Sashe 112
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Page 43-44* Washe gari da safe suhan ta tashi Da shike jikin ta ya dan bata captain ba adai dai yake ba kamar yana fushi. cos daga yanayin yadda ya mata magana tun jiya sai ta sha jinin jikin ta gashi dama tasan bata da gaskiya. So da safiyar Allah ta tashi tayi normal duties dinta a tsanake ..duk ma bai tashi ba amma sai ta dan kimtsa masa dakin sa lokacin yana kwance ne kamar yana bacci Har ta gama ta fita Bai motsa ba kuma bai fita ba tana ta na kan jira ga lokaci ya tafi ta kira su anty jamila kuma shiru baya tafiya bare tasan ya ake ciki da jikin ummahn ta. Wajen 10 dai dai taga bazata iya hakura ya tashi ba kawai tayi serving dinsa abincin sa takai masa... Alokacin kam bacci ne na gaskiya ta dan dauke sa don bai ma san da shigowar tan ba ta ajiye a kan table .tana fita ta sabi hijabin ta ta kama hanya... Asibiti ta soma shiga cikin sauri amma dai dai bakin ward suka hadu da su ummah.. Tace anty ya dai..ya jikin ummah?ena zakuje kuma... ya naga kun fito? A sanyaye anty jamila tace da sauki suhan" ummah ta dan dago da kyar tace "gida zamuje kawai sunce kudin mu ya kare ga kuma magani nan da suka rubuta enaga kwara muje gida sai muyi na magananin if not da wanne zamu ji ? Suhan tayi ajiyan zuciya in dismay" tace to bakomai ummah..amma dai da dan sauki ko? Ummah tace eh ba laifi muje jamila ke kuma sai kije aiki tace toh umnah sai nazo.... tare da antyn suka dan taya ummah takawa har suka tafi bakin hanya ita kuma ta kama hanyar wajen aiki Kwata kwata hankalin ta baya jikin ta" amma sai ta yi kokarin kwantar ma kanta hankali cewa ummah zata samu sauki... Da safiyar Allah zarah ta tafi singapore basu ko hadu da captain ba..shikam yana kan bacci tafiyar suhan da kusan minti 15 ya tashi . A gurguje ya kimtsa ya fito... dakin ta ya fara dubawa bai ganta ba ko tsaya tambaya bai yi ba ya fito ya dauko mota ya fice daga haraban gidan .. Yana tuki yana dube dube har Sai da ya dan samu nitsuwa aransa sannnan ya kunna tracker daga wayar sa nan ya soma tracing location dinta.. Anguwar da ya nuna masa yakama hanyar zuwa.. Lokacin suhan isowar ta kenan itama keke napep ya ajiye ta suna kan neman canji a bakin titi Suna Cikin haka wata shaqiqiyar prado baka kirin wanda taji tintect ta dan dosu su ..gashi ba aganin kowa aciki so bata ma kula ba mutumin da ke aciki da boys dinsa guda biyu" yayi mugayen dariya tare da cewa ince dai kun kalle wannan yarinyar da kyau?..duka suka maida hankali kan suhan as there were coming closer. Nan suka kare mata kallo da kyau sannan suka ce mun gane ta ogah..yace good to muje gaba chan ku ajiye ni sai na shirya muku yadda zaku min da ita.. Ba musu suka isa gaba ..sauka mutumin yayi bayan sun gama zancen su wani mota na daban ne ya zo ya dauke sa ya bar wajen Wannan pradon ne ta dawo kofar restaurant Daya daga cikin boys din ne ya shiga ya ce ena mai wannan shago . Madam bola tuni ta hallaaro musamman data ga damshim kudi tattare da su...oder yayo na abincin kala kala wanda suka fi kowanne tsada awajen leda shida aka cika na take away madam bola sai kai kawo take tana nasa fadanci "sannan yayi nuni da suhan yace ita yake so ta biyosa da shi mota ..madam bola tace ai ba komai tuni ta je ta jawo suhan ta ce oyah dauka ki kai ma custoner wannan gasu chan ga motar su a bakin kofa tanayi rana dan tura ta sabida ta hanzar ta ...suhan ta danja da baya ta daure fuska cos hakan bai daya daga cikin aikin ta akwai masu aike aike ita nata dai dafawa ne da serving ..amma haka madam bola taki firrrr tace sam sai ta kai abinci koda tayi yinkurin daukan hijabi ma stil saita hanata a haka suhan ta kai har waje daga ita sai wannan uniform din da ledojin oders a hannun ta Tana fita motar captain na parking daf da wajen dama shikam baisan da nan din ba...shidai ta baya kawai ya ganta sai ya soma tuna ranar da suka soma haduwa da kayan jikin ta ne na yanzun Tana kaiwa bakin car din ta dan knocking sai aka bude seat din baya tana ajiye ledoji na farko ta dago na biyu kenan suka fetsa mata wani magani tuni ta tafi unconsious ta sake jiki zata kai kasa damka daya gayen ya yi mata ya sureta cikin motar kamar kiftawar ido komai ya faru so im no minutes suka bar wajan.. Duk wannann a idon captain ya faru its seems like shikadai ya bada hankalin sa sosai akan abun da ke gudana a motar...a gurguje ya kama hanyar yana binsu tsala tsala har yaga hanyar da suka bi.. bai damu sosai ba cos har yanzu tracker daya sa mata a suman ta na reading suhan na kwance galala a bayan motar tafiya kusan mint 40 ya kai su wani anguwa sabon anguwa ne cos most of the building are under construction Don haka wajen shiru ne ba motsi kuwa.. Captain na daga bayan su har yayi coping number bayan motar" sun ganshi kam tabbas amma basu damu ba cos motan captain bai musu kama da irin na mutanen da zasu kawo wani abu aransu ba..don haka hankali kwance suka shige wani fankacecen gida mai brown gate dogo.... kallo daya zaka mata kasan sabuwa ce.. Captain sai yayi gaba kadan ya tsaya zuciyan sa sam ta kasa nitsuwa gaba daya sai kamannin sa yana neman zancawa ya rasa me guda daya zai kawo a ransa game da al'amarin...very confused haka yake zaune cikin motar sa yana jiran ya ga shigar su gidan kafin yasan yadda zaiyi shima ya shiga... a ranshi ya riga ya sani koma meye ne ke faruwa suhan bata hannu mai kyau kuma tana bukatan taimako" but who are they? kidnappers ne koko wani business din banza takeyi? Kasa yayi da kansa da sauri ya sunkuyar da kai kadan ayayin da daya daga cikin su biyu yake jan gate din yana leke leke alaman gidan ma ba mai gadi.. Captain Ya dan danna wani abun kadan daga gefe ya dauko pistol yayi loading bullet ya ajiye a gefe... wayar sa ya dauka ya tura sako ma securities Kafin Ya sauko daga motar ya taho bakin gate din gidan Ya leka ta buli Bai ga kowa ba sai motan su..alaman sun shige ciki da ita. Har yanzu suhan bata farka ba don haka a hannu suka shigo da ita har gaban mutumin suka dire ta.. shikuwa ganin ta a haka ya sa shi sake wani kayataccen dariya. Yace aiki yayi kyau..cikin zumudi yace "yanzu kuje sai nagama zan kira ku. Ba musu suka fito shikan sa majeed baiyi aune ba ganin su yayi sun sake fitowa don haka ya koma gefe ya labe yana lura da kyau har ya tabbata fita za suyi daga chan jikin 3rd pillar ya rabe ya danna alert ma security alert ya sanar da su motar da ya turo musu number zata hau kan hanya ... as usual dayan ne ya bude gate din daya kuma ya fito da motar basu damu suyi wani dogon dube dube ba suka rufe suka bar arean wajen Captain Bai sha wahalan shiga ba duk da yanayin structure gate din gidan cire takalman sa yayi climbing har ya kamo daya daga cikin design din da dabara irin na su na trained armed forces yayi scaling ya sauko cikin compound din succesfully ba tare da wani motsi ba. Ko ajikin sa yake tafiya ya dada gyara zaman gun dinsa..duk sun sake ba wanda zai shigo so basu kulle ko ena ta ciki ba.. aciki kuma Lokacin mutumin gaba daya ya gama sullebe kayan sa ya rage daga shi sai gajeren wando yana faman fade fade shika dai. Ya zo daff da ita ya shafo fuskan ta " yace suhanna baby yau kam ba guduwa kinzo hannu na ...yayi hahahaha da karfi kamar mahaukaci.. Kallo yake bin ta dashi yana lashe baki ya sa da yatsan sa akan lips dinta charap sai ta bude ido..a firgice ta mike ganin alhaji sani ya sa ta shiga rudani da rikicewa batare da ta damu da azaban sarawa da ciwo da kanta yake mata ba ta yi yunkurin tsala ihu... tuni ya sa hannu ya toshe mata baki da iya karfin sa.. Wani irin firgici take yi lokaci guda ta samu ta fizge kanta ta gantsara masa cizo a hannun sa tayi gudu ta koma dayan bangaren gado" kuka ta fashe da shi mai razani tace ' meyasa ka kawo ni nan alaji ka nada hankali kuwa? Cikin fusata da son ya dada firgita ta "yace hahaha har ni zakiyi ma wannan tambayar? Ai kinyi kuskuren taba ni... kudi na nazo fansa wanda kuka ci da ke da kawar kuka gudu Kin dauka kunsha ko? Dai dai nan captain ya so majin magana don alokacin yana dai dai bakin door din da suke ciki Toh babu wanda zai cece ki anan alaji ya zaro ido yana fada" Idan nagama fansar kudi na ita kuma kawar naki sai na koya mata hankali don ba barin ku zanyi ba... Suhan ta tsorata sosai a lokacin don bata ma san ena take ba bare ta kawo wani dabara" yanzu babban tashin hankalin ta in har wani abu ya same ta anan me zatace da ummah bare kuma mijin ta.. Kuka ta fashe da shi ta rusina kan gwiwar ta ..alaji dan Allah kayi hakuri nasan mun yi maka karya amma wallhy bada san raina bane..dan Allah kar kamin wani abu ni ban taba iskanci ba..zan biyaka kudin ka Ya fashe da dariya