Sashe 129
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *ena alfahari da ku sosai duka kun mini kyautar littafi masu dadi masu ma'aana lokaci guda and yet always looking after me my besty Azeeyan and my sweety Hernyluv jazakahllu khairan alheri ke gaba da bayan ku this page is oll urs* _Elle o fans i dey sory Ku dai yi hakurin dai kawai ba magana..nagode *Page 51-52* Suhan ko juyi ba tayi ba don kuwa saida ta fito take jin wani irin tashin hankali na musamman Allah Allah take tagan ta gaban ummahn ta... so bata ko lura da motar mijin ta a baya ba. Shikam yana tukin sa calmly... Ranshi ba dadi kam amma hankalin sa bai wani tashi kamar yadda yake masa a da chan ba .. Dan achaba ya sauke ta kudin ta dauko ta mika masa a gurguje ta shige cikin gida.. Yana kallon ta shima sai yayi yunkurin parking cikin mamaki yace nan kuma ena ne haka? Me suhan za tayi anan...ya tabe baki Isowar su ummah kenan daga asibiti ko minti 10 ba suyi ba..ga nan anty jamila akan tabarma ta riko ummah sai rusa kuka take yi tana cewa" anty dan Allah kar ki tafi ki barmu..gaba daya jini ya fetsu jikin su baki daya sakamakon mummuman yunkurin tarin jini da take yi... A daskare suhan ta tsaya bata ko motsi saboda a halin da ake ciki sukan su basu ga shigowar ta ba.... Wani dogon numfashin ummah ta sake a wahale ta ce" jamila har yanzu suhan bata zo ba..bana so na mutu banga yata ba ta karashe da wani tarin jini.... wani birkitaccen ihu suhan ta tsala ta rugu aguje gaban ummah " ta kamo ta tare da fashewa da kuka...ummah meya same ki haka? ..ummah..ummah ta dan girgiza ta..ummah ko jin muryan suhan ya sa ta dago da kyau cikin dauriya ta zauna Duk sun birkice da yanayin suhan din anty jamila ne kawai ta iya kamo ta suka mike tsaye tana dafe da kafadun ta ...cikin jimamai tace" ena kika shiga suhan jikin anty ya yi tsanani meyasa kika kashe wayar ki gaba daya... a rude take sai ta soma gaya ma anty jamila abunda ya faru tsakanin ta da captain akan maganan satar fita restaurant data keyi don ta samu kudin jinyar "tace tun ranar daya gane ya hanani sake fita a gidan shiyasa baku ganni ba gashi ya karbe waya na..anty muje asibiti dan Allah bana so ummah na ta mutu ta barni.. Jin anty jamila tayi shiruu yasa ta gane tayi baran bara ma gaban ummah sai ta kama bakin ta tayi tsuru tsuru tana kuka a hankali captain baiji duk wannan ba don anguwar babu space da kyar ya samu ya tsomare motar sa so yana sa kan sa cikin gida ya shiga dube dube aganin sa har mutane suna rayuwa anan??... kuka kuka ya soma ji sai ya kara azama musamman da ya dago muryan mutumiyar sa ce... A lokacin ummah ta na kokarin dagowa da kanta duk da ma tana cikin azaban radadin ciwo ...baki na bari tace suhan? Kika ce mena? Suhan dama tun tuni karya kika min kina fita bada izinin mijin ki ba?.. wani irin garas majeed yaji saukar maganan a kunnen sa sai ya dakata daga inda yake wanda baifi taku uku ya iske su ba' Jikin suhan ya hau karkarwa batace komai ba wani azama ne ya taso ma ummah kallo daya zaka mata ga gane shes highly dissapointed ranta yayi mugun baci...tas ta mike zaune kamar bata jin zafin ciwon Baki na bari suhan tace ummah..umm..ah ki tsaya kiji...cikin tsawa ummah tace bana so naji komai rike karyan ki Ashe bakida hankali suhan duk maganan da nake miki ashe a banza nake ? Da haka zaki rike rayuwar ki a duniyan nan..kikace min mijin ki yasan da aikin da kike duk gidan ku ansani ashe yaudara ta kike yi kina min karya? Cikin wani rudadden kuka tace ummah ai baki da lpya ne kuma....ta tsare ta da cewa toh kuma sai me ?anji ban da lpya akan hakan ne zai sa ki taka dokar ubangiji kina fita bada izinin mijin ki ba sannnan kiyi min karya suhan? Innalihhi wa enna ilahi rajiun "amma bansan ki da wannan halin ba . ummah ta fashe da kuka mai dauke da tashin hankali ta cigaba da fada tana cewa " "Meyasa zakiyi wasa da darajan auren ki wai don kina so na samu lpya wayace miki hakan da kikayi dai dai ne? Anty jamila ta rusuna kasa cikin jimami tace anty dan Allah ki yi hakuri ki fahimce ta ....kiyi hakuri ki saurare ta dan Allah ...tace kiyi min shiru jamila ai har dake ma aciki wallhy kun bani kunya ...dake wato take hada kai tana min karya tana taka dokokin ubangijin ta ko? To me kukayi kenan? wai a hakan ne da kukeyi Allah zai cika muku burin ku har na same lpya? Ai shi Allah ba azzalumin ba wansa bane ku ba kusan hakkin da nidin nan nake da shi akan ki ba komai bane in aka hada da wanda mijin ki ke dashi? Ina ilimin naki yake suhan... Toh maza ki koma gidan ki yanzun nan bana son na sake ganin ki anan sha shasha kawai.....maza fita min a gida ta karashe a tsawace... Tace "duk randa kika san kare darajar auren ki zaki zo ki same ni anan in ena raye oho in na mutu ma oho..ciwo da lpya na Allah ne in yaga dama ya dauke ni in yaga dama zai barni amma bazan taba lamun ta karya da yaudara ba ..ki fita min nace...ta karashe da wani mummunan tari Dukan su kuka suke yi musamman suhan data daura hannu akai tana neman birkicewa.... ganin tarin ummah ya soma tsanan tawa yasa ta karaso daf da gudu zata tallafo ta cikin kuka ummah ta bankade hannun ta gefe cikin fushi ....duk dama yanzu kam ta kasa magana tsaban tari amma sam taki bari suhan ta kara taba ta .... kuka suhan keyi tace ummah dan Allah kiyi hakuri bana kara wa nayi kuskure ummah kar kiyi fushi da ni...ummah.. ta shiga kiran ta tana bubbuga kafar ta a kasa.. Cpt majeed yana jin duk abunda ke faruwa mamaki ne gaba daya ya rufe sa so dama asalin kan magananar kenan? Wani karamar zufa ke keto masa cikin rudani yace lallai ma yarinyar nan me nayi mata haka? ...ummah ta na dada gurfana kan kafanta cikin radadi aman ya soma fita ta rike kirjin ta...ga shi sam ta hana suhan zuwa kusa da ita bare ta taba ta...anty jamila ta rude ta ce suhan ki tafi mana dan Allah ki tafi ni zan kula da ita ran anty ya baci ne kije mana ...suhan ta shiga girgiza kai alaman bazata ta iya tafiya ba gaba daya sai ta kasa magana kuka kawai ta ke yi tana cewa" ummah ..ummah dan Allah... Ummah ta dago da kyar ta kalle ta wani irin numfashi ta sauke mai nauyi tare da bude baki za tayi magana maimakon hakan sai ta fetso jini tare da kafewa tana neman fara convulcing .. captain na jin komai hankalin sa yayi mugun tashi he cant take it anymore kawai sai ya karaso ciki ..shigowar suhan ta sa ihu a birkice zata je kan ummah bazata taji ya finciko ta gefe ya mayar da ita baya da azaman sa ya karasa gaban ummahn ..dukan su wajen basu taba ganin sa a sarari ba sai suhan ga umma na daf da fita da hankalin ta baki daya saboda bata ko numfashi mai ma'ana.. Ya tsuguna gaban ummah cikin tausayi da sanyin jiki a guje ta karaso cikin bori da masifa tace ni kar ka taba min mama na....ka kyale min mama na duk kai ka jawo min a rude take jan rigar sa tana fada....tun daga nan anty jamila ta dago cewa shine mijin suhan wato capt majeed.. shikam baice komai ba don sai da yaga ummahm ido da ido hankalin sa ya mugun tashi kirjin sa har dokan tara tara yake ....tana jan sa bai kula ba ya danna emergency call ya kira asibiti basu ko lura ba.. lokacin suhan na kan maida masa borin ta da masifa Abun ya ishe Anty jamila Sai ta kamo ta tayi gefe guda da ita tana mata fada....uffan baice ba ya tsuguna ya tallafo ummah yana gyara mata zaman ta ..kan kace wani 5 minutes ummah ta suma hancin ta ke fitar da jini sai ya rasa meke masa dadi ji yayi bazai iya tashi agaban ta ba but he cant wait to see the arrival of ambulance... Suhan na daki anty jamila ta nitsar da ita Suna isowa anty ta fito ta tallafa masa aka sa ummah a emargency ambulance na babban asibitin garin.. suhan ta biyo su waje lokacin an gama sa ummah a mota...yace ma anty jamila kar ta damu shi zai kula da ita ta zauna da suhan..yace doctors suna bukatar nitsuwa inda wani abu zai neme su... Ita ta fahimce sa amma sam suhan ta dire tace ita wallahy sai ta bi umman ta ..nan ta je ta tsare a bakin car dinsa tayi banga banga ga hawaye nan sun wanke fuskan ta wasu nakan bulbulowa ... anty jamila zata yi magana yace mata no ki barta kawai its ok... Zan tafi da ita...kaiwa nan ya jawo ta da karfi ya dura ta a mota ya rufe ya bi bayan ambulance suka bar wajen... Tam ya daure fuska yana tuki ko ajikin ta don yanzu gaba daya laifin sa kawai take gani.a tunanin ta duk a kanshi take shan wahala da chan ai ba haka rayauwar ta yake ba gashi yanzu yasa ummahn ta ta yi fushi da ita...Allah Allah take jira yace zai mata wani maganan ta fita A gidan sa yau bata tambaye sa ba tayi masa deban albarka amma shiru bai tanka ba..da shike ma ya lura masifa ke dawainiya da ita sai ya share ta tana famar kukan ta abun na cinta arai... Suna kaiwa asibiti ko kallon ta