← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 205 OF 225

Sashe 205

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kada kansa baice udfan ba ya shiga wani sabon yanayi mai tsoratarwa amma da shike sun sa ransu ba abunda ke damun su har ya gama ya dawo dai dai" Yace kin ci sa'a ..za"ayi miki shaidanu sun tausaya miki. har zatayi murna ta kawo godiya ya dakatar da ita yace "amma fa da akwai sharuda guda biyu" Ta nitsu tace ena jin ka. Yace" na farko zaki kawo mana kayan aiki "mumy tace kamar me kenan? Yace danyen gawar mace mai juna biyu..da kasan kabarin ta"kashin tsusa..kashin bayan mesa Kangon zuma buran rikakken giwa da idon cinnaka baki ba fari ba... A haka ma saida ya lissafo ganyen da ko a littafan science bata taba jin irin su ba Daga karshe ya ce in bazata iya samowa ba ta kawo kudin aika aljanun su zaije kafin ta bada kudin aiki 800k ta ajiye mafari kafin gobe ta dawo..shi sam wannan bai wani dara shi cos manyan masu kudi dake zuwa yana biya musu bukata har in million akan bashi kudin aiki.. Sharadi na biyu yafi kowanne kaifi don haka ki nitsu ki ji in bazaki iya ba gwara ki yanke hukunci tun yanzu yace" Ta ce ena jin ka boka... Yace" idan aiki ya gamo dai dai kishiyar ki zata rabu daku. aljanu sun soma shirya yadda komai zai kasan ce.. Sai dai Ki sani mijin ki bazai manta da ita ba kece zaki yi kokari ki dawo da shi akalar ki don bazai taba samun ta da abum dake cikin ta ba har abada.. Mumy tace mutuwa zatayi ne?" yace mutuwa araye ba..ku dai kuyi watandar kudin aiki zaku ga cika aiki wajen mu... Zaraj tace ba matsala boka ..ena dai shikenan Yace e'e'e ah"a" dakata Sauran bazan fada ba sai mun gama komai kije ki dawo gobe ... Ba musu suka mike suka yi godiya suka fita.. . "Zarah kin tabbata zaki iya ? Tace yes mumy...tace kudin fa ? Kinsan fa duguri akwai aiki amma he's kind of demanding kudi mai yawa yake chaska.... Tayo murmushi yace wannan ba matsala ko ban da shi i cant take it from my co members Kuma ...kar ki damu mum bazan ma sa majeed anan ba bare ya yi zargn wani abu i will use my money ko da duka zan kashe im ready ke dai ki kasance tare dani Gobe nake so na cika buri na akan suhan. Mumy ta kamo hannun ta tace Good my angel..u will win definately..tayi dan murmushi karfin hali sannan ta wuce ta koma gidan ta.. Yai kwana ta ne amma Ko ta kula ta neme shi don aranta tana dada jan shaukin ending matsalan ta She just cant wait for tomorow" Cahn dare yayi cikin shirin sa na bacci ya shi ma suhan gudnite kafin ya koma wajen zarah... Armless shirt ya sa mai kama da singlet na khaki mai laushi da bakar wandon sa he looks hot and apearling Akan gado ya hangeta itama ta sanya white simple sleeping dress mai kyau da tsari sai dai ya na dan kauri... "suna hada ido ta yinkuro Kamar wacce bata jin nauyin katon cikin ta cikin shaukin murnan ganin sa ta yo kansa tafada kirjin sa. "This is what he loves most a kanta kullum tana nuna masa so wanda baiya gushewa he feel happy har cikin ransa da Allah ya bashi wancce ke kaunar sa sanyin idaniyan sa tun a duniya..... Ya dada kankame ta yace" mypreetylove is very happy today tun safe na ke lura dake wai miye sirrin ne? Ta sake murmushi mai sauti ta dago ta jawo hannun sa suka zauna a gaban gadon but a kasa akan mat so romantic sai ya jawo ta tsakiyar cinyar sa ya mike kafafaun sa yana shinshina ta yana shaqo qamshin ta.. Ta lumshe ido tare da lafar da kanta akan muscular soft arms din sa Idon ta a rufe ta sanyaya murya tace "" i love you sooo much sweetlove' pls give me a story i wanna sleep in ur arms right now before u go . Yayi kissing dinta agefen cheeks dinta he feels happy musamman yau da yake ganin ta a hakan"ko mum sai da tayi shaidan suhan na cikin farin ciki Yace wani irin labarin kike so" Tace irin naka mai dadin dadin ji..kan ya bude baki yayi magana ta ce miji na"kasan me'?? Ya dan girgiza kai hannun sa na dan shafa hair dinta a hankali "tace all my life i dont think i have thank you enouhg So,Thanks so much "tace har tana dan kakkame hannun sa cikin shauki Yayi slight murmushi da gefen bakin sa yace for what pretywifey menayi kuma yanzu ake min godiya" ta danyi shiru daga baya tace kamin komai a rayuwa ta..i neva tot zan rayu har haka cikin farin ciki da kwanciyar hankali in babu ummah na ..you took away my pain ..ka koya min yarda da gode wa soyayyar ubangiji ure my hero my true strenght... she sound ok data ke maganan amma she's already getting emotional a ranta sai ta daure tana rufewa da smiles masu nauyi ya dan yi murmushi yana dada squezing dinta"suhan tasan yadda take sa shi jin Yayi sa'a r samun ta arayuwan sa but she dont know that 'yace whoa" yau kuma abunda zaki min kenan i tot am the one giving stories here .. ta katse sa da wani sanyin murya mai ban tsoro da fargaba" tace i missed my mum soo much i was dead when she died believe me sweetlove... Hawaye dan karami ke son sauko wa mata amma ta hana ta cije ..ta dan dago tana kallon sa tace "but im alive now with u by my side ena ga zan iya fuskantar ko wani irin wahalar rayuwa kaine garkuwa ta kaine sirri na kaine kuma abun alfahari na... magangaan nata na ratsa shi ya jawo lips dinta ya bata quick kisss tare da sauke mata oily eyes dinsa na dan lokavi yace " kece rayuwa ta suhan' i was lost but you found me abunda kika min bazan iya fadan su a kalmomi ba bare kalma daya... "tayi dan dariya cos tunda yake maganan kallon shi take critically tana tunanin randa za'a ce mata shima baya duniya tare da ita... She can't control it now ta soma silent tears tana smiling at the same time....they got emotional amma sai ya shiga smiling hrtbrokingly yana share mata tears dinta da hannayen sa shi namiji so babu wannan a face dinsa sai abunda ke cikin zuciyan sa... Ya kamo ta again ya rungume ta a kirjin sa yana dan tapping bayan ta sofly" muryan sa na rawa yake cewa" "Forever is ours bazamu taba rabuwa ba har duniya ta nade ni naki ne.. Ire iren maganan masu dadi masu sanyin ratsa brain da shiga zuciya yake mata sosai itama hakan sai ya sake yana professing undying love din da yake mata a zuciyan sa in perfect words.. Har ta gaji tayi shiru ta naji ta lumshe ido tana sake boyayyen hawallaye tana smiling ba tace komai ba har tana jan shessheka... She feel safe with him yau wani yanayin kwanciyar hankali take ji aranta but she dont knw why na yau din kuma ya zarce na kullum kowa sai da tayi waya da shi su kayi hira don kuwa sosai ummahn ta ke fado mata arai... Har tayi bacci anan kasa a hannun sa bai dena shafa ta yana godiya ma Allah akan kyautar da yaba shi na farin cikin kasancewa da ita ba kullum yakan yi adduar Allah ya barsu da tsawon rai tare don sosai ya sa aransa wannan babban niima ne kuma albarka ne na musamman daga ubangijin sa... Ya dago ta ya ajiye ta kan gado ya rife ta "sai dai Har ya koma dakin zarah ya kwanta bai dena jimamin words dinta ba... Asubahin fari 6 yayi ma zarah agidan boka takai masa kudi cos da abun ta kwana a ranta... Yadda suhan ke jin sabom rairayin kwanciyar hankali ajiyan ita kuma tashin hankali ke damun ta haka kawai take jin bakin bacin rai... Da kyar ta runtsa don ajiyan cikim dare ta kasa zama waje guda daba don tasan zata iya cin karo da wani mummunan abu ba a yadda wutar abun yake soka mata zuciya adaren jiyar da ta fice cikin daren takai ma boka kudi anyi aiki.... Boka Ya sha mamaki daya ganta da safiyar Allah amma he's not affected cos ya gano she's soo desperate... Kudi mai yawa ya sake karba daga hannun ta...tana tsaye tana jiran sa tin kan gari yagama washewa da sanyin safiya ya dauko mata wani katon kwarya.... yace an gama komai saura ki gaya mana wa kike so ayi amfani da muryan sa Wanda idan kishiyar ki taji dole zata amsa ' da sauri tace majeed ...muryan majeed za ka dauka " yace ta wanke hannu acikin kwaryan tayi hakan ba tantama Ya juya da baya...muryan sa wani iri ya ce" Murkuszali sharban dam...ya sake maimaitawa alaman shedanun aljanu wanda za suyi aikin kenan yake yi da su" yace ku kira ta tazo gare ku ..ku jefa ta duniya cahn da nisa "daga yau na haramta mata magana da ganiya"har abadan ..uayi dariya mai karfi mai iska a haukace yake cewa Ku tura ta ku tura ta Zarah sai da ta tsorata duk karfin halin ta sai da ta koma daga gefe... Bakar guguwa ke hautsinawa a sama like a movie take gani gashi tana jin muryan majeed a cikin guguwar exactly ba maraba.. In not less 5second komai ya washe boka ya bushe da dariya mai ban mamaki...tayi tsuru tsuru tana so taji sauran bayanai Daga chan kuma Suhan tayi sallahn asubahi kenan amma wani azababben bacci ya hanata sakat sai ta koma kawai ta cigaba... cikin bacci take jin sweet voice na majeed kusan yafi na ko wani lokaci ma dadi yana cewa preetylove dina zo mu tafi ..ena so na kasance dake ki zo muje..kamar a mafarki take ji sai dai bata tashi ba amma da abun ya tsanan ta sai ta daure ta farka.. .tana farkawa taji muryan sa garau yana kiran ta kamar ta awaje a hujajan ta sauko akan gado
Chapter 205 · 0% Book details