← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 108

Sashe 62

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata zuciyar ta sake haska mishi. Damke hannayen sa yayi a kirjinsa yana jin zafi Sosai, zafin yadda abubuwan suke kasancewa, me yasa abubuwan ke masa kwan gaba kwan baya ne? Ya riga ya gama gane wani abu guda daya, Mah-Mah ta zama selfish woman, babu abinda ta sani take tunani sai Safwan, ba kuma wai Kawai saboda Safwan din ne take masa abubuwa ba, ya lura kamar harda tsanar sa da tayi a yanzu da kuma rashin son ganin sa da bata yi kusa da ita ko Safwan, tana ganin kamar shine ke kara saka Safwan din a halin da yake ciki.
   Sultan mutum ne me matukar zuciya Amma zai wuya kai tsaye ka gane hakan, ya iya danne zuciyar yabi ka a yadda kake so, musamman idan yana mugun ganin mutuncin ka. Dukkanin su basu taba ganin dayan side din sa ba wanda yayi matukar kokari wajen daidaita kansa , saboda inda ya samu kansa da kuma yadda suka karbe shi, shiyasa yayi ma kansa alkawarin zama a karkashin su da bin dukkanin umarnin su, indai be saba wa Mahaliccin sa ba. Sai dai anzo gabar da ya kamata shima a rayuwar sa ya nuna yasa me yake, ya kuma nuna yana da zuciya a kirjin sa. Kuma shima tsayayyen namiji ne. Allah da kansa ya halarta saki amma baya so. Saboda haka, da ba'a daura ba toh tabbas yayi niyyar barma Safwan, amma tunda haka ta faru ba zai zama me butulce ma Allah ba.
  Taku daya yayi ya isa gaban gadon, kallon sa yayi kad'an sannan a hankali yace

"I'm sorry Safwan, I'm so Sorry."

Sai ya juya cikin wani irin taku da be san yana dashi ba, ya fice daga dakin, ya kuma bi ta hanyar da yasan akwai karancin mutane ya bi fice gaba d'aya daga gidan.

***A hankali ta d'aga idon ta, ta kalli matar da suke tare tsawon lokacin nan, ta kuma kalli kofar taga masu tsaron nasu sun dan matsa daga wajen saboda rana. Sai ta dan matsa k'adan jikin ta, ta tallafi kanta ta dora a saman kafarta, sosai take cikin wahala bata komai sai fitar da numfarfashi.

"Zaki iya sanar dani dalilin da yasa kike cikin wajen nan?"

Cikin muryar da kana ji kasan tana jin jiki tace

"Zan iya, ko da hakan na nufin katsewar numfashi na."

"Ina sauraron ki..."

"Sunana Aminatu, ina daya daga cikin hadiman gidan nan a tun zamanin adalin sarki, Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji."

"Aminatu, Kece dama? Duk zaman nan da mukayi tare amma ban taba gane ki ba? Dama tsawon wannan lokacin kina cikin wajen nan, amma babu wanda ya sani?"

"Ina nan tun ranar da abin nan ya faru, tun ranar ko hasken rana basu barni na sake gani ba, me yasa hakan ta faru dani? Me yasa suka kashe min rayuwa tah?"

"Zaki iya bani labarin abinda ya faru?"

"Eh zan iya."

"Madallah." Tace tana gyara mata zaman kan nata.

"Watanni goma sha takwas na dauka ina goyon ciki, cikin da aka saka min shi ba tare da izini na ba, saboda bani da galihu,bani da wanda zai ce dan me, nasha bakar wuya matuka, wanda sai da aka saka min sau uku yana zubewa sannan aka samu ya zauna. Tun ranar da na bar Masarautar ban kuma shigo ta ba, ina chan garin na Lagos inda muke zaune a wani babban gida ni da Yabi da masu yi mana aiki, sai masu duba lafiya ta mutum biyu nurses sai likitan da yake zuwa ko yaushe ya duba ni."

"Cikin hukuncin Allah, na haihu lafiyw, na haifi yara maza biyu tagwaye, girma da lafiyar su ya bawa duk mutanen da muke tare dasu mamaki, sai dai bayan zuwan su duniya da mintunan da basu gaza talatin ba, suka dira a garin bisa umarnin maidakin sarki, su biyu ne, sai dai mutum daya na gane, Babbar amintacciyar baiwar Gimbiya, suna zuwa suka ce an umarce su ne da tafiya da yaran. Hankali na ya tashi,na hau kuka sosai ina rokon su da su bar min yaran duk kuwa da nasan dama za'a yi haka, tun kafin suzo duniya Gimbiya ta fad'a min abinda zai faru duk ranar da suka zo duniya. Sai dai ba abu bane me sauki raba ni da yaran, wanda ban taba sanin ina son su ba sai bayan da suka iso duniya, naji zan iya yin komai akan a bar min su. Na dinga rokon su akan dan Allah karsu tafi dasu, suka nuna min dole ne su tafi dasu saboda umarni ne da basu isa su ketare ba. Ina ji Ina gani suka tafi da yaran. Nayi kuka sosai har sai da naji kamar ido na zai fita daga gurbin sa. A k'asa na durkusa ina kuka sosai, sai na lura da alamun takalma a tsaye a gabana, na daga ido na da sauri. Yana tsaye a gabana, banji shigowar sa ba, ko dan halin da nake ciki ne? Ya karasa matsowa ya tsuguna a gabana yana bina da kallo

"Kina kukan rabuwa da yaran ne?"

Yace yana kallon cikin ido na, da sauri na daga masa kai ina jan numfashi

"Tashi tsaye." Yace min yana matsawa baya. Tashi nayi ya mika min wani k'yalli

"Share hawayen ki."

Karba nayi na share sai dai basu daina zuba ba hawayen. Da hannu yayi wata alama sai gasu sun shigo, Maza ne manya majiya karfi, suka rissina a gaban sa.

"Ku wuce da ita da kakarta, zan biyo bayanku."

"Toh." Suka had'a baki sannan suka umarce ni akan na wuce muje, nabi su ina tunanin inda zasu kai ni, ciki muka fara komawa suka tisa mu a gaba ni da Yabi sai filin jirgi, karo na biyu da na sake dawowa tun bayan zuwa na garin. Bayan kamar awa d'aya jirgin mu ya d'aga.
   Tun daga farkon hanyar da zata kaika Masarautar zuwa karshen ta, mutane ne suke ta tururuwar isa Masarautar wadda alamu suka nuna gagarumin abu ne yake faruwa a Masarautar. Hannun Yabi na kama da naji itama ashe rawa duk kuwa da mu a mota muke mutanen kuwa a k'asa suke. Muna zuwa kofar Masarautar muka ganta a rufe sai dai akwai tsaro sosai dan yadda wajen ya cika mutane na ta hayaniya. Lekawa wanda ke gaban motar mu yayi, suna ganin shi suka yi saurin bud'e kofar, motar ta kutsa kai cikin Masarautar. Bamu tsaya ko ina ba sai gaban fad'ar, fad'ar Maimartaba Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji, sai muka ga ashe cikar da akayi a wajen ma kad'an ce akan ta ciki.

"Ku fito." Yace mana bayan ya daidaita motar a waje daya, na sake kankame hannun Yabi dan yadda nake jin kamar zan fadi saboda jiri muka fito, duk sai hankalin mutane suka koma kanmu, kamar sun ga wani abun mamaki. Kai tsaye cikin fad'ar aka umarce mu da shiga. Daga nesa na hango wani kamar Maimartaba a k'asa kansa a duk'e,sai wadda ko tantama banayi Gimbiya ce a gefen sa, tana kuka sosai sai dai babu wanda ke kallon ma inda take. Kaina ya sake kwancewa ganin wani daban akan gararar Sarkin, wanin da ba kowa bane sai dan uwan Sarkin da duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda shakuwa me karfi ke tsakanin sa da Sarkin, dan babu yadda za'a yi Sarki yayi wani abu ba tare da sanin sa ba. Gefe muka samu muka rakube, karo na farko da muka samu kanmu a irin wannan wajen da ke ciki da manyan mutanen Masarautar wanda da tsakanin mu dasu sai dai hange daga nesa.

"Masha Allah, gasu ma sun karaso." Wani da yake tsaye ta gefen Sabon sarkin yace, duk suka maida kallon su kanmu.

"Taso." Wani ya bani umarni, ban iya tashi ba sai jan kafa da nayi na isa gaban su, na dukar na kai na saboda yadda kwarjinin su ya cika wajen.

"Wannan itace yarinyar da sukayi amfani wajen cimma burin su,kuma itace ta haifi yaran nan guda biyu da suka dauko suka nuna wa kowa a matsayin yaran da gimbiya ta haifa, gata nan sai kuji daga bakin ta."

Wani da ya kasance babba a cikin yan majalisar Sarki yace

"Baiwar Allah muna son jin me ya faru."

"Karki ji tsoron komai, kiyi bayani babu wanda zai miki komai anan."

Wani ya dora akan abinda dayan yace. Ba tare da dogon tunani ba na shiga basu labarin komai, wanda sai bayan na sanar musu da komai sannan na fuskanci duk abinda yake faruwa, sannan na fuskanci gadar zare aka shirya ma Sarki da gimbiya. Bayan jin bayani na, mutane suka yi ta girgiza kai wanda ina kallon lokacin da Sarkin ya girgixa kansa yana jin kamar k'asa ta zage ya shige.
   Sai dai ashe duk abin nan ba wai ainihin abinda ya faru bane, ba wai ainihin maganar da aka fara ba kenan, kawai sunyi amfani da magana ta ne wajen sake tabbatar da abinda suke son tabbatarwa dumbin al'ummar Masarautar Saji.
   Mutane ne wanda a kalla zasu kai su goma aka bawa umarnin shigowa cikin fad'ar, dukkanin su kallo daya zakayi musu kasan suna cikin tashin hankali, na farko ne ya fara magana.

"Tsawon shekara guda kenan da kashe min dan uwana, kuma ba kowa bane sai Maimartaba Sarki Usman."

Da sauri Sarki Usman ya dago kansa, mamakin maganar mutumin da be taba gani ba ya shige shi, shi da tun da ya fara mulki be taba salwantar da ran ko da kiyashi bane, balle mutum sukutun da guda? Amma ba wannan ba ne zai baki mamaki, sai yadda dukkan mutanen nan suka kawo kwakkwarar hujjar da har yanzu ni kaina na k'asa gane yadda akayi hakan ta faru, idan dai zaka duba karfin hujjar da suka kawo ne to tabbas babu wanda ba zai bawa Maimartaba laifin ba, amma kuma anya zai aikata haka? Anya zai iya kashe mutum akan haihuwa? Ko da sun aikata min zalunci mafi muni duk akan haihuwar amma ban yarda da Maimartaba zai iya aikata hakan ba."

"Menene Hujjar da suka yi Amfani da ita akan Maimartaba?"
Chapter 62 · 0% Book details