← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 108

Sashe 14

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

(Mu ajiye wannan zaren, zamu bukace shi nan gaba wajen hade labarin)

***Bata san tsawon lokacin da ta shafe a asibitin ba, kuma tun bayan zuwan su bata sake saka shugabannin nata a idonta ba, baiwa daya ce hade da wani bafade suke kula da ita, duk da bata san me ya faru da ita ba, bata san me akayi mata ba,tana jin wani irin yanayi a tattare da ita, wanda ba zata iya fassara shi ba. Watarana tayi bacci me tsawo, sai ta farka data yabi a gefen ta, tana matsar kwalla, ganin ta farka tayi saurin tasowa wajen ta, tana jera mata sannu...

  ***Gyara zama tayi tana sake jin zafin abinda suka aikatawa marainiyar Allah, tana kuma cigaba da tuno fuskar yan kananan jariran cikin shigar fararen kayan sanyin data zaba musu, ta kuma sanya musu a ranar da suka iso duniya, soyayyar da take musu daban ce, ta bi jini da jijiya ta zagaye ko ina. Yan biyu ne dukka maza, wanda ta kwallafa rai akan su tun ranar da aka sanar musu da abinda yake cikin Aminatu, ta kuma tanadi kalolin gatan da zata yi musu, sai dai tun ba akai ko ina ba, ta rasa wannan babban burin nata, tun daga ranar har yau bata sake samun farin ciki me suna farin ciki ba a rayuwarta, tun ranar da yaran suka iso duniya komai ya lalace musu, komai ya chanja musu ciki harda rasa abu mafi soyuwa a wajen maigidan ta, Mulkin Masarautar Saji. A wannan ranar, a wannan yinin komai ya baci, komai ya zama ba a muhallin sa ba, basu da iko ko hurumin bin ko da gefen masarautar ne, balle akai ga shiga ciki. Ta sani, kuma kowa ma dake da kusanci dasu sun san cewa alhaki ne ke bibiyar su, kuma suna da burin ganin ta kafin su har duniya, ko ba dan yaran ba, ko dan su bata hakuri su kuma samu sassaucin nauyin da ke dauke a wuyan su wanda son zuciya ya kaisu da aikata abinda suka aikata din, amma sai dai ta ina zasu fara neman ta? Bayan tun bayan wannan ranar babu wanda ya kuma jin ko da labarin ta ne.
   Muskutawa tayi kadan tana share hawayen da ya zama abokin ta a kullum, duk sanda tayi irin wannan tuna bayan takan rasa sukunin ta, har sai dai ta zubar da hawaye sannan zata ji dad'i.
   Da daddare ya shigo, ya zauna a falon sannan ya dauki landline ya kirata, sai data dau lokaci sannan ta fito, ta sameshi a zaune yana kallon network news, bata yi magana ba ta zauna gefen sa, ta maida kanta tana kallon gefe, murmushi yayi me ciwo,ya rasa me yasa ta kasa mantawa da komai bayan shi kanshi ba daidai yake ji ba, yana tunanin ma ya fita cutuwa da abinda ya farun. Girgiza kansa kawai yayi, sannan ya shiga yi mata bayani a hankali yana fatan kuma ta fahimta, ko da bata fahimta din ba,yana fatan ya rage mata wani abu kadan daga cikin abinda take ji a ranta.

***Shigowar da Aysha tayi yasa Ammi tayi saurin boye abinda ke hannun, tayi kokarin daidai ta kanta, dan kallon ta Aysha tayi, tasan halin Ammin tasu ko da ta tambaye ta me yake damun ta, ba zata taba fad'a ba, shisa ma kawai sai ta share tayi abinda ya kawo ta dakin ta fita,tana fita Ammin ta tashi ta maida komai yadda yake, ta gyara fuskar ta,ta fito waje domin kammala aikin waken gobe.
   Tana aikin tunanin yana sake dawo mata a cikin kwakwalwar kanta, duk yadda taso ta yakice shi ta kasa, har sai ta ya shafi kuzarin ta, wanda Muhammad na shigowa ya gane bata jin daidai, ya kuma san ba zai rasa nasaba da abinda ya baro dasu daga gida ba, sai dai rashin son ayi maganar yasa basa matsa mata da zancen, da sun ga irin haka basa matsa wa, sai dai suna iyakar kokarin su wajen taimaka mata ta dawo daidai.

***Karar message ne ya shigo wayar ta, ta ajiye rubutun da take ta dauka ta duba, sakon ne kamar ko da yaushe, sai dai na yau ya dauki hankalin ta sosai, sai kawai ta danna kiran number tana fatan samun kowaye suyi magana.
   Safwan na zaune kiran ya shigo, kirjin sa ya buga sosai dan be yi zato ba, kura wa wayar ido yayi kamar me nazari ya kasa dauka har sai da yaji zata katse sannan yayi saurin mika hannun sa, ya daga ya saka a kunnensa. Sallamar ta, ta doki kunnen sa, tabi jini da jijiya ta zagaya ko ina sannan ta dawo saman zuciyar sa. Ya lumshe ido ya bude a hankali sannan yace

"Wa'alaikisalam."

Tsaya wa tsak tunanin ta yayi, jin muryar sa, idan har abinda taji gaskia ne, kenan Ya Safwan ne, dan tayi waya dashi a wayar Ya Adnan farkon zuwan sa, a zuwan zasu gaisa suna kuma gaisawar ta bashi wayar sa tayi tafiyar ta, kenan shine ke turo mata sakonnin kenan tsawon wannan lokacin? Me hakan ke nufi?"

"Amrah, kina jina kuwa?"

Yayi karfin halin cewa yana jin dukkan sauran karfin halin sa na barin sa, da gaske ne da ake cewa wasu mazan basu da liver, liver da zasu iya tsaida mace har su tsarata, da bai yarda ba idan suna tare da abokai ana musun, gani yake ai yana da baki dan haka komai lafiya Lou, sai dai yanzu ya karyata kansa, wani abu me kamar tsoro tsoro ma yake ji yana sake kanannade shi, yana jin kamar ace masa kyet ya ruga a dari, gashi dai damar da yake ta jira ce, amma baya jin yana da confidence din da zai iya.

"Ina ji ya Safwan, ina wuni ya gida ya aiki?"

"Lafiya Lou, ya makaranta, ya kowa da kowa?"

"Alhamdulillah."

Sai sukayi shiru gaba daya, ita tana tunanin abinda zai ce mata da bata fatan hasashen da take ya zama gaskiya,shi kuma yana tsara yadda zai fara,dama zata taimaka masa ta dauko masa zancen messages din da yake mata da ta bud'e masa hanya, amma sai yaji tayi shiru alamun shi take sauraro,

"Umm.. umm, dama toh... Ya karatun?"

Ya samu bakin sa da furtawa bayan ba haka suka tsara shi da zuciyar sa ba, ajiyar zuciya ta sauke dan har ga Allah bata shirya abinda zai ce matan ba, ta amsa da lafiya lou sannan suka sake yin shiru, sai kawai ta kashe kiran gaba d'aya sannan ta kashe wayar ta kwanta rigingine tana kallon saman dakin.

"Damn it!" Yace yana buga hannun sa a jikin fuskar gadon, dama iya dama ya samu amma yayi wasa da ita, haushi ne ya kamashi, haushin kansa da zuciyar sa, ta k'asa fitar da abinda yake cikin ta.

***Daga chan bayan gidan akwai wasu resting chairs guda biyu da d'an karamin table, mafiya yawancin lokuta Abba ke zama a wajen idan yana gida, anan yake zama yayi bitar littafan sa idan zaman Library ya ishe shi. Tun bayan tafiyar sa Amrah ta maida wajen, wajen zaman ta da yamma nan take zuwa ta zauna kusan kullum.
   Yau ma kamar yadda ta saba yi, bayan ta gama taya Umma komai ta dauko wani wani littafi na 200 recipes ta fito ta zauna tana dubawa, ya budo kofar ya tsaya yana dubanta, ta dago suka hada ido ya shiga takowa har ya kawo in da take, sai yayi folding hannayen sa a kirjinsa  yana kallon littafin hannun nata, gaishe shi tayi, ta maida kanta abinda take yi, a zahiri ta bada attention dinta baki daya akan littafin, sai dai a bad'ini ba haka bane, ta kasa kara ko da kalma daya ce akan inda ta tsaya kafin shigowar sa, yana tsaye still a inda yake, tana jin idanun sa akanta, sai dai bata yarda ta dago ma.

"Taimaka min da ruwa please." Taji yace yana zama a daya kujerar, sai a lokacin ta lura da katon littafin dake hañnun sa, ya ajiye saman dan table din, tashi tayi ta ajiye nata littafin ya awajen zaman ta, sannan ta shige cikin gidan, da sauri ya dauki littafin ya bude page din tsakiya ya saka mata dan karamin note sannan ya ajiye. Ruwan ta kawo mishi ta ajiye ta dauki littafin ta, ta shige ciki dan ko giyar wake tasha ba zata iya cigaba da zama dashi a waje guda ba, wajen ma haka so close da babu wata tazara me yawa a tsakanin su, da yasan yadda take ji idan taji alamun tahowar sa wajen da take da be dinga kawo kansa so close haka da ita ba, ji take kamar jijiyar dake taimakawa wajen rarraba jini a sansan jikin ta na tsitsinkewa.
    A saman gado ta ajiye littafin ta jona wayar ta a charge ta rufo dakin, zaman ya fara isar ta haka nan, ta matsu Afrah ta dawo gidan ya dawo kamar yadda yake, so take ma ta dan fita amma ta k'asa, duk sanda zata fitan idan ba makaranta ba sai taji bàzata iya ba dan bata saba ita kad'ai ba.
Chapter 14 · 0% Book details