← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 225

Sashe 114

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

tana fita aikin dafe dafe a cikin gida na ba tare da sannu na ba?ya tabe baki "hmm lallai an ma Raina min wayo.... cikin ransa yake maganan yana girgiza kai don bakin takaici da haushi da abun ya ishe sa ya buga kan stairing sa da karfi saida ta yanke kukan don razana a haukace yayi wani wawan parking a gefen hanya .. ... Baice komai ba ya fito ya bude kofar baya ya sa hannu ya fin ciko ta sukayo waje tare.....a kasa ya jefa ta ya kama hanya a fusace zai bar wajen.. Ihu ta tsala tana bin bayan motar tana cewa ""dan Allah kayi hakuri..nayi kuskure kayi hakuri pls. ..Sir..ka saurare ni.... Kamar zata shide haka takame jikin ta tana binsa shiko ya hau dokin zuciya .....tana gani yana tafiya ta zube kasa ta shiga ihu sosai cikin firgici tana cewa yayi hakuri....bazata sake ba Tuni ya bar area wajen da shike ma ba jama'a sosai Hanyar wani estate ne so Ko nisa baiyi ba ya da kata ya kashe motar ya tsaye tare da kife kansa da stairiing" yana maida numfashi For the first time yake jin wani irin yanayi a rayuwan sa yasan tayi masa laifi amma tausayin ta na mugun kashe masa gwiwa gaba daya ya kasa gane kansa Wani zuciyan tace masa ai in ita yarinya ce ma yau kun zama daya tunda ka barta anan kayi tafiyar ka batare da ka nuna mata laifin ta ba"toh ta ya za'ayi ka kawo gyara? ..maganan yake lailawa a ransa daga bisani kawai ya juya kan mota ya koma inda take Har yanzu tana kasa gwanin tausayi ta kame waje daya tana kuka a hankali.. ganin sa ya sata mike a guje tayo kansa . A sanyaye ta ta zube kan gwiwar ta a gaban sa " tsaban kuka n data ci da kyar kalman hakuri ke fita daga bakin ta.. Shirun da yayi nata yasa ta dada tuma Ta fashe da wani kukan mai ban tausayi ta kamo kafar sa dam "tace kayi hakuri walhy bana kara fita ban gaya maka ba dan Allah kayi..ha ku..ri. sai ya lumshe idon sa don ya samu karfin gwiwa...daga nan ya dago ta yana rike da ita hannu bibbiyu ya narka mata furiouss eyes dinsa anata baice komai ba.. ganin yanayin sa sai ta dada firgicewa tace"dan A..lla...h kayi ha..kk.kuri na tuba bazan ka...r..ra ba. Ya dube ta cikin wani rin yanayi da zai biya Fahimtar dakai yana cikin tashin hankali a zuciyan sa ya dan ja tsaki" tare da zame hannun sa " Kamar dama hakurin zaiyi amma ya fasa.tuni ta juyo a haukace zata sake taba sa anan ne ya juya ya daura mata wani firgitaccen mari sai da ta dauke ji dummmm kunnen ta yake bada kara.. Cikin tsawa Yace kar na sake jin kin ce nayi hakuri anan for what? Hakurin me zaki bani bayan bakisan darajar kanki ba bare abunda ke rataye a wuyan ki na hakkin wasu" Ya shako ta a fusace yace "So U worked in a restaurant kin taba gaya mun haka? Tayi saurin girgiza kai cikin tsoro..ya dada cewa And u went ahead to be going out of my house witout my permission zaman kanki ki keyi ko? Ta shiga bulbulan hawaye daya na bin daya gwanin tausayi..."toh Kiga abunda ya so ya faru dake yau ...anan muryan sa har yana rawa yace wannan adalci ki kayi mana kenan ko? Wai kin taba tunanin nauyin dake kanki kuwa kin ma kawo tunanin wacce ta kawo ki zaman aure da ni ..me za kice mata suhan answer me ?"Tayi saurin sunkuyar da kai tana kan hawaye.. Yace aje ni baki dauke ni mijin ki ba and i cant blame you don bani na kawo ki zaman aure dani ba..toh what about my mum ? Baki damu da ita bako..Kin taba kawo tunanin yadda zataji yau in da wani abu ya same ki kuma taji ke dakan ki kike shiryawa baki sanar da kowa ba? I tot kina iya gaya mata matsalar ki what did you need wanda baza ayi miki ba sai kin zo wani waje kina jawo mana masifa? Cikin kukan har bakin ta na rawa tace nayi kuskure kayi hakuri dan Allah Kallo kawai ya bita dashi yace" Look ni bazan ma iya zama dake ba ke makaryaciya ce mayaudariya..and u know what yau din nan zan sanar da ita wanda ta yarda dake halin ki na asali kinga daga nan sai ki samu abunda kike so dama ki samu awajena ki kara da gaba....a raunane ya fada idin sa har sun tara ruwa Masifa ya cigaba da hantsala mata kamar kamar zai sake watsa mata wani marin" Ita kam tun da ya kira sunan zai gaya ma mum ta rusuna kasa tana kuka ba tace masa uffan ba again...cikin ranta tace To ni ya zanyi?nasan In da na fada ma mum komai zata taimake ni amma ummah bazata karbi hakan ba sabida nasan zatace zai dawo min abun gori wata rana .. shi kuma ai bai taba bani matsayin mata agidan sa ba.... to meye laifi na don naje nema ma mahaifiya ta mafita?uhmm ai bazan bar ummah na ta mutu dan ena auren sa ba.. Nima dole ya zame min nima nayi aikin nan ba son raina ba ne kamar yadda nake zama da shi ba a son raina ba..... Wani zuciyan tace mata "ah ah dai suhan.. duk da hakan dai kinyi masa laifi mai girma. Kece fa matar sa ki tuna fa ko ayau kika mutu aljannar ki na karkashin kafan sa .so ko a wani matsayi ya ajiye ki dole ki bashi darajan sa na mijin ki...ure wrong. anan wasu zafafan hawayen takaici mai dunkule da rudani suka dada bulbulo mata..kaf ta dena jin masifan da yake saukewa akanta kamar zai buge tan...ita dai tasan yace zai sanar da mum abunda tayi kafin nan ya sake ta Ko da ya juya zai tafi bata iya cewa komai ba tsaban yanayin Data tsinci kanta aciki sai ta kasa ko tashi ta bi shi kuka kawai takeyi har ya sake jan motar sa ya tafi ya barta anan. *my dear wattpadians ban mance da kulawar ku ba am so grateful Allah ya bar kauna Keep voting "ummuafreen asmy pinky Ena miko gaisuwa...* *surriem* [9/17, 23:49] SURAYYAHMS: * BRILLIANT WRITERS ASSO
Chapter 114 · 0% Book details