Sashe 27
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bace ni nasan wacece ita... Mum pls ki saurard ni ki sauya min amma banda wannan inkin zanca kowace ce zan zauna da ita i promise .. Just shut up,mum ta daka mai tsawa..kace kasan ta ?a ena kasan wacece ita da zaka fada min haka karyan banza kawai..i know what you think about her kuma shikadai ne aranka and all this is blund majeed duk zargi kake.. ni nan da kaina na bincika naga halayen ta shes not a thief kamar yadda kasa aranka satisfy?..uarinyar nan bata taba dauke abun wani ba for god sake abu bai wucewa awajen ka ne? Yaa budi baki cikin rikicewa zai mata bayanin ganin suhan da yayi a hotel mum tace kamin shiru kawai In dai wata ke zuga kaka bijire ma zabin da namaka sai kafada min ba kazo min da silly reasons din ka ba ..this is not a joking matter na kawo yarinya gidan nan kazauna kana cin mata fuska a gabana . Ni dai ita na zaba maka kuma da ita zaka zauna, and this is finale bana son ka kuma maimaita abunda kayi yau har abada na fada maka kenan..mum ta daure fuska Yayi shiru bai amsa ta ba alaman baiji dadin abun ba kwata kwata sai ya maida kansa kasa cikin rashin jin dadi.. mum na lura da shi ji yayi tace to shikenan na fahimce ka yanxun.. Toh sai ka tashi kaje ka sake ta saki uku ta bar maka gidan nasan ka isa da ni..sannan kazauna da wanda ka xaba makan ka ..mum ta wuje gaban sa a fusace tayi waje yana binta da kallo hankali tashe har ta bace. Wani zazzafan ajiyan zuciya yayi ya tashi jiki a sanyaye yayo waje mota ya dauka ya buga horn aka bude masa gate ya fita. Bayan tafiyar inna A hankali mum ta bude kofar dakin suhan lokacin suhan din na kai kawo hawaye sun gama wanke mata fusa ba irin juyi da batayi ba don kuwa ta tsorata sosai da maganganun captain. Mum ta tsaya tana binta da kallo na 2 secnds tausayin ta ne ya kama ta..suna hade ido kuwa suhan ta rugo a guje har mayafin kan nata ya zare kansa tafada kasa ba shiri ta zube kan kafar mum ta fashe da kuka mai ban tausayi...indai har matan nan na da digon imani yau zata sa ya warware auren nan wallhy bazan iya zama da wannan mugun ba..da kyar suhan ta ce hajiya dan Allah ki tausaya min ki kaini wajen ummah na bana son auren wallhy bana so..... mum ta kasa magana tana jin takaicin halin da suhan ke ciki..ta dada cewa kiyi hakuri hajiya nasan nai muku laifi keda ogar sir amma daga yau banna kara zuwa kusada da motar wani bare na taba wallhy tsautsayi yasa ni shiga booth dinsa kiyi hakuri ki sallameni agidan nan bana sake shiga tsabgar ku kinji hajiya?ta cigaba da kuka Jikin mum yayi sanyi lokacin amma sai ta daure ta dago ta sama kuka suhan keyi tayi fuska kalar magiya tsakanin ta da Allah tana rokon mum duk yanayin ta yanuna tsoro da fargaban zaman nata da su.. Mum ta riko hannun ta tace,yi shiru abunki wannan ai ba matsala bace zan miki duk abunda kike so kiyi shiru kinji?.. suhan na kan kuka mum sai ta dan jawo ta rugume ta calmly cikin wani yanayin mai sanyi da saurin kwantar da hankali tana tapping bayanta ita kanta suhan saida tadan ji dama dama ta rage sautin kukan nata..daga bisa mum ta kamo hannun ta tace'zo nan muje Cikin bayi suka nufa mum na tsaye ta kunna mata ruwa gaban sink tace wanke fuskan ki sai ki sami nitsuwa muyi magana kinji? Tadan shafo black and smooth hair na suhan cikin kulawa da lallami.. Ita ko Batace uffan ba takai hannun ta ruwan na tsiyaya jin sanyin ruwan na ratsa ta wani kuka ya sake kufce mata... Mum tace ya salam suhan kiyi hakuri mana yata...da kyar suhan ta dago tana shesheka tace "hajiya kinyi alkwari idan nagama zaki kaini wajen ummah na? Murmushi mai dauke da tausayi ya kufce ma mum tace ' idan kika yi duk abunda nace kiyi ba gardama zan miki abunda kike so yanzu wanke fuskan ki ki kimtsa ena jiran ki a daki Suhan ta gyaada kai a sanyaye mum ta fice ta bata wuri. Kan couch na dakin suhan mum tayi zaman ta tare da sauke ajiyan zuciya..cikin ranta tace" duk majeed ya jawo min wannan fitinan yabi ya tsorata yar mutane da silly thougts dinsa.amma bakomai auren nan anyishi kenan kuma ba mai raba shi sai Allah... Captain kuwa Daga motar sa yake yawo yana zaga gari shikadai..wato ma shi za'a araina ma wayo shidai kawai ya ajiye a ransa cewa suhan da akwai abunda ya kawo ta gidan sa ranar data shige masa booth har kuma gashi tayi nasara akan mahaifiyar sa .could be kudi take so ko kuwa wani abun daban? Dan jingina kai yayi da seat ya lumshe ido yace" da ni take yi,in har tsabga ta ta zabi shiga daga yanzu zai zame mata na karshe a rayuwar ta...ba ta aure ni ba? Ni kuwa nasan me zan mata.../hmm daga yau zata fara gane banbancin tsaki da tsakuwa. bayan kamar 15 mints suhan ta fito a sanyaye tana rakubewa don sai da tadanji normal take fahimtar yanayin ta kanta babu ko dankwali ga tsarin rigar yana dan nuna shatin boobs dinta a sarari.. Kunya ya dan kama ta mum na lura tace karaso mana suhan zo nan ..tayi saurin isowa ta rusuna gaban mum cikin ladabi da saukar da kai Mum tace "suhan yata, kafin na fara cewa wani abu anan zan fara baki hakuri don ni nayi sanadiyar saki halin da kika shiga a yau.. kiyi hakuri kinji ? Mum tafada tana dafa ta.. Sunkuyar da kai kasa suhan tayi bata amsa ba mum ta cigaba da cewa" nasan bakijin dadi a ranki saboda auren nan bada izinin ki ko da sanin ki akayi shi ba amma ena so kisani ni mace ce kamar ki kuma kamar uwa agare ki nasan kinada yanci da kuma rights akan yi makanki zabin mijin aure sai dai qaddara yariga mu fata amma fa kisani nice silar yin haka amma bani da ikon sa haka ya faru sai Allah... inda ba nufin Allah a auren nan wani mai kudi ko mugunta ko iko bazai sa ayi auren nan ba..kinga tunda an daura kuma kin shigo dakin ki da sanin iyayen ki da albarkan mahaifiyar ki why not kiyi hakuri. Ena miki kira da ki sa ma zuciyan ki ruwan sanyi ki dauka wannan a shine tubali na farko wajen amsar jarabawan ubangijin ki na rayuwa kuma insha Allahu xakiyi nasara... Nan Suhan ta dago ta dubi mum baki na rawa tace" amma baya kaunar zama da ni yanzun kenan sai na jira sai mun fahimci juna kafin mu zauna lpya ? Wallhy nima bana son shi kuma nasan shima baya sona in nayi hakuri nayi biyayya ma qaddara toh shima xai yii kenan,..hajiya danki ne fah to meyasa zaki aura masa wanda bai yarda da ita ba ce min yayi ni barauniya ce watsasiiya ...har zamu xauna a hakan kenan? gaskiya ni ena ga amfanin auren baida yawa Rashin sa yafi yawa kitaimaka yadda kika hada shi ki warware shi ni zan koma wajen ummah na..pk na rokeki ta karashe cikin kuka mai ban tausayi Mum tayi ajiyan zuciya tace kiyi hakuri suhan ki cire wannan tunanin nan aranki pls,..i know your fears.. duk wannnan naji kuma na fahimce ku duka daga ke harshi akwai rashin fahimtar juna tsakanin ku..shi bai sanki ba amma ni na sanki kuma ena alfahari dake da kyawawan halayen ki shiyasa na zabe ki a matsayin wacce ta dace da shi na zaman har abada ko nayi laifi ne danayi hakan suhan ke fa macece wata rana zaki haifi danki namiji kuma zaki so masa rayuwa mai inganci'ke tamkar alkhairi ne gare mu baki daya duk da bansan ki sosai ba amma na aminta da ke da tarbiyan ki yadda baki tsammani.."suhan shima ni na haifeshi na raine shi har yakai ga yadda kike ganin sa haka abdl majeed bazai cutar dake ba na tabbata zaku zauna lpya lokaci zai tabbatar mana da hakan. Suhan ta dada fashewa da kukan rudani batace komai ba Mum ta riko hannun ta itama ta dawo kasa daf da ita"tace""..yau ko nice a matsayin ki ba abunda zan bukata illar kuncewar wannan aure na fahimce ki ata,..amma ki daure kisani wajen wata mahaifiyar kike yanxu mutuncin ki da darajar ki ni xan kare shi ke amana ce na gaskiya da gaskiya daga mahaifiyar ki. Mahaifiyar ki ta fahimce ni sosai kuma na ji dadin kasancewar ta mai imani da sanin darajar aure wajen ubangijin ta.suhan kema ko daure kiyi koyi da ita kinga ba kowa Allah ke bashii wannan rahaman imanin ba..Kiyi hakuri kinji yata ..nayi miki alkwari in har daga baya naga cutarwa ce auren nan da kaina zan maida ki gidan ku kinji? Suhan ta gyada kai muryan ta a dishe da kyar Ta amsa da cewa shikenan hajiya..tunda ummah ta hakura nima na hakura zan zauna amma ..ammma..wallhy tsoron shi nake ji cikin kuka ta karashe gwanin tausayi.. Mum tace ,karki damu babu wani abun tsoro wajen majeed zaki fahimci hakan kinji? Kuma kukan ya isa haka Yanzu ki tashi ki kimtsa kiyi baccin ki gobe xamu karasa maganan mu kinji yata? Suhan ta amsa da toh.. kanta na kasa still hawayen na zuba.. Mum ta mike tsaye tare da cewa Allah ya miki albarka sai da safe...ta amsa a sanyaye.. mum ta yi waje ta barta. Tajai minti 10 awajen tana zaune Wani ajiyan zuciya tayi mai nauyi idon ta sun haura don kuka ..ta rasa meke mata dadi yanzu tunanin meye guda daya zata yi? Zaman ta da captain ne ko tunanin yadda familyn ta ya wargajeh ayau.. bayan kamar minti 30 ta mike ta shiga bathrum bata iya amafani da shi sosai ba don haka shower kawai ta kunna ta mutsaka gel mai sanyin qamshi ta samu taji dai dai sai tayi alwala Anan ma dakin Bata iya