Sashe 57
Sakamako Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_WATTPAD_ @: _SURAYYAHMS_ @ _IG:Surriem-sule_ *#Lovestory2018* *#romance#fiction..* *any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison,beware copy cats!.* *Page 37-38* Tan asuban farko zarah ta tashi ta soma shirin ficewa sabon office.. Bayan ya idar da sallah ya lafe kan pillow yana dube dube a system din sa yayi shiru alaman hankalin sa yayi nisa wajen abunda yake yi Har wajen karfe 7.30 na safiya bai ajiye ba.. lokacin ne zarah ta dawo dakin sa cikin shirin ta tsaf.... skirt da riga ta sa na suit d&g mai dan karan tsada da tsari gaba daya pitch ne sai black a yar cikin ... Da shike wandon ya dan kame ta sai tayi mugun kyau .. yana binta da kallo tana tafiya tana dan tattaba golden blonde din data kima akai cikin riigima ta zo ta zauna daf da shi tana rausaya idanun ta sai da yayi murmushin ba zata don ya san ba asaba masa hakan ba..ya sauke mata golden eyes dinsa tare da "cewa baby wai yaushe zaki fara sa native wears ne wayannan din basu ishe ki bane girma fa kike yi i think u need to cover pls.. take tayi wani irin dariyan rainin hankali ta dube sa da kyau..uhmm majeed kenan ure funy tabfada sigar irin wannan ai maganan banza kake .. Bai kula ba yace cmon im seroius zarah.. tace to wai banyi kyau bane ko me? Yace noo kinyi.. but i want you to cover your self wannan dabiar yaushe zaki bari ne ..u know im noy comportable da wayannan kayan naki this is 4 yrs kuma korafi na kenan amma kin kasa dubawa and u know that ...ta mike tsaye a dan gurguje cikin masifa tace"tohv i cant..kaga ni bana son neman fitina majeed ka kyale ni na sa kaya na nayi kyau.. ta daura hannu a kugu "wai meke damun ka ne kam naga kamar tunanin ka ya soma karkacewa kwana biyu ....and if u think am gonna dress up like that Your ugly dirty looking wife ure wasting ur time...ni dai bazaka na takuramin ba ehe...ta murguda baki... Ya ajiye system dinsa agefe da niyyar ta shi tsaye kamin ya amsa ta" salam alaikum suka ji daga bakin door ... Wani mugayen harara da tsaki zarah ta sauke ma bakin kofar tun kafin suhan ta karaso ciki.. Sanye take da riga da skirt pink ta daure dankwalin ta a karkace Tray din hannun ta ta ajiye gefen sa " ba tare da ta kalle sa ba tace ena kwana sir.. Ba bata lokaci Yace lpya... Daga nan Ta juya abunta ta fice.. Gefe da shi zarah ta dawo tace baby wato kana gani tana raina ni agidan nan ko ..wai kai kadai take gaisharwa nidin sarar tane? Ya dan kalle ta yana mamaki ....ta wani dake tana maganan kamar ba ita tagama fetsa masa raini yanzu ba..yace baby pls stop.. Gwara wannan ai yarinya ce ke fa? U barely respect me bare wasu na daban abunda kayi dama shi ake maka ...ta dan ja tsaki ta juya kai batace komai ba.....ya kuma cewa " da hankali zaki na binta zata gane itama..ta tabe baki batace komai ba still amma sai ta bude abincin da suhan ta ajiye.....cikin son ya ji bakin ta yace zakici ne" bata amsa ba.. da mamakin sa ta dau spoon din ta dan yi tasting daga bisani ta kai loma biyu..tana ci a ranta ta raya " ai sai kin game kuran ki a gidan nan sai na gwada mikibni dake ba daya bane im always the queen in this kingdom sai dai ki kare a slave din mu... tace baby nima ena son naci pls kace tana serving dina mana.. Ya sha mamaki sosai ya dawo ta gaban ta yace uhm uhm sai dai kije ki fada mata nikam ba ruwa na.. Ta dan tabe baki sigar ka dauka bazan iya ba ko? Nan ta mike ta fice a lokacin wayar sa ne ya buga ringin ya tsaya amsawa.... Tana fita dakin suhan ta soma zuwa ta turo kafar cikin isa da bunkasa sai dai bata same ta ba..nan ta gangaro kasa tayi hanyar kitchen.. Anan suhan take tana gogee sauran cutleris da tayi using zata maida su mazaunin su sauran maids kuma na gefe altho ko ena tsaf yake amma wasu suna kimtse kimtse wasu suna moping Dama Su Biyar ne a fannin girki amma gaba daya suke bada suhan girma a tunanin su ra"ayin ta da saukin kanta ya sa take shiga kitchen duk da ma ita matar gida ne amma ba kamar zarah ba.... shiyasa ko kadan ba raini a tsakanin su duk dama ba sa'ar ta a shekaru daga cikin su. .. Shigowar zarah Kowa ya rusina kasa yana miko gaisuwa sai binsu take da wulakantaccun kallo cikin Comanding voice dinta mai tayar da hankali tace waya dafa abinci a gidan nan yau? babban cikin su ta ce " madam nee.. tare da nuni da suhan a dan tsorace ..tsaki ta ja mai sauti cikikln takun ta na kasaita take tahowa har ta iso daf inda suhan take.. Ke" ta dan twiting hannayen ta tana jan attention din suhan.. a nitse ta dago ta maida mata kallo ba tace uffan ba..wani uban harara ta watsa mata "ehen?? where s my food ko ance miki na gidan ubanki ne da zaki na hana wasu kina ba wasu.. suhan data daure fuska batare da ta juyo ba tace.'ni bani da lokacin ki sai ki je chan ki sami mai gidan ya baki amsa bani ba..ta dan ja karamar tsaki itama... Huruwa zarah take kamar wanda zata tashi ..cikin hatsala ta daka ma sauran cooks din tsawa " kamar su suka gaya mata maganan kowa sai yayi waje salun alun aka barsu su biyu.... "Ke' wai ni sa'ar ki ne da zagi na gaya min magana duk yadda kike so ....toh tau sai na farsa miki baki Ke naga daman tambaya kuma dole ki amsa ni... Suhan bata tanka ba ta tsame hannun ta da towel ta ajiye .....warmer ta bude ta zaro abincin ta baki shiru ta kama hanya zata bar mata kitchen din ..da sauri ta biyota a baya dai dai bakin step na fita dinning area ta jawo ta karfi cikin masifa "how dare you? Ta fada cikin fusata .. ni ki kyale ni nace bana son fitina ....suhan ta mayar mata da dan dagon Murya" zarah hannu ta sa ta fauce abincin zata bar wajen dashi ....suhan ta tsare ta tace "ki bani abinci na ai kinada hannu sai kije ki dafa...."bazan dafa ba meye aikin baiwa agidan miji? Zarah ta fada da gatse tana mai da mata mugayen kallo..... Nan suka soma jaye jaye da abincin karshen ta gaba daya suka bata kayan su da shi daga karshe da zarah ta fusata ta ture suhan da karfi tayi kasa sauran abincin da yarage ta kwaba mata ajiki....tana cewa "shegiya mayya kazama ke da kuka gaji yunwa a gidan ku ke zaki ji dashi.. marowaciyar abinci matsiyaciya kawai...cikin bacin Rai suhan ke ture hannun ta tana mayar mata maganan itama" tace "in har yunwa muka gada ai ba zamu yi fada akan abinci Kamar kariya ba... amma kinga wasu ko ba yunwar suka gada ba hauka da asara zai hana su iya girkawa sai dai subiyo ta hanyar kokuwa dan salon kwadayi. ...abun ya bata ma zarah rai "ma wani banzan abincin naki zan yi ma kwadayi ?...hannu ta kai zata make bakin suhan suka ido da captain.. A dan tsorace ta ja daga kan suhan ta tsaya gefe tare da harde hannu cikin fushi tana diri tana dada kallin stains dim rigar ta... Da shike kayan suhan yafi na zarahn jin maiko sai ta mike tsaye zata bar wajen ..yace ke dawo nan.. Ta dawo ta tsaya ta kau da kai "Wai meya ke faruwa anan whats all this ya maida tambayar kan zarah ...yana kallon kasa yadda sukayi facali da abinci... Kamar jirah take" ta juyo a fusace" ai sai ka tambaye wannan marar kunya da ka ajiye a gidan nan.. ko ni ba mutum bane agidan nan da baza tana serving dina ba?...ya juya ba yabo ba fallasa yace ma suhan haka ne? Tayi shiru ta dan turo baki ..cikin tsawatar wa yace answer me " take idon ta suka kada tace " "ni fa bazan iya ba gaskiya ta san wanda zata na bata abinci bani ba ai zagi na ta keyi ...ta karashe maganan a kasale cikin shagwaba kamar zata masa kuka...tsaki mai sauti zarah ta ja ganin yadda yake bin sakaltaccen fuskan suhan din da Wani irin kallo ..sai kawai ta ji she is irked da yanayin ...abun sai ya bata takaici... Ya juyo zai yi magana har hannun ta na rawa wajen dakatar da shi...tace "ai ba laifin ta bane dama kai da mum kunsa tana ganin Kamar bani da daraja agidan nan... just see the way she pour trash on me... tayi masa nuni da jikin ta da Ya dan shafi mai mai kamar bai ga abunda ya faru ba hasali ma ita yazo ya samu tana kwaba ma suhan abincin ajiki amma da shike yana son ya tozarta suhan din sai ya dawo gareta.. fada ya shiga mata kamar itace bata da gaskiya Yana cewa" ..kar ta sake raina masa mata ..ya dada jaddada mata zarah ce kadai matar sa abun kaunar sa so dole ta mata biyayya kamar yadda zata masa...sosai zarah ta ji dadin wannan kalma ... Yace" daga yau ko bana gidan nan zaki na bata abinci dai dai da yadda zaki na bani ko bata nan dole ki ajiye mata. ..youbmust respect her kinji ko baki ji ba? Ta danyi shiru tana danne kukan da ke so ya kufce mata da kyar ta dawo hayyacin ta Ta sake...murya ciki ciki ta juyo tace naji..daga nan ta wuce ta basu wuri.. Dariya mai sauti zarah ta bi ta da shi tana cewa adawo kuma agoge mana kazantar nan .... ya dake yana kallon ta kamar ba shi ba tana kammalawa suka hada ido yanayin ya sa ta yanke dariyar cikin mamaki " baby what wrong? meye kuma kake min