← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 225

Sashe 33

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *ORIGINAL PAGE there has been a mixed Up ga asalin nan pls *Page 25-26* [9/4, 13:40] Surayyahms : 25 26 Mum tace zara yadai lapiyar ki kuwa where are you? Ta sake tambayar ta..Zarah kam sai ta dada kara sautin kukan nata dagangan ' tace ena abuja ne .. mum ta sha mamakin jin hakan amma sai tace ohhh.. Zara ta cigaba cikin sigar kukan makirci har ta na jan shessheka"mum kiyi ma majeed magana..Wai shine dan na fada masa na tafi bai ma tsaya ya saurarani ba ya ce wai na dawo yanzun nan mumy na ce fa bataa da lapya tun jiya take kwance "" toh shikenan ni bazan kula da mama na ba kenan mum pls ki sa baki cewa fa yayi in 1hr na dawo ni gaskiya bazan dawo yau ba sai mumy ta warke...ta karasheh a karkace tana jan numnfashi... Mum tagama jin ta batace komai ba ta tabe baki ta dube shi batare da ta katse wayar ba.."majeed kaji ai tace maman ta ne ba lpya?pls let her be mana...yayi dan karamin ajiyan zuciya ya dan kau da kansa cos yasani sarai ba gaskiya cikin lamarin zarah ....sau nawa mumyn nata ke ciwo bata zuwa ba shidai yasan akwai abunda ya kaita chan ba wannan ba amma sai ya bari kawai a haukan kishi ke damun ta... Ya karbe wayan ba yabo ba fallasa yace.ena mum din take bani ita mugaisah ..zarah batayi expecting zaice hakan ba tuni sai ta daburce baki na rawa "tace uhmm ai..ai bacci take yi doc yace kar ta ..ta tashi sai chan chan anjima ..ta murkudi baki Yace kk..i will call her bak anjima Allah kara sauki bai jira ta sake magana ba ya katse wayar ya ajiye ma mum akan gado.. Nan ba wani bata lokaci tayi masa rakiya private jet dinsa ne ya kaisa chan uS enda babban ofishin sa yake kafin ya fara setting operation Zarah kuwa ko minti 5 bata kara ba ta danna ma mumy rabia kira ta dauka ""tace hello yar arbarka ta zarah tace good mrning mummy na amma akwai matsala fa.." like how wani irin matsala kuma zarah?.. Zarah tayi ajiyan zuciya "mumy kedai idan captain ko mum dinsa suka kira ki kice ena tare dake baki da lpya sosai kinji?.... .mumy tace bangane ba where are you zarah... tace ""ena scotland me tare da su Ahmad look mumy nasan bazaki fahimce ni ba yanzu dana so sai na dawo muyo magana .... mumy tace "noo just tell me now meyakai ki scotland kuma .. Ajiyan zuciya zarah tayi tace mumy naje meeting ne i want to start my career ko captain yana so ko baya so "can you imagine dat wai anyi auren captain jiya..? Wani dum Mumy rabi ta ji a jikin ta gaba daya take ta sake kan wayar lakatar ya zame ta ja da abaya..cikin tsananin mamaki ta ce me kikece zarah?aure ,majeed din? ..zarah tace kwarai kuwa wannan muguwar mum dinsan ta sashi yi dan dole "but he claims he dosnt know the girl amma bazan zauna ya raina min wayo ba... . Hmmm gaskiya ne wannan amma nasha mamaki "good kinyi dai dai mumy tace ranta a bace.. Dont worry mum cewqr zarah kamar bata damu ba "yawwa mumy shyasa ma kikaga na bisu Ahmad kema ki shirya min yanxu ena so na hada contacts ne daga sai na sama ma companyn da zam fara processing babban mafaka kinga koma wacece ya auro ta shigo gidan tasan nafi karfin ta Nan ma mumy tace goood """...haka nake son ji ena bayan ki dari bisa dari "ashe dai banyi asarar haihuwa ba..zarah tayi murmushi mumy tace sannan in kika dawo ki sa ido sosai ... duk abunda ke wakana agidan ki ki fada min karki kuskura ki bari wani yayi ruling dinki don an kawo wata daban... ure a special woman always remember that ke ba dai dai da kowace mace ba ne.. Zarah ta gyada kai cikin jin dadin maganan mumyn "itama haj janan nasir din nan bawai na barta bane naga tana neman shige min gaba..zarah ta tabe baki tace just live her mumy banda lokacin ta kedai kiyi min back up din nan yanzu mumy 2 weekz zanyi daga nan na dawo ... zan kuma aika miki cash anjim...mumy ta washe bakin tace "to yayi Allah ya miki albarka oya get ready to work....Suka katse hirar su. Mumy da zarah Duk yadda suka tsara haka suka tafiyar don captain sai da ya tabbata ya kira kowa daga familyn sa cos dama in ya shiga bakin aiki musamman idan ma irin wannan ne ba'ajin motsin sa har sai ya kammala Gefen suhan kuwa baccin ta mai kyau tayi ba ita da tashi ba sai wajen 11.30am Kafin nan ummah ke tsaye bakin kofar gida da kayanta duka..wasu mutane agaban ta da alaman sunzo amsar key ne..batayi gardama ba ta basu key din gida...dama ita kam tunda ta karance letter baban suhan a daren jiya ta gane cewa gidan nasu ma ashe siyarwa yayi .. .. Tana cikin tattarawa zata nemi adaidaita taga saukowar anty jamila .. yar dattijuwa ce amma fes fes take don kuwa kallo daya zaka mata kasan idonta a bude yake ..yar kimanin shekaru 35 ne bazaura sannan itace kanwa kwalli daya data rage ma baban suhan.. Ta karaso daf jikin ummah tace .."ah ah ya haka ena sauka kina shirin fita ? Ummah tayi murmushi tace "wata sabon gani yau kece dakafan ki anan jamila?.. Dan dariya aunty jamila tayi ""tace an kauda mushe dole masu hancin shan iska suyi shawagi... ai naji ance azzalumin nan ya bar garin nam shiyasa nazo na dubaki wai shin dagaske ne ya aurar min da dota na suhan? Nan ummah tayi ajiyan zuciya tace " eh jamila suhan jiya aka aurar da ita nikuma ya sake ni kinga har gidan nan ma ya siyar masu shi ne yanzu suka karbe key waje na... cikin fushin bazata mai dauke da kunan rai aunty jamila tace "tsinanne mugu..toh Allah ya ture keya ta Allah bata shi ba.. ai naji duk abunda ya faru wajen wawan aminin sa oga siyasa wai yana cewa zai koma wajen zuwairah ko? Tohmm yafi ruwa gudu ..kekam muna nan tare dake yanzu haka gida zamuje tare dani ki huta naji dadin da kika samu yancin ki yanzu inba ma qaddara ba me zai sa ki hada jini da wannan azzalumin. ...ummah ta sauke ajiyan zuciya "tace ah a jamila bar wannan maganan kwara dai na nema waje nima na tsuguna don kaina kar na daura miki wani nauyi... don bazan iya barin inda suhan take ba ne dana koma garin mu.. Anty jamila tace ah a..wallhy bakomai waje na fa tamkar wajen ki ne nifa da chan halin yaya ibrahim yasa na yanke alaka da ku sosai bawai don bana kaunar ku ba wallhy ku kadai ne gata na da rufin asiri na a duniya shiyasa ma yanke hukunci tunda baya nan a gidana ai saimu zauna tare mu rufa makan mu asiri.. Da kyar ummah ta amince suka tafi" 2 bedrom ne a gidan aunty jamila sai dan pit toilet dinta mai hade da bayi suna kammala kimtsawa Basuyi wani dogon hira ba suka fito da niyyar zuwa shamud residence don duba suhan.. abakin titi suka ci karo da zuby itama hankalin ta ya tashi sosai da kyar suka hadu suka kwantar mata da hankali "ummah tace ...kar ki damu zuby suhan tana lpya insha Allah kije muku aikin inyaso daga baya zata ki je ki duba suhan din kema.. Daga kan gado' Tagumi suhan ta buga har yanxu bata sauka ba tana kan wondering ya zasu kare da captain" sannan wani irin sharuda zai sa mata Cikin haka mum ta shigo dakin... murmushi ta sake mata mai sanyi suhan sai ta sulale kasa ta dan rusuna tace ena kwana hajiya? Tace yata har kin tashi baccin ya ishe ki kenan?Tana karasowa daf suhan ta gyada kai a hankali tace eh .. toh tashi mana ai ya kamata ki kimtsa yanzun nan ma zamuyi baki .. Suhan ta tashi sum sum batace komai ba ta shige bathrum sai dai still bata iya using ba.yau ma shower ta kunna tayi amafani da wani goat milk shower gel ta wanke jikin ta fes.. Mum na zaune a dakin cos dama tana so ta dan gwada ma suhan wasu abubuwan.. tafito sanye da kayan ta still bata daura towel ba Mum ta mike tsaye tace ohh noo" ..ya baki daura towel din ba tayi shiru ta sunkuyar da kai mum ta ce to xonan na gwada miki wani abu.. nan suhan ta shiga bin mum ita kuwa tana nuna mata yadda zata yi in zata sa kaya ko amfani da wani abu a dakin ta a saukake Bayan nan sai da ta zaba mata wata dalleliyar dark brown but simple gown sabo kal ta ce mata kisa wannan idan ya dawo zai kaiki kasuwa kizabi irin wanda kike so kinji? Ta sunkuyar da kai mum tace toh ki shirya ga make up nan... tayi mata nuni da kan madubi ""in kin gama komai'saiki sauko ki same ni kafin bakin namu su zo Tace toh hajiya..nan mum ta fice ta barta Isowar su anty jamila da umma kofar shamud residence aka bude musu don dama ummah saida ta kira mum kafin nan ....Tafiya sukayi kusan minti 40 kafin suka kai cikin haraban gidan kalle kalle kam ba a magana musamman da suka dire cikin asalin gidan don saida aunty jamila tayi rikon hannun ummah...cikin zuciyan ta tace lallai wannan shi ake kira daula Anty jamila "tace hmm ni fa banga mutane ba sai tarin securites kamar bariki ko dai mun bata hanya ne?...kan ummah ta amsa saiga wata mata ta bullo cikin uniform dinta tace musu su shigo, nan suka bi bayan ta. a falour na biyu aka sauke su ko zama basuyi ba sai ga mum ta fito da farar ta... Suka gaisa cikin girmama wa da karamci ummah tayi introducing aunty jamila
Chapter 33 · 0% Book details