← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 225

Sashe 67

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

dadin jikin ta.. As usual zarah da su anisa suka shiga tsula mata rashin mutuncin su..bayan ta jera abinci Anisah ta turje ita kam sam sai an kawo mata fresh coconut drink suhan ta daure ta sanar da ita babu kalar ingredient din data lissafa ayi mata dashi amma sam taki hakura da kyar sai tace taje tayi mata kowanne as long as is chilled and hand made Suhan Bata jin dadi sosai cos shes running out of patient ga tunanin halin da umman ta ke ciki abubuwa suka taru suka mata yawa... amma sai ta danne zuciyan ta bata bari ta afka musu kamar yadda take shirin yi ba ta kama hanyar shirya musu yadda suka umarce ta sukan abun na su ma sai ya dada yin tsamari don boro boro suke gaya mata bakaken maganganu wuce tunanin mai hankali suna shewa tsakanin su Ba laifi suhan ta kama hanyar shiga kitchen" ko karasawa batayi ba ta sa aka kira mata maids sarah. Tace dauko min antibiotics dinnan ena so nayi amfani da shi..duk dama tasha mamaki amma ba tantama taje ta dauko ta kawo ma suhan Guda biyu ne babu acikin sachet mai dauke da gida 12.. 30 minutes mai kyau ta dauka gaba daya da zuciyan ta ta sa wajen hada musu drink.... wani kayataccen carrot and cocumber drink wanda yaji kayan qamshi da flavors ta kammalaa ita kanta sai da ta ware nata daban a gefe guda don tasha kallo.. kafin ta sa nasu a cups ta yi arrangin dinsu gwanin sha'awa rediish green ne kalar drink din sai bai mata wahalan dura maganin ta yadda take si ba. kowa ta sa masa yadda take ganin zai serving dinsa zarah guda uku sauran kuma biyu biyu ta dauko ta dosu falo.. Tun kan ta karaso faizah tace" wallhy wasu mata dai sai a hankali..yanzun har wani kwadayin duniya zaisa na zauna irin wannan bauta" chab lallai talaka mai kwadayi baida zuciya sam sam sai yau na yadda..suka danyi shewa lokacin daf da so suhan take.. bata damu ba ta ajiye faranti a gefe sai dai yadda sukayi tunani ba hakan bane sai ta dauka tana mika ma kowa a hannun sa yadda ta tsara ..suko sai zuba rigima suke a ganin su duk isar su yakai haka da ruwan sanyi tayi drink din don haka qamshin da sanyi sai ya ja ra'ayin su ba wani jan aji suka shiga sipping...ta juya takai tray kitchen ta fito da nata a hannu maimakon taje daki kan kujera ta zauna daura da su ta zuba musu ido drink dinta na daga gefe bata ko taba ba tukun wajen shiru..kowa nasha ba wanda ya tanka jim kadan faiza ce ta soma reacting... abu wasa wasa ta zube kasa tana rike cikin ta cikin radadi duka suka yi kanta hankali tashe suna tambayar meya faru ana cikin haka Sai zarah ta biyo baya da shike abun na zarah yafi yawa anisah taga karamin tashin sense don kuwa tuni zarah tayi wani yar karaman suma tsaban azaban ciwon cikin sai aka bar anisah da abun da shike ita baiyi wani affecting dinta sosai ba duk dama tanaji kadan kadan ...gaba dayan su suka rikita wajen suka rude da koke koke kowa na neman agaji..kamar basu din ba anan suhan ta harde kafa Ta dauko drink dinta tayi relax kan kujera tana sha hankali kwance... tamkar wasan kwaikwayo a talabijin haka ta tsura musu ido tana binsu da ido suna tereren tashin hankali ... ga zarah a sume Ganin abun fa gaba gaba yake nan anisah ta shiga hada suhan ta Allah akan ta taimake su ta kira musu emergency ko zasu samu rangwami amma ena!! yadda kasan bata wajen haka ta basar da anisah. karshe ma da taga faiza na neman dauke nunfashi itama sai ta mike tsaye data bar wajen da rarrafe anisa ta kamo kafarta ....tace su..han pls don go..pls kar ki bari mu mutu mana ita kanta ta sha mamakin rashin tausayin su datayi sai ta dan janye kafarta tace wai meye ne kuma bana muku abunda kuke so ba?ni wannan ba aiki na bane so bazan yi ba... in kuna so na kira emegency sai ku kira shi ogan naku ku fada masa ya samun a list din aikin da zan na muku amma wai don ku?tabbb Kun san wallhy karyan ku kusani nayi darajan aure sa baku san dashi ba kuke ci...ta dan maida musu murmushi mai kularwa Cikin radadin takaici da fushi anisah tace haba ke kuwa ke wai wata irin marar imani ce".suhan tace iyeee to ni me zan muku ...da ni nace ku yi ciwon ciki koni na yaba muku ?ai mugun bakin ku yasa cikin ku ya hautsine dakan sa ni ba ruwa na... Wani azababben kuka faiza ta fashe dashi cikin ranta tace wayyo Allah na im dying here ashe haka yarinyar take da bakar mugun ta"so take tayi magana itama amma ciwon ya hanata tankawa Ga suhan sai tsula musu bakar rashin mutunci take ta ma nuna musu ita ba abunda ta sani game da abunda ke damun su don haka baruwan ta...dan dole anisah ta sauke girman ta ta shiga maqiya tana rokon suhan...amma fir haka suhan taqi da Abun ya ishe ta tace: kinga nifa wannan baiya cikin aikina na fada miki so ba ruwa na.... sai ku karata da shi ai ku a waye kuke kuma kunada arziki sai ku taimake kan ku ..ta ja tsaki mai sauti tace ni barci ma nake ji gud nite. Kaiwa nan ta haura sama ta barsu awajen.. A cikin dakin ta Dariya sosai tayi musamman in ta tuna yadda suka nuna rashin dauriyar su da mugun tsoron mutuwar su a fili cikin ranta tace muje zuwa"daga yau duk wanda ya shirya cin abinci na sai ya shirya fama da ciwon ciki.. da safe koda ta tashi jitayi ance a asibiti dukan su uku suka kwana... Wanka kawai tayi ba bata lokaci ta nufi asibiti domin duba jikin ummah kafin ta wuce aiki. *thanks for waiting fans wayan da suka min maga na a pc ban amsa su ba suyi haKuri na sauya waya ne .. so im using new chat babu kuma chat history repost if u can.. same goes to all masu cemin na basu book din sakamako daga farko wallhy ban dashi kamar yadda kuke tunani nima a wattpad nake dubawa mostly so u can also get it @surayyahms"DONT ask me pls nagode *surriem*[9/13, 13:44] Hapsy: * BRILLIANT WRITERS ASSO
Chapter 67 · 0% Book details