Sashe 217
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta roki alfarma ta cigaba kawai da basu kudin company nata da ba nata ba duk tana kwasa tana bayarwa. A ranar da za'ayi ma suhan wankan karshe na magani duka suna nan baba da ogah majeh. Fulani Jabbo "yace insha Allahu daga wannan ta samu waraka'sai dai abu daya ya rage shine jin muryan mijin ta daga nan in aka samu ta warke kenan har abada... sannan yanzu ajikin ta akwai kaikayi koma kan mashekiya daga yanzu duk wanda ya jefe ta zai koma kansa sannan ta dage da addu'oi da karatun qur'ani... Su kayi masa godiya baba "yace amma yanzu zata na amsa magana? Jabbo yace eh amma ba acikin hankalin ta sosai ba..amma tabbas yanzu babu wani shedani ajikin ta Kuyi dai kokari ku kaita inda zata samu mijin ta sannan haihuwarn ta zaizo bayan hakan ya faru... aka kammala ma suhan wanka na karshe amma sai ta suma.. Bata farka ba sai da su baba suka isa gida da kusan awa biyu... Yana waje suna tattaunawa da baba majeh .yanzu babu kudi babu abinci sukan su yunwa suke ji ga yamma yayi sosai ana neman karfe 6.30pm... Daga kan gado Ta soma motsawa tana dan girgiza kai kamar wata mai shirin tashi daga mummunan mafarki Da asalin muryan ta ta soma kiran sunan a hankali "tana cewa maje...eed.majeeed majeed.. "kamar an tsakure ta ta mike firgit tana haki ta dube kanta taga ko ena wani iri hannu ta sa ta toshe kunne ta cikim rudani ta fashe da kuka mai sauti wanda ya sa su baba shigowa a razane Yana ganin ta hakan sai Ya taho kan gadon cikin kulawa yace yata kin tashi ne? Ogah maje ma yace yaya jikin naki yanzu sai kuma tayi shiru ta bisu da ido hawaye na kan sauko mata... Tabbas akwai sauran waraka da ba tayi ba ido kawai take binsu da shi bakin ta yaki motsawa... ..majeed kawai kunnen ta ke son ji Zuciyan ta shi kadai yake ambata..tana so ta tsala ihun sunan sa amma ta kasa... "Haka su baba suka shiga rarrashi da tarairaya dadin sa guda da take yin magana yanzu duk dama ba akai akai bane..sometimes sai tayi kamar bata san su ba Sometimes kuma in suna maganan kama hankali har rungumar baban ta take yi tana kuka tana kiran sa.. Farin ciki da sabin nadama ke dawainiya da shi a ko yaushe Yanzu haka kudi suke neme wanda zasu tafi abuja amma babu hanyar samun komai ya tsanan ta wajen toshe musu ..abinci ma da kyar suke kaiwa bakin su... Gashi A kulli yaumin i dan abun ya dan taso mata sai tana musu kukan su kaita wajen mijin ta majeed ..ita majeed bata son jin komai sai shi Abun har na basu tausayi. Daga nan kuma abuja zazzabi ne mai zafi ya rufe Majeed bayan mumannan mafarkin ganin suhan dinsa a kabari dayayi tana bacci kuma babu cikin ajikin ta.. Ya razana sosai har ba a iya control dinsa anan gida ba sai da aka hada da asibiti aka sa masa drip.. Duk wannan Zarah bata sani ba saboda yau aka kira commitee meeting aka mata warning akan kudin data ke deba Fada ne mummana ya tashi tsakanin ta da su Ahmad da su faiza kowa ma ya juya mata baya cos akan kudi ba wani maganan friendship Abun ya matukar mata zafi she's now emotionally stressed zuciyan ta a cunkushe yake da boka da aljanu zata ji ko da matsalan office dan dole ta soma ramewa kullum ka ganta fuskan ta a daure yake kanta a zafafe yake ta shiga nan ta fice nan zama a inuwa ma sai ya gagare ta bare kuma bacci.. And then zagin data dinga kwarara ma wasu board members tana kiran su munafukai matsiyata tana tono asirin su ya sa suma suka dau abun da zafi Har Aka kai media ana sa'in sa ana cakka magana ma juna abun ba kyan gani kowa sai da ya san me tayi which is very bad for her ego tasan ko da ta sake farfadowa mutuncin ta ya riha ya zube a idon wasu a duniya kenan har abada.. Haukacewa ne kawai batayi ba gashi tasan bata da kudi kuma taci kudi sosai A yanzu inda suka yi baram baram da kowa tasan da kyar in wani abin ya zo ma su neme ta sai ta koma wajen mummy da complain.. Kafi nan Mum ke kan majeed a asibiti " ya juya kansa hefe yana zubar hawaye a hankali yana bata labarin abubuwan dake damun sa game da bacewar suhan tsoro ya riga ya kama zuciyan sa sosai yanzu itama kukan take amma ya zatayi? Sai tace ka haukatar dani kawai ka huta majeed? Ashe har yanzu bazaka saduda ka cire maganan suhan a ranka kayi tawakalli ba? Idan fa Allah yayi al'amarin sa ba yadda muka iya sai dai mu roke sa kuma yace mu roke sa cikin hakuri da juriya zai mallaka mana kyakkywan sakamako Muryan sa har na rawa yace "mum am trying amma kullum mafarkin ta ne a wani irin mummunan hali sai na ga kamar ma ankashe min ita ne mum... Ni menayi ma duniya haka ni kenan banda farin ciki? Me yarinyar nan ta taba ma wani she's always with me... mum tana mugun tausaya masa don ita kam tayi har tagaji yanzu ta zuba ma sarautan Allah ido akan maganan suhan she dont even want to go deep don duk randa ta tuna sai tayi ciwo.. Anty jamila ma nachan ta shiga gari gari tana raba hotuna da kanta tana neman suhan lungu lungu Tunda suhan ta bace bata sake zama ba har yanzu. ...in ta ci kukan takan ce gwara da kika mutu tun wuri baki ga wannan tashin hankalin ba anty maryam ...amma bazan zauna ba har sai na nemo mana yarmu ko araye ko a muce.. Zarah ta gaya ma mumy rabi'atu halin da take ciki sai suka shirya wani mafita "Suna kan shirin zata je wajen wani bokan ita ta nema musu masalaha Kirar boka duguri ne ya shigo wayar ta..dama tana neman sa 3 days back shiru ba dagawa ga aljanun sa sun ishe su da bani bani tana so suyi baram baram kawai a nemo wani mafita "Ta dauka ba sauran jira tace" haba boka kwana 3 kana gani ena kira baka dagawa wannan wani rin abu ne..ta ja tsaki ta daure fuska Wani murya daban ne ya amsa yana cewa".muna bugowa ne dom mu sanar da kowa Boka duguri ya kone kurmus a wata gagaruman lwutar bazata da ta taso masa a tukunyar tsafin sa ko kashin bayan sa ba a samu ba ... Wayar ma don ansa ta chagi ta tsira .... Mumy Bata tsaya cin end of the story ba ta katse wayar zufa ke keto mata... zarah ta ce lapya mumy meye kuma.. Kema an gaya miki suhan na samun sauki ko? Tace " boka duguri ne ya mutu a gobara ko kashin bayan sa sa ba a gani Baki zarah ta rike cikin mamaki...tace toh ya kenan mumy Tace "toh sai ki je dai ki yarda abun banza ai tunda boka baiya nan a duniya duk tsafin sa ya karye kenan ko Sauki ma ta samemu yanzu ba wani kashe kudi...ko ma huta da mafarke mafarke... Ajiyan zuciya tayi ta nemi waje ta zauna Zarah tace haka ne ..amma ya zamuyi mumy yanzu ena muka tsaya da maganan mu na dazu ai kin ji ance tana samun sauki wani wajen am getting scared mumy gashi anan office ena cikin matasalar kudi u know that Mumy Ta buga mata wasu zafafan harara tace ohon miki..ni fa kin ishe ni zarah Duk kokarin da nake akan ki baki gani daga yau kice wannan gobe kice wannan.. Ta marairace tace mumy kiyi hakuri mana ki taimaka min this is the last time ni so ma nake a kashe ta kowa ya huta.. Mumy Tace "naki na taimaka miki ba ido kika zuba ma majeed yana kwance tashi ya yi watsi da harkan ki ba? Ko ke baki da hakki a kansa ne kije ki sa shi ya dawo senses dinsa ya fara treating dinki kamar matar sa ai yana da dukiya ya biya miki bashin da kika ci mana.. yanzu ke din akwai wani kwararen kudin da zanje neman wani aikin ne Tace " no ..kije kawai mum nasan kina da shi ai zan biyaki In na karba wajen majeed yau . mumy ta tabe baki tace ok Amma mumy dan allah anemo wani bokan mai zafiii bana so ta warke ta dawo". mum ta harare ta tace toh kije ni gobe zan kira wata kawata ql zata min kwatancen bokan ta yarinya zakiga aikin manya don duk wani shege ma dake takura miki a office zansa arufe bakin sa.. Murmushin bazata zarah tayi ta ce yess maam i love you soo much mumy ... Nan suka kammala zancen na su zarah ta koma gida Tana isowa ta same sa da mum afalo dawowar su kenan daga asibiti tana kan lallabasa tana gyara masa zaman sa kamar baby boy ga abinci nan ta sa agaban sa dan dole tana so ya dan taba amma yaki daga kai.. Zarah ta karaso kansu kallo daya ta musu ta ja tsaki mai sauti zata wuce ...ya daka mata tsawa yace ta dawo nan... Ba tantama ta dawo cikin masifa yace baki da hankali zaki zo ba assllam ba gaisuwa kina mana tsaki akai Dama abunda take nema kenan.. sai ta dawo gaban sa da kyau..tace akan me? Wazan gaishar iye" mijin da yake azabtar da ni akan matar sa ta bace har yanzu bai same ta ko uwar da bazata iya nuna ma danta yayi kurkure ba... Mum tace"ah'a stop there zarah... ta fashe da kuka mai zafi dama kiros take jira tace" i wont bazan yi ba ai tunda matar ka ta bace u left me all alone baka kulani baka san ma ya nake ciki ba or dont i have some rights anymore? Suhan ita kadai ce matar ka ko... jikin mum yayi sanyi tasan bai ma zarah adalci ba kuma abubuwan data ke yawan tsawatar masa ya yi kenan amma sam majeed ya