← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 225

Sashe 73

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Page 23-24* Daga bakin kofa ya tsaya don Alokacin jin kansa yake free don har zuciyan sa ya gama shirya masa yadda zai na cin uban suhan daga yanzu a gidan nasa.. a ganin sa zai bata wahalan da zaisa yadda ta sa mum ta sa shi auren ta haka ita dakanta zata sa mum ta warware . Itakam Ko motsawa bata yi don kuwa kallo daya zaka mata kasan bacci ne mai cike da wahala da kunci da nauyin xuciya.. Ga wani uban shessheka da take ja har kirjinta na dagawa a hankali sai ya soma tahowa setin inda take yayi zaman sa akan side drawer ya kura mata ido.... Looking at her very innocent cute face.."waje daya ta rakube ta takune kanta tare da nade hannuwan ta kamar jaririya akan kafadar ta ko ena jikin ta a kame ta sake sai bacci takeyi "nan ya dada duban ta yace mmmm"amma ancuci kyakyawan halitta..just look at her she is soo beautiful amma bata da good personality ni bansan me suke ji ajikin maza ba da suke watsar da kansu ..yayi kwafa ranshi haka kawai yake baci.. A haka Kusan minti 10 ya dauka wajen yana kan kallon fuskan suhan zuciyan sa na admiring duk wani tsari da lungu na halittan kan fuskan ta amma sai dai sam ya kasa ganewa sai ya dauka ko normal ne shi dai gaba daya so yake yanajin haushin ta. Yana Cikin hakan ta motsa kadan tayi wani wawan yunkuri gamida murdawa alaman jikin ta yayi tsami daga yanayin kwanciyar ta mayafin kan nata sai ya warware yayi gefe suman kan nata ya dada sukurkucewa dama gashi kan nata ba akan pillow yake ba daf yake amma bata daura akai ba Sai ya dan ja da baya tare da dawo dakan shi cikin seti..xuciyan sa ne tace majeed ka nitsu kar kabari ta ruda ka da halitar jikin ta kamance da qudirin ka a kanta.. dama chan haka watsasun mata suke kayi hankali majeed ...kar ka shagala kaifa kafi karfin karuwa in mata ne baga zarah nan ba.? Sai ya daure fuska shi kadansa ya dada fizgewa ya sake maida hankali kan suhamln nan ne ya lura da yadda take moving uncormfotably da closed eyes dinta alaman wani abu ke damun ta... shiru yayi ya kure ta da ido chan sai ta sa hannu tana dan sosa kunnen ta har ya fahimci ashe strands din gashin kanta daya barbaje ke shiga mata bulin kunne ba shiri ya sa hannu ya zare mata su sai ya shiga maida mata suman kanta baya gaba daya yana yi yana shafawa a hankali...sosai ya a shagala amma bai gane ba don alokacin ko xuciyan baya jin maganan ta..jin inuwar hannun sa akan ta yasa ta bude ido a hankali suna hade ido ya zare hannun sa cikin sauri ya dan ja da baya itama firgit ta mike tayi baya da sauri tana maida numfashi... ko magana bai mata ba ya kure ta da mugayen idanu cos haushin kansa ya fara ji da yake saurin fadawa wani yanayi"yace anya ma na shirya cin uban yarinyar nan kuwa ohhh my god whats wrong with me? Yake tambayar zuciyan sa. Kuka suhan ta soma yi a hankali don kuwa kanta ne ya soma mata wani azababben ciwo wanda ya dada tunzura captain..ke!!! Ya daka mata tsawa Kukan me kike ma mutane anan..? Tayi shiru tana faman rage sautin kukan amma tsoro takeji sosai gashi ha kowa alaman waje yayi nisa kowa na bacci. Batayi wata wata ba A hujajan ta sauko kasa tace ""kayi hakuri nasan nayi maka laifi amma dan Allah kar kamin wani abu ... ni wallhy bana son auren nan ka sake ni na koma wajen ummah na na rokeka Kallo ya bita da shi Yayi tsaki ya kau da kai kamar baiji ta ba "Yace wai ma kukan me kike yi ena tambayar ki Cikin hanzari tace babu komai "yace,ohhh iskanci kenan ko,wani auren ne zakice min baki so ai ke kika kawo kanki nan so u most be ready to stay bana son munafurcin banza da wofi.. Nan ma kuka ne ya kufce mata cikin dagon murya yace"cmon shut up maza kame bakin ki yanzun nan... Cikin rudani Tayi saurin kame bakin ta tayi shiru sai tears dake sauko mata.. Ya mike tsaye ya kalleta ya buga karamar tsaki "look bani da lokacin ki don haka ki nitsu da kyau ki saurari abunda zan fada miki yanzu don bazan sake maimaitawa ba : A hankali tace toh bai kula ba ya cigaba" Nasan ke wacece ce amma ke baki san ni waye ba ko? toh yanzu zaki sani: Ya juya yayi wani lungu Cikin dakin nata taga ya sa hannu wani waje ya budu bindiga ya dauka yayi loadin bullet tana kallo yayo kanta. Jikin ta ne ya tsananta rawa tana karkawa har tana karkacewa don tsoro Ya bata rai ya ce get down .... Tayi saurin sauka kasa a razane tayi kneeling gaban sa tsaban yadda take shaking hannun ta yakasa zama kan bakin ta Yana kallon ta ba imani ya daura mata bindiga akai... Cikin son ya dada firgita ta Yace idan baki nitsu kin bar wannan rawar jikin ba zan kashe ki ...tuni ta sake bakin cikin firgita ta tsala ihu cikin razana ta shiga birgima akasa tana neman ceto ga rudani da tsoro yayi mata dabaibayi.....ko ajikin sa ya dada jan bindigan sa ya nuna kan ta alaman in bata masa shiru ba zai harba "kyat kyat taji gashi ya daure fuska.. tuni ta tashi ta nade kanta waje daya ta dunkule tana rawan jiki kukan na fitowa ciki ciki.. Yayi murmushin mugunta yace good" ashe kina da fahimta ai da kuwa yau kin gane kuran ki ..tunda aure dani kika zaba dani zaki zauna har karshen rayuwan ki bana sake ki Daf da ita ya zauna yace" da bakin ki kikace wai baki son auren nan? Da sauri ta gyada kai tace eh bana so,yace..good, waye kuma yasan hakan bayan ke?..tace kowa ya sani ..yayi murmushin mugun ta yace perfect kinga kuwa duk randa na kashe ki ba mai ganewa hasali ma in nace musu ke kika kashe kanki kowa zai yarda tunda ansan baki son zaman aure sai yawun banzaa.. kinga sai ki mutu a banza babu ruwan kowa ko? Ya karasa sounding irin ko ajikin sa A razane suhan ta dago kai ta kalle sa..ya daure fuska shima yana kallon ta "yace sharadi na na farko ma fansan sa kisa ne so ki sa ma ranki wannan 'muddin kika kuskura kika tsaba sauran sharudana toh ki saurare ni babu mai karban ki a hannu na sai mutuwar ki Suhan A tsorace take amma ita kanta bata san ya akayi ta watsa masa harara ba .tace nidai wallhy bazan iya ba.. in baka son auren kaima ai nace ka sake ni na tafi bana kara shiga tsabgar ka ni bana bukatar zaman gidan ka bare cika wani sharudan ka ni wajen ummah na zan tafi ...sai da ta karashe maganan kuka ya kufce mata don ita kanta bata yi niyyyan amsa shi ba don kuwa tsoro takeji matuka.. "Yayi ajiyan bindigar akasa ya chaukomota tare da murda hannayen ta biyu saida suka yi kas kas ...ihu zata sa ya tsare ta da razanannun idanun sa tare da cewa ,,.idan bakin ki ya sake motsawa sai na karya ki marar kunya kawai mani kike fadan haka? A zuciyar sa gani yake duk abunda takeyi salo ne na yaudara don ta cimma unknown burin ta akanshi in har ba son auren take ba meya kawo ta gidan sa yanzun..da bata san da hakan bane ta bari aka daura auren da shi iskancin banza da wofi yar rainin hankali kawai ..."ranshi a bace yake surutu cikin ransa suna kallon juna da suhan dake hawayen radadin damkar da ya ma hannun ta duka biyu. Yace:babu ruwa na kuma babu enda zaki je bana sakin ki har sai nagada ma. Ta fashe da kuka mai ban tausayi..batace komai ba Anan ya sake ta ya juya mata baya " bazan mai maita miki sharadi na farko ba saboda kinsan fansan sa Saboda haka Zaman ki anan gidan cikin salama yana daga wajen ki ..daga yau ni Zan baki sharudan abubuwan da zaki nayi don ki samu zama a gidan nan a raye Don haka kisa a ranki daga yau baki da gindin zama duk abunda nasaki yi shi zaki nayi kuma a kowani lokaci babu fashi bana son kukuskure Ita kam Tana shiru daga bayan sa tana hawayen takaici ga uban radadi da hannun ta ke mata daga damkar da yayi maga.. Cikin ranta tace." Allah ya sawwake irin wannan halin...laifi kalilan na masa amma ya wani sa aransa kamar maye..toh in sace motar nayi fa?msww sai na fada ma maman ka wallhy baka isa ba mugu kawai Chan kuma wani zuciyan yace "a'ah tsaya suhan. ki tuna fa zai iya kashe ki a banza yace ke kika kashe kanki kamar yadda yace ke kanki kinsan maman shi tafi kowa sani baki son auren sa gashi baida imani.. Tace wasssh wayyo Allah na... na shiga uku captain kam nakan zuba surutan sa na gargadi ciki harda ce mata saura yaji ta budi baki tayi maganan sa a wani waje sai ya karya ta..cikin tsawa yace": fatan kina ji na? A sanyaye Tace naji Ta goge hawayen ta cikin dauriya tace" yes... Ya juyo a fusace yace ..yes what? A sanyaye tace yes ..si..rrr ta kau da kai tana zubar da kwalla Uhmm uhmm Amma ..ammma..sir nace ba Bai amsa ba sai ya kure ta da ido ..ta dago ta dube sa"nace idan na bi sharudan ka ba kuskure wata rana zaka sake ni na tafi? Yayi dan karaman murmushi cikin ransa mai dauke da takaici..yace wannan yarinya akwaita da rainin wayo.. nasan ta ta san nasan ita wacece wai ko hauka take ne? Why most she pretend that shes innocent bayan tasan inda muka hadu...? Amma bakomai since rainin hankali take so nima shi zan na mata..ya dago
Chapter 73 · 0% Book details