← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 225

Sashe 133

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Page Tunda ta fita Sauri take kamar wacce zata tashi sama so tana isowa bakin asibitin ta kuma danna kira ma anty jamila... yayi ringing ba a dauka ba hankalin ta sai ya dada tashi gashi bata san ma ta ena zata shiga ba bare tayi tambaya.. don kuwa tunda aka haife ta bata taba shiga irin wannan asibitin ba. 15 misd cols still ba dauka ba ta yanke huknci kawai ta shige ciki ko ma yaya ne.. Cikin sa'a ta yi tambaya sai aka hada ta da receptioniost ann ma iya kwatance tayi amma ba wanda ya gane sabida ummah a excutive ward aka kwantar da ita bata sani ba.. ita kadai ce ana bata kulawa na musamman.. Chan ta gaji ta koma gefe...Dube dube take har idonnun ta sun kawo ruwa"suhan? Taji an fada da sauri ta juya....anty jamila ne ke tahowa sai doc da captain...ta bisu da kallo suna hada ido ta dan sauke kai kasa...ya tabe baki bai kula ba shikam ya cigaba da magana da doc har ta karaso a dame tace "anty ya jikin ummah? Pls Ki kaini na ganta ....wai da gaske sai an fitar da ita wani waje kafin ta bude ido? Anty ta dan jawo hannun ta batare da ta amsa ba suka shige dakin ummah sai da ta kare ma wajen kallo tamkar ba asibiti ba ...ta juyo ummah ne a kwance shiru kamar mai bacci... wani murmushi mai hade da hawaye ta sauke ta zo daf da ita ta zauna" ta kai minti 10 tana dan shafa gefen fuskan ta gwanin tausayi cikin sanyin murya ta shiga cewa ummah na kiyi hakuri nasan na bata miki rai wallhy bazan kara ba. ..ena son ki ummah bana son ki tafi ki barni kinji ummah na..? A hakali ta soma kuka Anty ta dan dafa ta cikin jimami tace insha Allahu zata warke suhan addua kawai zaki na mata kinji. tace "toh tana dan tare hawayen ta da suke kin tsayawa..cikin haka sai ga wasu nurses sun kai su uku instead of normal white uniform sai aka hada musu da wani jacket mai kyau sky blue alaman da su za'aje... A ladabce nurse tace madam ..zamu shirya ta pls excuse us ..ba musu suka ja gefe...suna kallo nurse suka dago ummah aka sauya mata kaya zuwa normal gown na asibiti dark green ba bata lokaci suka hada duk wani abunda doctors din emergency plane din ke bukata akan wheel bed suka soma yunkurin turo ummah waje... kuka suhan ta dada fashewa da shi nai razani wanda ya tsorata su duka anty tace..wai meye hakan ne kuma suhan? ta kamo ta tana mata fada a raunane.. ta shiga karkarawa tana cewa shikenan ummah na zata tafi ta barni anty dan Allah kice su bar min ummah na nikam ...cikin rudadaen kuka take fada.. Sosai hankalin anty ya tashi cos tasan suhan ta na tunanin kar atafi da ummah ne aje a dawo babu ita gashi kuma tana fushi da ita ..a hankali ta kamo ta cikin rarrashi tace haba suhan..addu'an da zakiyi mata kenan babu sai kuma kuka? Ki sa a ranki zata warke mana dan Allah ki dena kukan nan haka...sukam nurses suna shiru duk dama sun tausaya. ana fita da ummah waje ta biyo bayan su a sanyaye tana kuka kamar ance mata rabuwar su kenan na har abada.. anty ma na binta amma bata kuma ce mata komai ba sai da suka isa filin da za'a sa ummah a plane.. Majeed Tun daga fitowar sa da doc ya hango ta kukan kawai take tana tahowa har tana shessheka ...sai ya dawo ya same nurse din ya dada basu izinin su wuce da ummah da sauri kar su bata mai lokaci. tana ganin haka ta karaso a gaggauce zata bi su hannu daya ya sa ya kamo ta ya dawo da ita baya"a rude ta ce dan Allah kar ka raba ni da ummah na ena so na kula da ita ne...pls na roke ka ka kyale ni " ta cigaba da kukan a hankali... kallo ya bita da shi gaba daya tausayin ta yake ji shiyasa baice komi ba Anty jamila na gefe tana binsu da ido.. Sai ta kuma maimaita masa maganam nan ne yace wai waya ce zai raba ki da umman ki? ta cigaba da kuka yace toh kiyi shiru ki saurare ni ya dan jawo ta daf da shibcikin rarrrashi yace..kina son umman ki ko? Ta gyada kai a hankali yace toh meyasa baki so ta samu lpya baki san asibiti za' a kaita ba ke din yaushe kika iya aikin asibiti da zaki ce abar miki ita? tayi shiru chan tace toh zata warke kenan ko? Yace insha Allahu... u need to hope for that ba wai kina kuka ba.. tace to nima zan bisu na gani... yace no.ki zauna kinga wannan emergency ne ba space din daukar wani mutum..uhm? Ta dan kara fashewa da kuka batace komai ba..ya riko hannun ta by then an gama komai Ya juya da ita zuwa wajen anty jamila fuska ba yabo ba fallasa yace" ki zauna anan tare da antyn ki call me if u need anything ok? Ya juya zai tafi batare da ya jira amsar ta ba...kuka mai sauti ta dada fashewa da shi wanda ya sa shali kasa samun sukuni iita dai anty bata ce uffan ba don ta san abu kadan ke fitar da suhan hankalin ta. not so eva tasan yadda suhan ta sa ummahn ta arai sosai babu dama .. this time da ya juyo amma anty jamila yake kallo" yace dan Allah ki kula da ita babu lokaci.. tace ka tafi abun ka kar kadamu Allah dai ya tsare yace ameen ya kara da gaba.. Tare da shi suka bar kasan nigeria zuwa chan yamen.. Already doc carrene ya gama shirin sa don layin appointment wata 6 ke kansa na mutane masu bukatan irin wannan taimakon daga kasashe daban daban....but luckily enough kudi ba abunda bai iya sawa acikin kwana daya kacal ya amsa bukatan captain so tun kafin su iso aka shirya komai na jinyar ummah... Tun daga wajen anty ke rarrashin suhan da kyar tayi shiru..cikin kukan nata harda masifa tace..ai da sai ya barni naje shi ya zauna karya yayi min yace ba wajen da zan zauna nabi ummah na.." anty tace ai gwara ma da yayi miki karyan madallah... suhan ashe bazaki sa ma zuciyan ki ruwan sanyi ki nitsu ba..ko so kike kema ki kwanta rashin lpya? Tayi shiru ga fuskan gaba daya ya haura ...suna tare har ta dan samu tayi wanka sallah ta ci abinci Chan kusan dare hankalin ta ya kuma tashi tana so taji motsin su...ya ake ciki achan.. Anty ne ta fito daga daki kamar an tsakure ta tace anty ya kira ki ne? Ya jikin ummahn? Anty ta kalle ta ta girgiza kai tace ni ban sani ba ...suhan zan fa saba miki idan kika kuma daga min hankali da daddaren nan kin taba ganin yadda aka taba yin aiki lokaci guda ne?..toh nima jira nake ya kira ni tukun.. tayi shiru ta sauke kanta kasa.. Chan ta dago tace Allah ya sa ummah na ta warke..anty tace ameen kinga ma ya ya kamata muje ki tafi gidan ki dare kar ya miki anan.. cikin marairace wa tace haba anty kamar ya fa na tafi ?tace suhan kina gani ai muka rabu da mijin ki bai baki izinin zama a nan ba wallhy na ji kunyar abunda muka aikata gaskiya bana kuma saki aikata irin wannan kuskuren ki tashi kawai ki tafi gidan ki.in yaso inya kira sai ki nemi izinin sa ki dawo mu zauna anan din.. suhan baki a wangale take kallon Anty amma da shike taga seriousnes akan face dinta sai kawai ta sabi hijabin ta tace to ni na tafi... Har bakin hanya tayi mata rakiya tare da dan mata fada akan daga hankali data keyi suka rabu... Duk iya dauriya suhan tana yi amma da kyar sai da ta yi hawaye sosai kafin ta samu tayi bacci mai nauyi... Shikam yana chan yana shirye shiryen sa na zama jinyar ummah 3 days operation za'a mata.. Acikin Kwanaki ukun sau daya ya kira suhan ya sanar da ita meke faruwa a chan.. duk dama hankalin ta ya kwanta amma har yanzu tana jin ena ma ace tana chan tare da ummahn ta ana kula da ita tare.. Yau ne ranar da ake shirin ganin sakamakon aikin ummah hour biyu kacal ya rage daga lokacin da doc carrene ya bayar so yana gamawa ya koma germany ..duk abunda ummah take bukata na kula da sauran jinya ya gaya ma majeed da kansa don shi wani irin mutum ne da tsaban gwarewar sa yana da tabbacin cewa in har yayi aikin to yayi kyau in baiyi ba to kwana ne ya kare.. Bayan tafiyar doc Gaba daya majeed sai ya kasa zama shi kadai ne sai securities din sa daga waje. Haka kawai yake jin ummah a ransa saboda kullum acikin sa kansa a matsayin suhan yake in mum dinsa ne hakan ya zaiyi? It was 10.ooam dai dai nurse ta fito daga room din ta same shi" he dint talk amma sai ya mata kallon yana jin ta...tace masa u can come in now sir shes about to talk.. a hanzarce ya mike tare da sake wani irin murmushi bazata yace Alhamdullhi... Yana shiga ya same ta farfado kam amma bata bude ido ..a kujeran dake fuskan tar ta ya zauna gashi rest room din yaji kwalliyar flowers evrything is red and white sai sanyi mai dadi dake ratsa ko ena... ya zauna daf yana lura da motsin nata magana take amma ba ya jin me take cewa...hannun sa ya sa kadan ya taba canula tare da cewa sannu ummah ya jikin Ya kike ji yanzu?..shiru ne ya biyo baya daga bisani ta soma bude idanun ta a hankali minti 3 ta dauka tana kallon sa wanda ya sa shi dan sauke kai kasa don kunya...tace jiki na
Chapter 133 · 0% Book details