← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 225

Sashe 116

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *reminder: Under 18 *Page 45-46* Majeed Koda ya bar wajen A hankali yake tuki jiki ba kwari" he knows he's deeply hurt and confused at the same time.... babu abunda yafi bashi haushi kamar yadda suhan ta boye masa komai shi da mum.a ganin sa koma meye ne ke tsakain su tunda akarkashin sa take zama ya zama mata wajibi ta sanar da shi. Amma to meyasa tayi min haka"ya dan buga hannun sa kan stairi Idanun sa sun kada yanayin sa duk ya sauya lokaci guda. Tunani kawai yake amma ganin bazai iya amsa tambayoyi dayawa a ransa game da hukuncin da yake shirin yanke mata ba sai ya koma gefe kadan ya dakata da tuki yayi gefen hanya ya tsaya" danna control button daga jikin motar yayi sai wani madaidacin face screen ya bayyana agaban sa ya sauke sit dinsa baya kadan ya jingina kai sai yayi dialing number mai taken "mahmud merah" Bugu daya ya dauka wani kyakkwan mutum ne ya bayyana tamkar bature haka siffar sa yake don kuwa sosai Ya kere captain hasken fata daga ganin environment din da yake zaune kuma kasan ba a kasa nigeria bace" Gaisuwar kirki basuyi ba yace lpya dai ko? Wai Kuka ka keyi majeed meya faru zarah ce ko? Talk to me mana why are looking like this wat happen? unease mahmud ya kure sa da ido cikin damuwa.. Shikuwa kansa ya dan kaucar gefe ya daure fuska yana rarrsahin zuciyan sa " wai meyasa abu kadan yarinyar na tayi sai ya dame ni ne?this is just a purnishment"... ya raya take aransa"Jin mahmud yayi masa wannan tambayar sai ma ya dada rikicewa Da kyar ya daure ya juya ya kallesa" sauke ajiyan azuciya yayi don kuwa mahmud sai da ya dan ji wani irin da suka hada ido ya san kafin majeed ya kira shi irin wannan kira sai abu yakai makura a zuciyan sa... Bai bata lokaci ba ya sanar da mahmud A- z abunda ya faru komai bai bai boye ba cos saida ya fara maganan ya soma jin nauyin dake kan kirjin sa na raguwa " yace im sooo confused ni kaina bansan mena keyi ba i just want to get out of all this. Mahmud ya danyi shiruuu na dan lokaci yana lailaya maganan aran sa..baby ne a hannun sa sai ya ajiye babyn a gado sannan ya juyo ya fuskanci majeed da ke lafe akan seat din chair kamar mai shirin yin kuka " yace lallai wannnan babban al' amari ne amma bai kai ka daga hankalin ka har haka ba majeed pls just relax lets go throu it together yace toh mahmud ena jin ka ai.. Mahmud ya gyara zama yace majeed"im sorry sai dai kayi hakuri dani amma ni dai anan abunda zan gaya maka shine laifi kun riga da kun aikata shi en maganan dukan ku bance ita suhan bata da laifi ba.... amma fa kasani naka yafi yawa aciki... ya dan tabe baki yace hnm but how ? thats just what i want to know mahmud me laifi na guda daya toh? Mahmud ya tari nunfashin sa da cewa ai kusan duka ma laifin ka ne" cos kai kafara kawo wannan matsalan gaba dayan ta... yanzu kuma har kai ne zaka ce zaka kai maganan wajen mum wai ena hankalin ka yaje ne? U will only complicate the issure more ka tsaya dai kayi tunani.... yayi shiru daga bisani ya ce nifa kaina a kulle yake i cant think ..wallhy haushin komai nake ji u wont just get it mahmud yace toh dakata na tambaye ka" ai tun farko mum ta gaya maka ta amince da yarinya shiyasa take so ka zauna da ita a matsayin matar ka u object and then she emphasise isnt it? Yace yes..amma ai na gaya maka yadda mukayi da suhan din Aha there you go.. toh asali wai me ya hanaka kwantar da hankalin ka ka bi maganan mum din kamar yadda ka saba da chan? I m sure inda baka razanar da yarinyar nan ka takura mata har haka ba bazata yi kasa agwiwa wajen sanin darajar auren ku ba..u tought her how to disregard ur status as her husband ...majeed da ka nuna mata kai mijin ta ne wallhy bazata maka wannan haukar ba" Ya dan tabe baki baice komai ba mahmud ya cigaba da maganan sa bai kula ba Yace ... "all in the name of an aura maka watsatiya? bayan na ure not sure about that yet .....gashi yau da bakin kace wani wawa yayi yunkurin raping dinta... .hmmm dosent it make sense to you now that yarinyar da zata je neman nakan ta a kasakantaccen waje kamar na siyar da abinci bazata fuskan ci barazana irin haka ba Why did u think that har zata bar zuciyan ta yakai ta ga aikata wani abun? ai a ganina wanda suka kashe zuciyan su suke bin maza ba masu nema a wahale ba ne... dats if u think don talauci take yi.! gaskiya nasha mamaki abunda ka fada sosai sai yamin kamar bakai ka aikata ba.... i mean kai da kake bamu shawara kullum ashe zaka bar kanka kana fada tarkon zuciya?u just over reacted with that girl kaki bada hankakin ka ka fahimci komai game da ita Majeed yace ok fine naji don baya so a dago masa nan din...amma ni gaskiya zan gaya ma mum bazan iya boye mata komai ba ...mahmud yayi murmshi cos yasan majeed baya so ya bude zuciyan sa ne kawai ya dubi abun da kyau.but it seems like akwai boyayyeen conection na wani feelings da yake ma suhan aransa amma bai gane ba tukun.. Mahmud Yace fine ai is your call kai zaka ji jiki ..kai kanka kasan mum has the right to be upset with you don nasan dole in akaje warware magana suhan itama zata gaya mata abunda kaima kake boye mata game da zaman ku.hmmmmm To me akayi kenan ka rabu da ita sannan ka dasa ma mum wani abun aranta? frankly speaking laifin ka zata gani gaba daya ma and you wont like the outcome ena gaya maka... don wannan ai karamar yarinya ne yau akace tsoron ka ya hanata fadan maka tana fita wani wajen wallhy kowa zai yarda sai dai wanda baiji labarin nan ba. Shiru captain yayi bai ce komai ba...mahmud na lura ya sani sarai maganan ya taba ransa amma sam baya so ya nuna afili...sai ya shiga rarrashin sa cikin sanyin murya yace"Please ka nitsu mana kayi corecting mistakes dinka majeed Koda suhan bata cika macen da kake so ba amma ai qaddara ya hada ku zaman aure sai ka hakura ka bar ma Allah komai kayi biyayya ma mahaifiyar ka kamar yadda ka saba ..anan zaka ga sakamako mai kyau" ka tuna fa is not easy for her nor isit for you besides baka san meyasa take zuwa neman kudi ba.and that man too shin kataba tambayar ta gaskiyar abunda ya hada ta da shi a matsayin ka na mijin ta? Look mata fa ba kamar yadda kake tunani bane mai aikata abu ba ka taba gane sa a fuska sometimes seeing is believing yes" but it can also be decieving... so pls think deep kar kaje ka sa rayuwan ka wani yanayin da bazaka ji dadi ba nan gaba. Lokacin zuciyan sa yayi sanyi Muryan sa har na rawa yace toh what are you tryng to say" ni yanzu me zanyi mata.. Mahmud yayi ajiyan zuciya yace "All im trying to say is ba sai ka kai maganan nan ko ena ba..ba kuma wani maganan saki ko rabuwa da ita..compose urself and know her teach her how to be a wife show her that ure her husband Amma abunda ka keyi yanzu ai ba adalci bane fisabillahi ..pls go back to her ka gyara dakan ka tun kafin ya kwabe maka.. Yayi shiru Baice komai ba don sai yanzu zuciyan sa ya gama sanyi har yake iya kai wani tunani na daban a zuciyan sa .he knew that Tunda ya aure suhan ya kasa sama zuciyan sa nitsuwa abubuwan da yasan bazai iya aikata ma mace bablbma duk ya aikata akan ta he just feel complicated.. Chan ya dago Yace thanks men" i think i have to go now..anjima zan kira ka..mahmud yayi murmushi ya ce ah to Allah ya bada sa'a Nan ya katse wayar ya maida shi position dinsa minti 2 bai kara ba ya juya ya koma wajen da ya barta Suhan na durgushe ba abunda ke yawo a brain dinta illah"Me zan ce ma ummah da mum idan ya je ya fada abunda na aikata ma kaina yau? Yau na shiga uku ta daura hannu akai cikin firgita da rudani... Kuka takeyi sosai har ta rasa meke mata dadi gashi babu takalmi bare dankwali a kafar ta... dan gefe da hanya ta koma ta takure gefe guda tana jiran makomar ta din harga Allah ta sadaukar yau.. Kanta a tsugune har yanzu tana kan jira koda ma wani abun hawa zai kifta don hanyar shiruuu ne tun da ya bar wajen wani motar kasuwa ne kawai ta wuce daganan babu abunda ta sake gani Yana yin parrking ya sauko Bai ganta ba har sai da ya shiga dube dube a kasa ya hangota ta takure....ba wani bata lokaci ya yo kanta ..bata hankara ba taji anyi tapping dinta kadan sai ta dago a dan tsorace suna hada ido ya jawo hannun ta ya shiga tafiya da ita ya maida da mota daga nan babu wanda ya tanka har suka isa gida... Shiruu tayi tana binsa a baya har suka haura sama dakin sa ya wuce baice mata komai ba haka itama ta shige nata dakin.. Its already past 2 na ranah don haka wanka kawai tayi ta dauro alwala ta yi sallahr azahar ta kwanta ga shi babu jakan ta bare ta dauki wayar ta ta ce zata kira su ummah." Shima kusan hakan ne bayan ya samu long shower yay sallah baici komai ba haka ma bai motsa
Chapter 116 · 0% Book details