← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 225

Sashe 11

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Page 9-10* Rawan dari suhan take kamar wacce ta fito yankin kasar eskimo musamman yadda taga zaratan maza sun zagaye ta da guns a hannun su. Daf da ita cpt MJ ya dakata tana duban ta da idon sa mai tsoratar wa,she can't take the horror sai ta lumshe ido cikin firgice bakin ta ya soma rawa gashi tana so tayi magana amma ta kasa motsa baki tsaban yadda cikin ta ke bada sautin kuuuuuu yana gululu kamar mai shirin zawo ta tsaya chak bata motsi ....baice komai ya juya gameda streching his hands dinsa ma security nan aka mika masa bindiga Ba wani bata lokaci fuskan sa a shake ya daga gun din a Kanta ya daura,.."start talking now meya kawo ki nan? a tsawace yafada sai da ta girgiza ... bai bari ta dawo dai dai ba ma ya kuma cewa How did u get in here wato Ke barauniya ce ko? Ta fashe da kuka ""Noo.o..o..o no...no oga.. sir...,kayi hakuri dan Allah..hawaye nakan bulbula kan fuskanta still shaking involuntarily, Cikin kallon mamaki ya danna mata harara" In yi hakuri fa ki kace?ohh my god..Get on ur knees,ya sake daka mata tsawa ...ke wacece? Bata amsa ba Tayi saurin zubewa kasa tayi kneeling tsaban tsoro Don Tamkar a military squad haka suhan ke jin kanta... muryan sa kawai wani torture ne bare kuma yanayin sa , 'kayi hakuri dan Allah Na...y.i k..us..kure na shiga maka bo..o..th ni wallhy ba barauniya bace ..Kayi hakuriii...kaji oga,sir dan Allah ,dan Allah ...wallhy ban karawa, Ta dukar da kai kasa still sobbing heavily " Jin yayi mata shiru ya sa ta sake cewa "Im sor...ry ta dada fada cikin magiya tare da kukan tsoro 'Sai ya sauke gun din a nitse yace"Toh What tok u to my booth in ke ba barauniya bace?kina min karya ko,taya akayi kika bude min mota..did u even know me..kin taba gani na? Yafada dagan gan kamar bai tuna ta ba ma Tayi saurin girgiza kai alaman a'ah, sai dai baisan hakan amsar na meye bane guda daya Cikin e'e na tafara" Uhmmm, uhmm.mmm dama a hotel din nan ne.. Ta budi baki da zimman Tana so tayi masa bayanin komai ya dakatar da ita.. "Ohhh just hold it there ..hotel? kece dazun kika buge ni kamar kin buge sa'ar ki and then now you reluctantly get into my closed booth ba tare da sani na ba? Tace..A.ah ,pls ogar sir ka tsaya kaji .. "Just shut up ,ya dakatar da ita cikin fada "u dont talk when am talking i can see gidan ku ba akoya miki respect ba ko Nan ma ta girgiza kai.. Yace" stupid gal toh nizan kowa miki" oyah kama bakin ki nace. Tuni cikin daburce ta kame bakin ta hannu bibbiyu a gaggauce Ta gyada kai cikin sauri sauri tana binsa da ido still sobbing heavily kar na sake jin kinyi magana sai nace kiyi Tayi nodding gwanar tausayi Sai ya juya abun sa Salehhh... ya kwala kira da coarse voice dinsa kakkaura sai da ta karkace da kneeling dinta don tsoro Kawo min dushan,yace ya koma baya ya tsya abunsa aka bar suhan a tsakiyan fili Sai kiiiiyytt taga ana janye wani katon cage ,zumbut ta mike tsaye taja da baya nunfashin ta na neman daukewa, Tuni ta sake baki idon ta suka fito waje"Na shiga uku ta daura hannu akai tana fada cikin kuka. Police dog ne kosasahhe sai jan shi ake a chain har gaban Cpat MJ. Hannu yasa yana shafa shi ,in a familiair gesture sannan ya masa izinin zuwa kan suhan. Dushan na tafiya setin suhan""Zangani ko ke wacece da kai na ya fada aransa,i think wannan barauniya ce ya fada ma guard da ke tsaye wajen still in maximun raspect. Suhan ta soma ja da baya tana kuka mai sauti hankalin ta ya tashi,a ranta gaba daya she cursed that night, ta rasa meya kawo ta kusa ma da motar sa , Dushan kuwa Harshen sa ja yake fitarwa kamar wani kura yana tahowa idonsa still akanta jiki na rawa tuni takalmin ta ya cire kafa daya.. Da baya take komawa tana kuka tana kallon karen.. Sai Yayi wani mika yana buzur buzur da gashin cikin sa,suhan a guje ta balle da gudu tana zaga fadin wajen tare da tsala ihu duk wajen suna shiru suna kallonta musamman capt da ya harde hannu yana wondering how could such a beautiful girl like this be going after old men,isit for money ko rashin godiyan Allah? He just cnt stop to think don abun na matukar bashi haushi da takaici,shiyasa bayi ko jin abunda yake yi mata a matsayin hukunci yanzu ba dai dai bane after ol ita ta biyoshi. Ihun suhan ke dada ruda Dushan don yazo dap sai ya kama side din trouzer ta yana ja yana gurnani numfashin ta har na sarkafewa suhan sumewa ne kawai ya rage mata don hawayen ta da zufa a fuskanta baza a iya banbance su ba ta cike shataf Da kyar Ta hankade sa gefe da karfi tayi bakin swimming pool da gudu dushan bai hakura ba don yana daka tsalle zai sake chakumota ta fada cikin ruwan swimmimg pool Wanda yayi dai dai da fitowar mum hankali tashe, Guards ,guards, who is here? Take fada as she was coming out fully daga cikin gida tana so taji a ina ne taji sautin ihu da kukan yarinya Dushan ... cpt ya fada sofly yana tapping hannun sa dushan tuni ya juya a ladabce ya dawo wajen sa yana shafa sa a hankali kamar ba abunda ya faru . mum kuwa suhan ta soma hangawo tsakiyan pool ta kankame jikin ta tana shessheka a razane ta bi ta sunkuyar da kai tana kuka mai dauke da silent tears, ga shi duk tagama jikewa shatafff cikin ruwan sai faman kakkare boobs dinta take gwanin tausayi. Hankalin mum ya tashi ganin ta tayi saurin isa bakin pool tana cewa Who..who..ishe? Ta kalli cpt mj da sauran guards a gaggauce, cikin su ba wanda ya iya tankawa mum sounding so Pitiful ta ce ,"come on my dear zo nan na taimake ki, mum ta mika mata hannu sigar rarrashi Suhan na tsaye cikin ruwan sai sheshheka take zuciyan ta fam da tsoro cos she can't wait to live this living hell of a place..kukan da take yi da yana damun mum saita shiga halin tausayin ta sosai Hannu ta dada mika ma suhan "" "Stop it mum, mj ya fada yana tare hannun mum dinsa gefe. 'Get away, ta ture sa gefe ta kamo suhan dake kan matsowa ko ena na sirrin jikin ta na nunawa sai ta dada rakubewa tana rawan sanyi Bayan ta fito Mum ta riko ta tana cewa" wai meya faru ne majeed mai aka mata? Shikam Yana shiru abunsa..nace Why the dog and the guards lpya kuwa,? Still nan ma Bai amsa ba yana binsu duka da kallo Musamman suhan da ke sum sum gwanin tausayi agefen mu Yana feeling pity kama Amma sam sai ya hana kansa tausaya matan cos shi baiga abun tausayi wajen wacce ke bin maza hotel ba. Cikin gida suka nufa Zauna tare da mum nan ta ce ma suhan dake kan buga kauyancin ta a dabaran ce wajen kallon kayan duniya shigo mana ta shigo fuskan ta still dauke da hawaye Mum na lura sai ta sake maimaitawa ki shigo ki zauna mana.. ....,a'ah madam ena so naje gida ne madam dan Allah kuyi hakuri...ta karashe murya a dishe cikin wani sabon kuka. 'Huhhhh ,i know.. ki zauna toh in kinaso na barki ki tafi gida Ba musu suhan ta zauna a babban palourn su gefe da mum. Shikam ko kulawa baiyi ba ya juya massallaci don gabatar da magrub da isha'i Meya faru?mum ta maida mata tambaya Daga ina kika zo nan, 'Uhmmm mmmm dama Na buge sa ne achan wajen cos she cudnt say a hotel anymore ,sai kuma mistakely na shige masa booth ban tanvaye sa ba... duk laifi nane kuyi hakuri dan Allah ku bar ni na tafi gida Ni ban taba sata ba i just wanted to go home,sobbing profusely ta karashe maganan nata.. Dan kada kai mum tayi cikin tausayi ta shiga rarrashin suhan, tace meye sunan ki Tana faman tsare hawaye tace "sunana Suhan , ok anan garin kike zama i gues , Tace Yes mah. Dan shiruuu mum tayi daga baya tace Tom give me your adress ok? Yanzu kinga ba lokacin da zamuyi magana cos ure already terrified ..amma ena fatan zaki yi hakuri ko ?a ladabce suhan ta gyada kai "kema next time dont come close to strangers bare kuma motar su is that ok? Ta rusuna kasa a ladabce tace yes madam thank you ma, Mum tace "Bakomai ah will get u some cloths sai ki sauya a kaiki gida magana suhan zatayi abari kawai amma tuni mum tayi magana da mai aiki aka je kawo ma suhan kayan sawa , Duk dama a firgice take She cant stop to look gaskiya gidan ko a film bata taba ganin irin sa ba Amma she really wanted to go ,tsoron sake hada ido take da cpt MJ again. Come with me ,taji ance mum ta mata permiting smiles nan ma sai kalle kalle take har tana bumps Nan jerin dakunan dake kasa a daya daga ciki aka bata simple arabian gown baki kirin da mayafi sai flat shoes na vinci mai kyau shima baki Minti 10 ta sasu ta fito sum sum da jikakun uniforms dinta a hannu cikin wata yar leda Mum was actually looking at her simplicity in perfect admiration, cikin ranta tace "i have to know this girl haka kawai nake jin wani abu daban game da ita daga gani yar gidan tarbiya ce so innocent and down to earth.. "Nagode madam Allah ya saka miki da Alkahiri suhan ta fada rusune gaban mum, Mum tayi smiles "No my dear bakomai, muje akaiki ki gida ko. tayi saurin gyada kai ta mike tsaye Mum na gaba tana biye har waje
Chapter 11 · 0% Book details