← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 225

Sashe 113

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mai kularwa yace" tooooh" ahh toh shikenan ai..yau zaki fara a kaina kenan don baki fita a dakin nan sai abu biyu ya faru ko ki banu kudi na ko ki kwanta min a gadobya buke da dariya.. gaba daya sai ta rude tayi har ta kawo tununanin in tace kudin baiya hannun ta hala yayi considerin sai tace" alaji nifa bani na karbi kudin ka ba zuby ce kuma dan naki nayi maka abunda kake so ai nafada maka ni ba yar iska bace wallhy ban taba yi ba...yace to ai duk layin ku daya" in ba ba ke kika karbe kudi a hannu na ba ai da sunan ki aka karba tace min zaki zo ki bani zuma na lasha shine don rainin wayo zaki maida ni mahaukaci ki gudu ko? Cikun kuka Tace to shikenan ni ka kyale ni na tafi mana ai zan nemo maka kudin ka .yace ah a ban aminta ba..ke din ?tabbbb Allah ya kiyaye na sake neman wani abu daga gare ki macuciya kawai to yau bana barin ki... ai dama hausawa sunce ramakon gayya yafi na gayya ko? toh nima yau zan fanshi kudi na da raina min wayon da kawar ki tayi min ajikin ki ba ruwana da ke ba yar iska bace... tsalle ya buga ya haura kan gadon tsaban tsoro sai data fada kasa garin gudu amma bata gaji ba ta kuma tashi da sauri tana ja da baya...a dai dai wannan lokacin ne suka kai daf bakin kofa daga nan captain ya soma jin maganan crystal clear dama tun tuni a sama sama yake dauko wasu bai fahinta sosai gashi hankalin sa dubu ya tashi idon sa har sun gama kadawa... Tana kaiwa bakin kofa ta juya a razane cikin kuka Tana jijjigaawa tana kiran neman taimako a firgice...daga waje yana jin ta wani zuciyan tace masa ya shiga mana wani kuma ya dakatar da shi ...sai ya kasa taimaka mata ya bude kofar.... Dariyar alaji yake ji da kukan suhan alaman hankali kwance yake tahowa gaban ta..yana zuwa ta sake kofar ta manne tana karkarwa zuciyan ta kamar zai fice tsaban bugu wani irin tuma yayi ya dada matse ta gam...ta tsala ihu yace shhhhhhhh" in kin ga dama kiyi ta tsala ihu yau abunda naga dama shi zanyi dake..ta razana so magana kawai take fitarwa bata ma san me take fada..tace dan Allah kayi hakuri wallhy bani bane na karbe maka kudin ka dan Allah kar kamin wani abu..ka barni na tafi. rikicewan nata na burge sa don haka sai ya shagala wajen mayar da abun kamar abun wasa yana jokes da shi. ..yana cewa kedin banzan kedin wofi waye uban ki? Zan wulakanta ki na kwana lpya... Mata nawa na kayar kece zaki min gwale da jikin ki ?...ai baki isa ba tunda da sunan ki a aka karbe kudi na sai na fansa in yaso kuje chan ku karasa ya fashe da dariya . suhan kuwa ba abunda take in banda rokon sa . ... daga bakin door kuwa sai yanzu captain yaji kan maganan da kyau cikin mamaki yace what? Bindiga sa ya zare a fusace ..yayi setin kofar don ihun da suhan keyi ya tabbatar masa an sa jarfi ne ake jawo ta .... yana gama auna lokaci ya danna sai tauu tauu jikin mabudin kofar ba shiri mabudin kofar ya ya budu" jin karar bindiga daga alaji har suhan kowa yayi miisplacing yana neman boya.. captain ya banko kofar a zuciye hannun sa rike da gun din.... Kasa ta rusuna ta kankame jikin ta waje daya tana karkarwa ko iya kuka ma batayi don tsoro .. alaji na hada ido da captain yayi yunkurin tashi sai tauuubya dame kafar sa daya ya buga ihun yana birgima.. wanda ya dada firgitata ta mike tsaye a daburce tana neman zaucewa hannu daya ya sa ya fizgota gefen sa da kyar hankalin ya zo mata ta daga ido ta kalle sa suna hada ido ta fada kirjin sa a tsorace ta tsala ihu mai razani..... ya san ta firgita sosai its possible bata taba jin karan bindiga ba sai yau... alaji kuwa na kasa rike da kafar sa yana ihu dan azaba..... Captain fushi yake yi sosai sai Ya kasa sauke bindiga duk dama ta masa dabai bayi ta kankame sa sosai tana kuka" sai ya rasa meke masa dadi haushin ta ne da tausayin ta suka hadu suka kawo sa wuya gaba daya idanun sa sun kada sunyi ja jajir... tun tuni kukan takeyi amma bata ce uffan ba tana jin yadda yake daka ma alaji tsawa gwanin ban tsoro ita kanta taka sa tantance jikin ta da nashi na waye yafi na wani karkarwa... Ganin abun na neman firgita ta sosai saibtayi magana "Disasshen muryan ta ya tsinkayo achan kasa kasa tana cewa ""dan Allah ka fitar dani anan ka taimaka min dan Allah mugu ne zai min wani abu kuma ni ba nayi.... kuma ni bani na karba masa kudin sa ba..."cikin kuka mai ban tausayi ta karashe ....koda tayi maganan sai yaji gaba daya ya sace' yasan bata cikin senses dinta har yanzu jikin sa sai ya mutu yayi shiru ya sauke bindigan kasa" ya sa hannun sa duka biyu ya dan dada matso ta jikin sa shima yayi ajiyan numfashi mai sauri don ya taimaka mata tadawo .. jin ta samu close contact da shi sosai sai ta dada shigewa jikin sa har very hot breath dinta yana rabar fatan jikin sa ta ciki.. . A take suka lumshe ido tare ya shiga shafa suman kanta yana maida su baya a hankali cikin sigar rarrashi..har tazo tafara rage kukan da kadan kadan Yadda take jinta tsam a jikin sa kuma yake bi da hannun sa yana shafata ko ena sai ta soma shiga hankalin ta sosai ...jin ta sauke numfashi ya sa shi saduda yana kokarin dago ta sai ta mike amma kanta a kasa tana shessheka yau dai tasan tayi masa laifi.... shikuwa ba abunda yake kallo illah dressing din nata sai yau ya gane ashe ma uniform din restaurant ne ajikin ta .... ji yayi wani fushi da tashin hankali na tsatsafo masa tun daga kasa kansa na hayaki"" budan baki yayi a fusace zai tambaye ta ..sai ga securities sai ya dakata... anan aka yo kan alaji aka kama shi.... Tun kafin su gama ya jawo hannun ta a fusace tamakar wanda zai daga ta sama har tuntube take ja bai damu ba Suka fito har waje enda ya ajiye motar sa Baya ya bude ya cillata ciki a zuciye ya rufe ya dawo ya kunna motar suka bar wajen Kuka ta fashe da shi gashi garin firgici ta yasar da beret din don Haka ba ko gwali akanta sai ta hade kai da gwuwa a bayan motar ta shiga tsula kuka wanda a hakikanin gaskiya dada kara masa bacin rai take.. Bai kula ta ba Sai da ya danyi tukin kadan kafin yayi parking gaban restaurant din madam bola...ya fito waje bai shiga ba ya sa wani mai irin uniform din Suhan din aka a kirata .. jiki na bari madam bola tafito tana yake it seems kike tau manya ne ke zuwa shagon ta.. ya sauke fuska ba yabo ba fallasa don iya kokari yayi wajen boye fushin sa ta dan rusuna a ladabce tace'sannu da zuwa sir kana bukatar wani abu ne..?toh ka shigo mana ko oder ne. ya danyi shiru daga baya yace " well yes ena bukatan wani abu amma bada ga shagon ki ba... amm ena so kimin wani alfarma daya,.. ko kinsan wata maikaciyar ki mai suna suhan .?..tace yes yes ahh suhan kuma..! ai tana da kokari sosai na she dey try for me pass oo..ai kuwa ta iya aiki. Baice komai ba ya bita da ido tace" amma sir alfarman me zan maka haka ko kana neman cook ne?ai kar ka damu ni zan iya nemo maka wata ma in kana so... Ya dan yi friendly scof yace "no thanks dama na sani ne kawai.... Kudi ya zare daga pocket dinsa wanda shi kansa baisan nawa bane ya mika mata.. cikin mamaki ta karba tana juyawa "yace nadam daga yau suhan ta bar aiki anan wajen.. I give you this money cos its an unxpected notice kuma kin gaya min tana miki kokari ko? A dan rude ta dago ta kalle sa yace"toh u can find urself another gal...abun ya daure mata kai tana so ta tambaye sa shidin waye da zai sa doka kai tsaye akan yar mutane ne.. cos tasan dai suhan iyayen ta bakomin komai bane amma yanayin fuskan mjeed da kwarjinin sa yasa ta kasa tambayan sa sai ta ce yes sir..thank you sir....yace and please ko da wasa ta sake zuwa nan call me ...sai ya ciro personal card dinsa ya mika mata.. Ya juya ya koma motar sa ..suhan na daga ciki tana dan lekowa duk dama bata ji me suka ce ba tasan kawai nata ya kare ne yau wani sabon kukan ta fashe da shi har da daura hannun akai bai ko kula ta ba ya ja motar suka bar wajen.... Madam bola da sauri ta shigo resatuarnt tare da kwalla ma wani dan ta kira ta gaya masa ta kuma ba shi card din mj ya karanta mata da kyau cos ko a mafarki bata tabajin zata hadu da wani makamncin wannnan ba ma bare tayi magana da shi face to face... abun ya ba ta mamaki sosai badon yau ba zuby ba.. taso tayi kyakkywan bincike taji meye hadin wannan hamshakin captain din da suhan. A cikin motar tafiya kawai yake amma sam hankalin sa baya jikin sa wani bin sai yayi blaming kansa ma duk abunda ya faru "amma wani zuciyan yace masa koma yaya ne laifin ta ya fi yawa auren ka ne fa a kanta? Why must she go out of the house ba tare da sannun ka... ba what if wani abun ne yaje same ta yau a hannun mutumin nan.. Zuciyan sa na masa zafi yace" wato aure dake tsakani na da ita a banza ta dauke sa kenan wai wannan wani irin rashin sanin darajar aure ne har ace mata
Chapter 113 · 0% Book details