riga ta nuna ma friends dinta ita isashhiya ce wajen mijin ta. so.. shi yake binta ita bata zubda girman ta wajen bin miji Bayan tsayuwar motoci ya fito suka rungume juna da mum suna dan hirar su na kewa ..... daya shigo ciki anan ma Still ahmad da faiza suka gaisa da shi wacce tuni ta kasa samun nitsuwa don har yanzu captain bai fita a ranta ba musamman ma yau data ci karo da shi a uniform again.hes soo hot Mum tace ai kuwa zuwan ka yayi dai dai the house is full now yanzu kowa ya tashi muje kuyi refreshing kanku a dinning table...suka danyi dariya musamman faiza dake cewa how lovely mum wallhy dama am starving ...dauke wuta zarah tayi hoping that captain shi zai soma mata magana amma sai ya dauke kai.. Mum ta wuce chan sama bayan yan mintuna kadan sai ga ta da suhan a bayanta sanye take da riga da skirt na kanti white and pink da mayafi sharara white sai sanyin qamshi dake fita ajikin ta. Dukkan su maida kallo su kayi wajen ta barin ma captain daya soma comtaplating ko sauya ta akayi... Suna saukowa suhan Ta dam ja baya ta tsaya Mum tace yata taho nan mana kinga bakin namu sun zo sai ayi serving din su ko? ..a ladabce suhan ta gyada kai gaban su ta dan rusana kai fuskan ta dauke da confidence da gwarjini tace sannun ku da zuwa...murmushi ne ya kufce ma Ahmad jin angelic voice dinta aka bar faiza da sake baki hannn tana kare ma hallittan suhan kallo zarah kuwa zufah ne ya soma keto mata a ranta tace who the hell is this badai ace itace amaryan gidan nan ba? Captain ya dakata kamar baya kallon ta amma a zahirin gaskiya ita din yake kallo.. jira yake yaga ko bazata gaishe sa personally ba ..ko kammala tunanin nasa baiyi ba tace sannu da dawowa sir.. Mum tayi murmushi a boye....shikuma tare da dauke kansa yace thanks.. Nan mum tayi mata umarnin ta yi serving tba musu tayi ma kowa dai dai ba kuskure ..dan dole faiza takawo hira don ta lura kowa hankalin sa nakan suhan ne alokacin Musamman ma zarah. Ana cin abinci kowa a ransa yana so yaji ita waye..suhan ko ji take kamar ta tsala ihu don bugun zuciya da fargaba takasa dago kai a hankali take kai abinci bakin ta cos kowani dagabido saita ga zarah tana watsa mata mugayen kallo.. ..daga karshe Faiza ta kasa hakuri tace mum ..wannan kanwar captain ne ya naga bata son magana? Mum ta danyi dariya tace lahhhh no my dear ai wannan itace amaryan gidan nan pls meet her.. ta dan dafa suhan wacce ta dago fuskanta da kyau dan dole "mum tace wannan itace suhan abokiyar zaman zarah.. Tare da droping spoon a razane zarah tace What? Kikace meye mum? Mum bata amsa ba Harara ta watsa ma suhan bazata..kafin mum tace of cous itace amarya.. kinga badon kinyi tafiya ba dake ce zaki yi introducing nata ma freinds dinki i am right?..faiza ta maida wa mum dariyar yake tare da kai ruwan sanyi bakin ta..wow basu yi tsammanin haka ba..wannan kyakyawan karaman yarinya fresh blood ma captain? Lallai mum ta dauka da zafi faiza ta raya aranta Ahmad ya dan tabe baki yace dats lovely she preety ya amida maganan kan captain wanda murmushin doe kawai yayi...sannan ya dawo kan suhan yace congrat mrs MJ junior "suhan tayi murmushi ... captain koya ya sake daga ido abincin sa kawai yake bai kula kowa ba ...mum ta dan kalle sa tace my boy is enjoying the meal i ques nan ya dago da karamin smile yace ure perfect mum i m totally loving this....nan ma mum ta dan dafa suhan da farar ta "tace all thanks to her im glad yau kowa yaci abincin amaryan gidan na ""wow!!!! Ahmad da faiza suka fada a tare cikin mamaki mai dauke da jinjina Zarah data gama kuluwa..watsi da plates din gaban ta tayi cikin hatsala ta haura chan sama cikin fushi da fusata kowa saida ya dago nan wajen ana binta da ta da kallo...... *More coments more tsayin pages tunda bazan samu dama yin sau biyu ba..i think long pages is enouhg ai *surriem* [9/13, 13:44] Hapsy: * BRILLIANT WRITERS ASSO
Chapter 35 · 0% Book details