← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 108

Sashe 99

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta amsa da Ameen, abubuwan da Aunty Muhsina ta fad'a mata sunyi matukar tasiri a ranta, taji atleast tana so ta gwada dukka shawarwarin.
Mikewa Aunty Muhsina tayi, ta wuce ciki sai gata ta dawo dauke da wasu robobi da wani littafi, ta bud'e jakar Amran ta zura littafin

"Idan kika samu lokaci ki karanta,akwai tips da yawa tun daga farkon auren har zuwa tarbiyyar yara."

"Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi."

"Amin ya Allah."

"Ungo wannan, fara dashi."

Da ido ta kalli robar kamar zatayi magana sai kuma ta karba ta kafa kai, madara ce ashe, amma irin wadda babu mix din komai, madarar ce zallarta, sai data shanye tas sannan ta ajiye, ta sake mika mata wani cup da ta tsiyaya mata a ciki, rabi tasha ta ajiye, ba wai don babu dad'i ba sai don cikin ta ya cika kuma.

"Bari nayi miki parkaging ragowar zaki ji dadin amfani dashi."

"Nagode." Ta fad'a a kunyace

"Baki tambayi mene ne ba, komai tambaya ake baki ji ance matambayi baya Bata ba?"

"Kinsan baure?"

Girgiza kai tayi

"Toh idan kin koma ki saka a nemar miki

*Sassaken Baure
*Kanumfari
*Citta
*Minannas
*Mazarkwaila
Ki dinga dafa su kina sha koyaushe, zaki iya yi da yawa ma ki saka a fridge yafi duk kayan tarkacen nan, sannan ki dimanci shan madara fresh one, sai su dabino kunan Aya, cucumber da zogale kiyi blending kisa madara,farfesu kisha romonki. Sai kuma bangaren gyara ta waje, seatbath da ganyen magarya sannan amfani da misk bayan al'adah kamar yadda yazo a hadith Nana Aysha tana amfani da misk bayan ta gama al'adah tasa a auduga tayi cleansing wajen. Idan kika yi haka sai ki tafasa ganyen magaryar ki kiyi seat bath kamar na minti goma sha biyar shikenan."

"Akwai abubuwa da yawa Amrah, naso tun zuwan ki muka fara, amma yanzu ma Alhamdulillah."

"Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi."

"Amin amin, naji kamar kiran sallah, muyi sallah sai mu dora ko?"

Murmushi tayi, zuciyar ta fes dan komai ta ajiye a kwanyar ta, tana jin dadin sabon karatun da bata sani ba, bata san ma yana existing ba sai yanzu. Suna idar da sallar kiran Sultan ya shigo,yace mata suna waje kawai ya ajiye wayar, ta tashi Anty Muhsina ta rike ta, ta ja hannun ta zuwa wani daki a gidan,

"Gyara fuskarki, ki saka turarurruka gasu nan, bari na saka ya shigo kafin ki gama."

"Toh." Tace ta fita ta barta, ta zauna tana kallon kan mirror dake cike da kaya da kayan kamshi kamar za'a bud'e shago, ta shiga daukar su daya bayan daya tana amfani dasu, sanyin kamshi ne dasu ba mai hayaniya ba, nan da nan dakin ya sake daukar kamshi, ta gyara fuskar ta ta mutsuka powder ta saka lipstick kad'an sannan ta fesa wasu turarurrukan, tana ajiye na karshen Anty Muhsina ta shigo, ta kalle ta tayi murmushi

"Akwai saura amma dai kinyi kokari."

Tissue ta ciro ta bata, tace ta goge lipstick din data saka, sannan ta dauko mata wani romantic jambaki red ta bata, ta saka abinka da fara sai gata tayi wani irin kyau,

"Perfect." Tace sannan tace su je,

Yana zaune rike da cup a hannun sa, kansa da yake sara masa sosai ya dafe da hannu daya, rabin hankalin sa ya tafi akan wayar da sukayi da Daddy dazu, tausayin Mah-Mah da kuma tunanin yadda za'a sanar da Safwan su suka hadu suka tarar masa, gashi yau gaba daya be zauna ba, abubuwan Maimartaba yake ta yi har magriba, so yake su gama komai kafin su bar k'asar, baya jin ya saka wani abu a cikin sa tun safe, sai wannan ruwan bunun da Aunty Muhsina ta bashi da yayi masa dad'i sosai, yaji gaba daya system din cikin sa ya karba, da yana jin wani kabaibai a cikin amma da yasha sai yaji kamar hanjin sa ma ya warware daga dunkulewar da sukayi waje daya.
Labaran da ake nunawa a talabijin ya dan dauki hankalin sa, har be ji fitowar su ba, sai kamshin da yayi ma kofofin hancin sa lale marhaban, da sauri ya waigo, idon sa ya sauka akan fuskar ta, be san sànda ya sakar mata murmushi ba, ta mayar masa tana zama a kujerar dake gefen inda ya zauna.

"Sannu da zuwa." Tace k'asa-kasa tana karantar yanayin sa da ya nuna gajiya sosai.

Da ka ya amsa mata,sannan ya ajiye cup din yana mikewa

"Zamu wuce aunty, angode allah saka da alkhairi."

"Amin Sultan, ka kyauta daka kawo ta,dan kaf kasar nan babu wanda muka shaku kamar maman su, munyi zaman mutunci shiyasa nake jin su kaman yayan ciki na."

"Allah sarki."

"Allah ya baku zaman lafiya, ayi ta hakuri da juna don shine kinshikin zaman lafiya, sannan communication is the key to every successful marriage, ku tattauna matsalar ku, shine zaku samu saukin komai, ayi ta hakuri da kau da kai da addu'a."

"In sha Allah,mun gode k'warai."

"Nice da godia."

Sallama sukayi mata, suka jera har wajen motar inda driver ke jiran su, shi ya bud'e mata ta shiga sannan ya zagaya ya shiga suka tafi. Babu wanda yayi magana a motar, kamar yadda suka tawo dazu haka ma yanzu, ya maida hankalin sa sosai akan wayar hannun sa. Tunanin ta yaya zata fara aiwatar da abubuwan da ta koya yau ta shiga yi, kunya take ji sosai musamman da yanzu ne zata fara ire-iren wadannan abubuwan, amma kuma dole ne ta koya din saboda hakan shine ya dace.
Shahada tayi ta matsa zuwa tsakiyar kujerar, ya dago daga kallon wayar tasa, yayi mata murmushin ya maida kansa ya cigaba da abinda ya keyi, shiru tayi tana jin nauyi amma haka ta daure, ta matsa sosai jikin sa, yana jin ta yayi kamar be san ta matso ba, ta dora kanta a saman kafadarsa.
Kashe hasken wayar taga yayi, ya zura ta cikin aljihu sannan ya saka hannu ya dago kanta, ya juyo baki d'aya yana kurawa fuskarta ido.

"Gani, what did you have for me?"

Shiru tayi kuma, hannun sa ya saka ya dangwali saman lips dinta

"Wannan jambakin yayi kyau, yayi miki kyau."

"Thanks." Tace a gajarce

"Ya yau din? Nayi ta jiran call dinka."

"And baki kirani ba, da sai ki kirani kiji ina wannan bawan Allah ya makale, kila ina chan anyi cefanan kaina ma."

Rufe bakin ta, tayi da sauri

"Allah ma ya rufa asiri."

"Amin ya Allah, misali ne kawai, next time irin haka kikaji shiru call me kinji, ina chan ne wasu harkoki sun rik'e ni, ban ci komai ba Allah sarki ni."

"Ayya Allah sarki, sannu."

"Shikenan?"

"Me?"

"Sannu kawai, nothing for me?"

"Babu komai." Tace tana yarfe hannu

" Ni kamshin nan ne ma, kaman zan zauce, ina kika samo shi?"

"Ba ko ina."
Hancin sa ya dora a saman kanta, ya shaki kamshin sannan ya sauko da fuskar sa zuwa saman wuyan ta, idon sa a rufe ya bata light kiss a wajen, ta ja numfashin ta da sauri jin yadda numfashin sa ke sauka akan wuyanta.

"Ina son kamshi." Yayi maganar yana matso da face dinshi ta wajen bakin ta, kafin tayi magana ya dora lips dinsa a saman nata a nutse.

**©®Hafsat Rano

53 & 54

****
*_kunsan me ake kira da ƘURE ADAKA?_*

_To ba kowa bane illa MAAB LUXURY HOME_

*_Wadanda suke a shirye kuma kullum a tafe wajen kawo muku ingantattun kayan qawata gida masu inganci da kuma kyan gaske_*

*idan matsalarki inda zaki samu kaya 'yan yayi masu inganci to kakarki ta yanke saqa,koda kuwa saqar qarfe ce,saboda zuwan MAAB LUXURY HOME*
_SUN TANADAR MUKU KAYA KAMAR HAKA_
_dinner set_
_serving trays_
_cutlery set_
_jugs_
_foodflask_
_thermoflask_

*kai dama dukkan wani nau'in kaya na qawata gida da maidashi aljannar duniya*
*_hausawa sukace gani ya kori ji,maza garzaya wadan nan shafukan namu don ganewa idanunku irin kayayyakinmu_*

*instagram* https://instagram.com/maabluxuryhome?utm_medium=copy_link

*facebook*:maab luxury home
*website*
http://maabluxury.com

_Ko ka tuntubesu ta lambar waya kamar haka_
+491521 4642007

*suna nan a garin kano,maza taho ayi daku*🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️

***Kai tsaye dakin mahaifiyar ta wadda ta jima da rasuwa ta nufa,ta bud'e dakin ta shiga bata ko bi takan matan gidan ba, burin ta kawai ta kadaita bata kuma son a bata wata shawara ko umarni akan abinda take jin babu me raba ta dashi sai Allah wanda dama shine ya hada su din.
Kwanciyar ta kenan taji an turo kofar data dan rufe ta an shigo, tayi tunanin daya daga cikin matan baban nata ne amma sai taji muryar  Hajiya Umma, ta tashi daka kwanciyar ta zauna ita kuma ta karaso ciki.

"Da gaske dai yara suke da suka ce sun ga shigowar ki, na dauka ma wasa ne wallahi dan dana tambayi su Hajja ma cewa sukayi anya?"

"Ina wuni Ya Umma?"

"Lafiya lou, ya jikin Safwan?"

"Da sauki Alhamdulillah."

"Lafiya kuwa? Akwai matsala dan jiki na ya bani ba kalaou ba."

Kuka ta saka kawai, dama abu da zuciya a kusa, abin na cin ta yana nukurkusar zuciyar ta, shiyasa daga tambaya sai kuka dan tana jin kukan ne kad'ai zai rage mata rad'ad'in da take ji,

"Subhanallahi, lafiya? Me ya faru?"

"Bana jin dad'i ne kawai ya Umma."

"Wannan ba zancen kamawa bane sam sam,ta ya zaki shigo gida ki tawo nan ba tare da kin nemi kowa ba, kuma na tambaye ki matsala ki fashe da kuka, dole dole akwai abinda ya faru, dole ne."

Shiru Mah-Mah tayi, ta yaya ma zata fara furta cewa Safwan ba dan ta bane, ta yaya? Waye ma zai tsaya ya saurareta? Zancen ma gaba daya ba wai wanda zai samu karbuwa bane, musamman kuma tana so ta rufa asirin mijin ta, bata so ta fad'awa duniya abinda ya faru, har su zama labarin da za'a dinga kwatance dashi ba. Ba ma wannan ba, sam yanzu ta dawo daga rakiyar Ya Umman saboda abinda ya faru a baya shiyasa yanzu ma taji tsoron sanar mata kar ta ingizata tayi abinda zai fi nada muni wanda zai jawo ta rasa Safwan din ma baki d'aya.
Chapter 99 · 0% Book details