Sashe 65
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Page 39-40* Tafiyar sa ke da wuya suhan ta shiga daki ta rarumo kayan ta ta fice a gidan Gidan anty jamila ta soma zuwa tana shiga wani dadi ne ya dada lullube ta ganin ummah zaune kan tabarma ..da murmushin ta ta zauna suka gaisa ummah tace " ah a suhan ..ya yau kuma naga kin fito da wuri lpya kuwa" lokacin suhan nakan mika hannu zata amshi gyaran domin ta cigaba da yi... Tace "Ummah ai ni kadai ce agidan bakowa yanzu..dama yayi tafiya ne shine nace Bari kawai nima fito da wuri... Ummah ta dan yi shiruu daga bisani tace" ah'a suhan, ni sam ban yarda da wannan sabuwar dabiar taki ba ai kamata yayi ki jira dai dai lokacin da mijin ki ya iyar miki sai ki taho bawai don ya fita sai kema kisa kafa kifito ba..wannan ba dai dai bane idan kuma kika fara daukar irin wannan salon Da haka fa zaku mike kuna ganin ba komai ba.. Ta Dan dago a sanyaye tace "Toh ummah naji bazan sake ba "... Ba kinji ba dai kidena kinji?... ta gyada kai a hankali tace toh ummah...anan anty jamila ta shigo ta same su sai suka gaisa sauri take don haka ta fice ta kyale su suka cigaba da hirar su .. Chan wajen 10 suhan ta kama hanyar restaurant ranar gaba daya aikin ta take hankali kwance bata ko tuna zarah. Haka rayuwa ta kasance musu yau kusan 4 days kenan da tafiyar captain amma sam suhan ta ki resuming bakin aikin ta na serving zarah abinci kamar yadda ya gindaya mata... Zarah na sane da hakan amma sai ta fuske ta cigaba da zuba mata ido Taso ace tayi ma suhan rashin mutunci amma sai ta ce bari dai ta fara neman shawaran kawayen ta.. yau da shike a office din ahmad ta wuni suna wani karamin meeting tsakanin su da acting board members na group dinsu .. Sai Bayan nan ne suka samu zama tare da faiza.. Wacce ke kan tsokanan ta cos a lokacin ana neman karfe 9 saura na dare amma zarah bata ko motsa ba bare ta yi maganan komawa gida.. Tace" kawata watoh don majeed baya nan a gari shine zaki kwana mana anan ko? Dan karamin tsaki zarah ta dan ja tana kan latsa computer batare da ta juyo ba tace" hmm faiza kenan.. u know that ko yana nan ma in naga dama zan iya kaiwa wannan time din so pls stop and dont make it an issure ta juya ta wata mata harara..... faizah tayi dariya tace a da kenan amma dai banda yanzu...zarah bata kula ba.... faiza ta kuma cewa ai na lura tunda aka kawo wannan amaryan nan naki sai abunda akaa ce dake kike yi ..zarah kin yi sanyi wallhy. Ta dan mayar da maganan in a seriious tone. Dan shiruu ne ya ratsa wajen cos har yanzu zarah na faman hadiye maganan da faizan tafada mata a ranta " babu abunda ta tsana kamar ace wani ya kawo canji rayuwar ta musamman ma in baiyi dai dai da ra'ayin rayuwar ta ba...amma ya zata yi? Gaba daya abun ya hau mata kai ya dawo mata har kashi biyu. ....a zahiri tana mugun son ta daura career ta ko dan ta kere ma tunanin kowa sannan tana ganin wannan ne kadai hanyar da zai sa mum da majeed suna daraja ta su daina correcting dinta cos she literally take all her mistakes as fair and independant ba ruwanta da ko dai dai tayi ko ba dai dai ba.. awajen ta "in life kowa da ajin sa da kuma matsayin sa so talaka ya zauna a talaka mai kudi ya zauna a mai kudi sannan haka ma mutum kaskantacce da mai daraja basa taba zama waje daya.. Ta dan juyo ta kalli faizah Tace :i dont have thy time faizah.. ni dai nasan nafi karfin su.wallhy kema ya ishe ki hada ni da wancan yarinyar she's nothing but a slave to me .maganan miji kuma all i know iz mum ke cusa ma majeed zama da ita i dont think ma zai tabaa son ta ..ko bakisan yanzun ita ke mana girki agidan ba?.infact doka majeed ya kafa mata akan tana min food services ko baya nan so u see!! bawata sai ni kuma wallhy nasha gaban kowa.... Tana kammala maganan ta dan yarfa hair dinta baya stylishly tana yatsine.. Faizah ta tabe baki tace hmm i like that... amma kinsan ranar da mum tayi mana rashin m din nan gaba daya sai naji na rusuna yasa sai naga kamar duk suna bayanta an bar mana ke a tsakiya. Hmmm mum ne fah kuma ya wuce kar ki damu faizah...dama buri na na sami hadin kan majeed wajen bude career ta kuma na samu so what? Indai wannan yarinyar ne kuma kar ki wani tada hankalin ki hadin kanku kawai nake nema by the time naci uban ta na wulakanta ta dakafar ta zata yi parking tsummokaran ta ta bar min gida na.. Faiza tace"Of cous gal sai yanzu naji magana..wannan ai ba sai kin nemi ni ba ko bakki nan zamu iya miki komai.. matsalar dama wannan mother inlaw naki ne amma she's gone now so zan ma aneesaha magana zamu hada plan din yadda zamu gara shegiyar ai sai ta gane kuran ta...da haka suka cigaba da hirar su ranar sai wajen 12 na dare zarah ta dawo mansion. Da shike ita kadai tasan majeed bai karasa US ba sai ta kira shi ta gama zuba masa makirci da hade haden da suka shirya da su faiza kafin nan tayi bacci.. Washe gari da safe suhan ta kammala shirin ta tsaf tana kwance tana jiran lokaci wayar ta ne yayi ringing..tunanin ta anty jamila ne ko zuby amma sai taga new number ..ta duba da kyau bata gane ba sai kawai ta ajiye a bugu na hudu ta dauka cikin sanyin murya mai dauke da dar dar tace salam" Shiru ne ya biyo baya kafin ta tsinkayo muryan sa yana cewa wato ba kiji ko? Zarah tace baki aikin ki tunda na tafi baki taba serving dinta komai ba "wai ma kafin na tafi me na ce kina yi agidan nan kin manta ne ko raini ke damun ki? Ta dan turo baki kamar wacce ke gaban sa cos dayayi maganan saida taji faduwar gaba..tace toh waye kuma zarah ni ban gane ta ba!!.. ..abun ya bashi haushi da mamaki yace "toh?baki san wacece zarah ba?hmm toh kar ki taba gane ta In kin ga dama" en dai nazo na sameki ne dakai na anan zaki gane da kyau..ya dan ja tsuka Dan shiruu tayi daga baya tace ...ni babu abunda banayi ai kaima ba gani kake ba c'mon quiet ya fada da normal voice dinsa cos rashin kunyar nata burge sa yake..yace "nidai idan na sake ji ance baki aikin ki just know that idan na dawo bazaki ji dadi ba. Toh naji.. ta fada kasa kasa tana murguda baki....ya katse wayar sa dan karamin murmushi yayi yace kwaji da shi ai Dan karamin tsaki ta sake ta dan tabe baki cikin ranta tace:mm mmmm wai ankai kara kenan ashe ana jin tsoro na tunda ankasa zuwa a same ni... Ai Sai dai nayi don ya dada sa baki amma karyan wata ta zo ta sani nayi mata girrki. Ko da ta fita ta samu zarah har ta fice so sai ta bada izini masu aiki suyi abinci su ajiye mata kafin ta dawo..altho bata taba fadan hakan ba amma sai suka amsa mata a ladabce sannan ta fice. Tunda ta fice sai Wajen karfe 6 saura ta dawo don haka ta shiga ta kimtsa kanta tsaf kafin ta dawo kitchen abincin da tasa aka dafa aka bar mata shi tayi musu warming ta jera su ta fito da sunkan dinning ta shirya tsaf ta koma kan kujera enda suke yawan zama da mum da tayi zaman ta tana kallo Chan wajen 8 Su zarah suka shigo surutun data soma ji ya tabbatar mata ba ita kadai bace sai ta dauke kai bata sake kallon wajen ba.. Da wani irin wulakantaccun kallo suka wuce kowace daga cikin su sai da ta ya motsa fuska kamar kashi suke gani yana zaune ..ko ajikin suhan don bata ko kalle su ba ma bare ta san me suke yi..su ukun suka wuce a gaban ta suna kaiwa daki suhan itama ta tashi itama ta koma site dinta... In not less than 20 minute maid mai suna sarah ta buga mata knock tare da sanar da ita zarah ke kiran ta.. Ba musu ta fito sanye take da dogon riga baki mai shape ba ko kwalliya akan fuskan ta she looks preety and natural.... Sarah tace ma zarah gata nan madam tare da rusunawa ko amsa ta basuyi cos hankalin su nakan suhan dake takowa hankali kwance .. Aneesah ta dan tabe baki tace tabbbbbbb... Nan Suhan ta karaso kan dining inda suka jeru agaban abincin kamar wasu yayan sarakuna Bata ce uffan ba ta ja ta tsaya...bayan musayar kallon banza faiza ce ta daure tace" a gidan ubanki haka ake serving abinci da bazaki zo ki yi mana yadda ya dace ba...? Zarah ta karbe maganan da cewa "pls hose down frnd kar ki bata yawun bakin ki kauyanci ne ke damun wasu amma kwadayi yaki barin su zaman wajen daya " tace" cmon will u open this filty thing you call food..? Suhan na shiru bata tanka ba bare ta nuna alaman bacin rai tankar bada ita sukayi maganan ba haka tayi....don ta lura intayi hakan sosai ransu yake sosuwa ..sai ta bude abincin ta shiga serving dinsu ko wanne ta sa masa komai a gaban sa neatly..tana yi baji su bai yi shiri ba suna mocking dinta da maganan banza cikin hirar su amma haka ta danne zuciyan ta har ta gama kafin ta ja gefe ta tsaya... Aneesa ta dan leka kan abincin tace" model pls ki soma tabawa ki gani in yayi