← Book details Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 209 OF 225

Sashe 209

Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ciki ai babu sauran abunda zaku lasha... Uselessly daya daga cikin su ke mirda murya yana kukkuni yace" haba oganniya tallabe kekan ki kinsan yanzu irin wannan muke so wanda ruwan dadin su ke kasa kasa ai daga ganin wannan ma zata yi dadi... Sai su ka maida abun joke "me ye sa kike haka ne ehhh kawai ki mana ita mu shana Suhan ta kame rigar ta tana labewa a bayanta tana rawan dari kamar wacce take gane abun da suke cewa" Matar tace "anki a baku ita shashun banza kawai.. kan na bude ido kar na ga kowa anan ko na fyede cikin yaro...a tsawace ta fada tana basu mugayen kallo Ba musu suka watse suna ja mata Allah ya isa aran su Kafin ta juya ta kalli suhan already tayi tsuguna kasa kan gwiwar ta ta hade hannu waje guda alaman godiya tana kan bulbulan hawaye masu taba zuciya.... Tallabe tayi shiru She felt her pained itama mace ce..sai ta soma tunanin me yakawo wannan kyakkaywar mace nan wajen kara zube? Bata tsaya dogon nazari ba ta kamo suhan ta tafi da ita gidan ta... Anan take observing dinta tana bata abinci da sauran su har ta soma declaring binciken ta cewa suhan ba yar kasar bane ma kwata kwata... But she want to protect her daga irin wannan abubuwan altho gaskiya imani ya mata kadan a zuciyan ta... Gashi suhan bata magana bare ta tambaye ta labarin ta ko ashirme ne ta gaya mata ta lura wani bin hankali yana dan shigo mata.. Wasa wasa suhan ta dawo yar gidan tallabe 3weeks kenan da ba tan ta a nigeria Takan je deban ruwa ta dauko karamin baho akanta da cikin ta dawo gida da shi.. Akan sata wanki da shara da sauran kanan aika.. In exchange kuma tallabe tana bata kariya da abinci da sutura tana sawa. Ranar da ciki ya kai 9month cass suhan ta soma zazzabi sosai It seems like abunda ke cikin ta ke son motsawa amma aljanun sun riga sun rike dam sun hana haihuwar Lokaci lokaci take nakuda amma sam babu progress in yayi ya bata wahala sai su dauke abunsu ta dawo normal tana aikin ta... Majeed was hospitalised Sati guda yayi ana sa masa ruwa A kulli yaumin sai ya sa an kara amount na kudin da zai bayar anemo masa ita amma shuru ba labari Mumy rabiatu kulluma sai tayi masifa ma zarah Akan haukar da majeed ke yi akan batar suhan" zarah tace ai baki ga komai ba mumy a hakan ne za ace na zauna da ita ni bana haihuwa ki fa dubo yadda ya kwallafa ta arai na san ba don mum dinsa tana tare sa ba wallahy da ya shiga duniya zararrre " mum kinsan ranar dana je wai zan gwada bashi baki na rarrashe shi kula yake yana roko na na gaya masa ko ni na boye masa matar sa ? Wallahy wani maganganun da yake fada min har yana sani fargaba i dont know that abun nasu yakai haka...he actually lost his mind i think he's his menatally ill "har cewa shikam mutuwar sa kenan ta zo masa muddin bai same ta he cant go on... 'arrghhhh Ouhhh "i was so embrassed "akan cinya na fa yake fada min zai mutu akan wata mace" ta fada a raunane cikin dacin rai tana tabe baki' Mumy ta tabe baki cikin kuna rai itama tana girgiza kai..tace tabb di jam ...aiki ja akanku..Allah ya sawwaka wannan ai sakarci ne da rashin tarbiya sam majeed din kun nan baida kunya ko irin jarumtar nan ma na maza bazai yi ba sai kace ba cikakken soja mai matsayi ba? Hmmm ikon Allah tabbb Zarah tace ohon masa "aikuwa zaiyi ya bari he cant live on like this sai na san yadda zanyi ya mance da ita ni sun ishe ni harga Allah... Mum tace yawwa ya ake ciki kin ji wani kotsi daga wajen boka... Ta dan yi dube dube tace " mumy dama maganan da nake so muyi kenan dake..kinsan me?wannan abun da boka ya bani ranar yayi min magana amma kinsa inform of dream ai yake zuwa ko.. Tace ehhn so what? Tace "cewa yayi suhan na labour amma sun rike haihuwar tana chan wani gari tana hauka ... Mumy tayo murmushi Tace amma kinsan nawa ya sa na ajiye masa...? tace noo Check ta zaro a jakan ta na zunzurutun kudi naira milliyon tamanin... mumy ta daura ahannu aka tace Wayyoooo Allah na wannan uban kudi" Akan me? gaskiya hakan baiyi ba ai abun yayi yawa wannan ma da kashe ta akayi kowa ya huta.. Zarah Ta firgita Tace shhhhh mumy ki dena cewa haka ..kinsan fa ance zamuyi facing atrosities da yawa idan muka karya namu alkwarin so pls calm down..da na shiga a harkan yankan kan mutane ba gwara ena biya ba ? Mumy bata ji dadi ba amma sai ta daure kawai ta ce toh shikenan amma gaskiya kudin yana yawa mu bamuci ba ana ba wani shege ai sam haka baiyi... Sai gwaff wani abu ya fado kan kafarta lokaci guda wajen yayi baki ya soma haurowa kamar kurji duk suka rude suka birkice.. Wayyoh wayyoh A rude zarah tace Mumy ena ga sune suke warning dinki? Kingani ko Ai saida nace ki bari zanyi kin ki yin shiru a rude muny ta shiga bada hakuri tana kuka tana cewa bazata sake korafi ba su cire mata abun Lokaci guda suka cire mata ta dawo dai dai Minti 2 bata kara ba ta dau jakar ta ta tafi ta kyale zarah anan... Ranar suhan na deban ruwa tallabe ta zo ta kirawo ta... Keken a kori kura ta daura ta akai ba imani kukur kur suka kai bakin wani hanya... Manyan manyan motoci ne sosai na safaran kayan cash crops da economic goods... Hannun wata mata ta damka suhan tace bani kudi na ga mace nan harda ciki... in ta haihu riba biyu ga abun cikin ta ga sabuwar karin kasuwanci ... Matar ta kalli suhan da kyau sai zare ido take ..ta dauko kudi mai shegen yawa ta ba tallabe ta juya abinta.. Kuka suhan ta fashe da shi gwanin tausayi tana bin tallabe ana rirrike ta amma sam tallabe taki ta juya baya ma bare ta kalle ta don tasan suhan ita ce mace na farko data so ta dawo mata da imani cikin zuciyan ta Hakan matar nan ta ma suhan karfi da yaji ta sa ta a mota suka kama tafiya ... Tayi kukan har ta gaji ta dawo tayo shiru ta rafka ta gumi After a very long jouney ta bude ido sai gasu awani waje daban wanda aka fi sani da lagos nigeria... Anan ma a bayan gari suke Sunan new madam dinta madam kande ice A gidan ta ake sayar da mutane iri iri akan ko wani farashi inma karuwanci zaka kai su bata damu ba in ma kashe su zakayi chan maka kayi alheri da mugun ta da su bai dame ta ba ita dai kawai zaka bata kudi sosai shikenan.. Duk wanda aka kawo suhan da su an saye Gashi ganin kyau da dirin hallita na suhan ya sa ta sa buri mai karfi a kanta.. Ga abun cikin ta a kullum gani take suhan Zata haihu amma sai dai tayi nakuda gadan gadan amma babu haihuwa Abun har ya so a damun kowa a wajen sosai.. Tun ana mata na bakon ta da tausayi har aka soma share ta kande ice ta na jira dai tasan don duk yadda akayi watan wata rana suhan zata haihu dan dole. Yanzu babu mai kulata in tana nakuda nata har ta yi ta gaji ya lafa... Daga chan kuma duk randa suhan Ta motsa sai abun nan ya bukaci kudi mai tarin yawa awajen zarah Kan aje ko ena ta kwashe millions daga acct din ta har wajen guda uku empty.. Gefen majeed kuwa an dawo da shi gida .. yanzu addua sosai ake yi masallatai da ko ena yau suhan dinsa 1month rabon sa daya ganta.... sai ya dawo quiet da kyar ya sa nitsuwa makan sa Mum da anty jamila na nan basu gajiya da bin cike da neman taimakon ana musu istihara Kaf dinsu sunki gaya ma majeed _sakamakon_ istiran... Thy alredy knew batar suhan bana alheri bane sihiri ne mai karfi sukan su malamai basu samu gayan cikaken details din ba Amma tabbas sun gaya ma mum suhan na cikin mummanan hali wahala da neman taimako Mum Sam taki zuciyan ta sawa ya yarda tana kan lazimi da ikon ubangijin ta amma da shike kowa abunda ke gani kenan sai abun yayi affecting zuciyan ta sosai Shikan sa mjeed bai San mum yanzu jinyar ta ake agida ba amma take daurewa take zuwa ta rarrashe shi every day... A cahn wajen suhan bakin ciki da kuncin rayuwa ya sa ta sake jikin ta sai yadda aka juyata kowa na aikan ta kamar karamar yarinya.. Sai dai sosai ta shiga ran wani old thug tsohon soja ne wanda rayuwan tantiranci ya masa tatil ya kuma waina sa da kasa ya dawo ya saduda... Haka kawai yake tausaya ma suhan sosai Daga bisani ya sa kansa yana kyautata mata friendly gesture da yake bata ya sa ta ke sakewa da shi har in ta ganshi sai tayi murmushi ....sunan sa oga rabi'u majeh kowa ya san shi har prison yaje amma shikam jin suhan yake kamar yar sa kuka in yaga tanayi sai yabi mata kadi... Ranar ma tafiyar ta ke nan yana kan binta da kallon tausayi wani keke napep yayi parking gaban gidan sa Leke yake yana mika wuya chan ya hango wani mutum jikin sa har na rawa ya sake kara ya daura hannu aka yayo kansa.. Rigar prison ne jikin mutumin so yana juyowa suka rungume juna da ogah rabiu suka fashe da kuka irin na jaruman maza mai ji kadai yasan akwai tashin hankali a cikin ta da nadama...... *Dedicated to all members na cikin ko wani groups a media dake coments Wasun ku ana kawo min chats da kuke yi muna gani a fans page dina so funy and inspiring wasu kuma da kaina
Chapter 209 · 0% Book details