Sashe 80
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Alhamdulillah!" Suka had'a baki wajen fad'a, Dr Labaran ya mika ma Dr Ahmad din hannu sannan yace
"Kaga ikon Allah ko Dr?"
"Wallahi, alhamdulillah."
Dr Osas da yake ta wajen Sultan ya juyo
"Dr Sultan ma ya samu kansa, but nayi masa allurar bacci saboda yadda jinin sa yayi mugun hawa, tunanin mun rasa dan uwan nasa da gaske yasa na masa allurar kar muje sad news din yayi breaking dinsa, sai gashi kuma ya samu numfashin ya dawo."
"Hakan da kayi daidai ne Dr." Dr Labaran yayi saluting dinsa yana murmushi.
"Thanks Sir."
Fitowa sukayi suka bar Dr Bash a ciki da yake sake examining Safwan din, abu daya zasu jira yanzu shine farkowar which basu san yaushe ba, zai iya daukar lokaci sosai, amma suna fatan ya tashi din.
Wucewa Dr Ahmad sukayi Dr Labaran kuma ya tsaya a inda su Daddy suke, Abba yayi karfin halin cewa
"Dr yaushe za'a bamu shi mu tafi dashi?"
"Ina za'a tafi dashi? Ko zaku chanja masa asibtii ne?"
Kallon juna sukayi, Daddy ya matso da sauri
"Dama wai gawar tasa..."
Katse su Dr Labaran yayi da sauri
"Ai be mutu ba, da ransa dogon suma yayi kuma yanzu an samu ma numfashin sa ya dawo daidai, duk da he's still unconscious amma ana saka ran farkawar sa ko zuwa nan da 3days ne."
Da sauri Mah-Mah ta taso, ta rufe bakin ta da mayafin ta tana dariya hade da kuka
"Da gaske kake Dr? Da gaske?"
"Baa wasa da mutuwa ai Hajiya."
"Alhamdulillah ya Allah."
"Sai dai an kara samun sabon patient, Dr Sultan ma an bashi gwada, tunanin ko Safwan din ya rasa ransa ya saka Sultan din faduwar data saka shi suma a take, gaskiya soyayyar da yake ma dan uwansa ba karama bace, ki gode wa Allah Hajiya, Allah ya had'a miki kan su, kuma tabbas kin yi kokarin basu tarbiyya me kyau."
Sai ya juya ya tafi, shiru Mah-Mah tayi, karo na farko tun Bayan abubuwan da suka faru taji abinda tayi wa Sultan bata kyauta ba, bata kyauta ba yadda akayi idon ta ya rufe ta manta waye ma Sultan din, yaron da ta raina da hannun ta, shi din kamar Safwan ne, tarbiyyar ta ce, ita ya sani a matsayin uwa har kuma gobe yana mata kallon uwa, soyayyar da yake wa Safwan din zata iya cewa tafi wanda shi safwan din yake masa, shi yake kula da dukkan al'amarin Safwan din tun suna kanana, har suka girma be taba gajiya ba, ya kan hakura da komai na jin dadi in dai Safwan zai samu farin ciki, ya akayi ta manta wannan? Har tayi masa abinda har ta mutu ba zata daina jin kunya ba, d'a na kowa ne, kuma baka san wanda zai taimake ka ba, baka san waye Alkhairin ka ke tare dashi ba, ya akayi ta biye wA sharrin zuciya har ta kasa ganin daidai da aikata daidai? Ta manta da cewa da haihuwa da mutuwa da aure duk lokaci ne,idan lokacin yayi dole ayi, ta manta da fad'ar nan ta hausawa dake cewa Matar mutum kabarin sa, babu kuma wanda zai auri matar wani. Duk ina ilimin ta yake? Ina sanin ya kamatan ta ya tafi da har ta yarda da rudin zuciya.
Ko da ta shiga dakin da suke a kwance, sai ta tsaya chak ta rasa wajen wanda zata je, ta cigaba da kallon su cike da tausayawa, dukkan su a dalilin dayan su suka shiga halin da suke ciki a yanzu.
Matsawa tayi gaban gadon Sultan din, ta dafa kansa ta yi masa addu'a, har lokacin idon ta na zubda hawaye, tana jin dana sani da tausayin Sultan din. Sai data tsaya a wajen sosai tana tuna abubuwa da yawa sannan ta nufi gadon Safwan din, shima tayi masa addu'a kamar yadda tayi wa Sultan sannan ta fita. Ita kad'ai ta shiga ta gansu shima saboda tausayin ta da Dr Labaran yaji yasa yace ta shiga din dan shi duk a tunanin sa duk su biyun yayan ta ne, yasan dole ta damu ta shiga tashin hankali saboda yasan yadda uwa take son yayanta.
***Tun da suka isa asibitin sai Muhammad ya tsaya wajen yan sandan nan ya basu dukkan bayanan da suke bukata sannan suka rakashi har gida, yana zaune yana tunanin ya kamata ya koma asibitin ya duba jikin su Aysha ta leko tana kiran sa.
"Ya Muhammad!"
"Ya akayi?"
"Yanzu Baba Altine ta zo take cewa wai yan sanda sunje gidan Alhaji zasu tafi dashi amma wai baya kasar, kowa yayi mamakin zuwan yan sandan amma babu wanda yasan dalili."
"Owk." Yace yana juyawa, yasan dalilin zuwan nasu ya kuma san Madakin ba zai zauna ba, tunda aka kama yaron sa daya ya tabbatar da zai shiga hannu shima, ga bayanan da ya bayar da kuma abinda suma su Sultan din zasu bayar a had'a, shi be damu ba, burin sa kawai Ammi ta dawo, tunda yasan idan aka kama Madakin zai fad'a musu inda ya kai musu mahaifiya.
"Baka ce komai ba yaya?"
"Me zance Aysha? Kawai aiki ne ya biyo ta kansa."
"Idan suka tafi dashi Ammi fa? Yaushe zata dawo ita?" Idon ta yayi raurau zatayi kuka.
"Addu'a!"
Juyawa tayi ta fita, tasan halin Muhammad din sarai, sai tace ma bata taba ganin miskili irin sa ba, idan baya jin magana toh sai ya wuni ko k'ala be ce ba, duk kuwa da ita yana ma sakar mata suyi hira amma idan yan abun suka motsa sai yayi mata mirsisi, sanin cewa ba zai ce komai din ba yanzu yasa ta hakura ta barshi.
***Sun cika dakin sosai yan uwa da abokan arziki, Amrah na zaune tana kallon kowa, hankalin ta rabi ya tafi kan halin da Sultan take tun bayan da labarin abinda ya faru ya bazu, so take ta tambaya ko akwai wanda ya san ya ake ciki amma ta rasa wanda zata tambaya, musamman tun zuwan hajiya da maganganun da ta farfada tun bata ma san dalilin da ya saka akayi kidnapping Amrah din ba, sai kawai taja bakin ta, ta tsuke tayi masa adduar samun sauki da shi da Safwan din dukka.
Tun bayan azahar Sultan ya tashi, kafin ya gama bud'e idon sa ma Dr Osas ya sanar dashi condition din Safwan din da abinda ya zata da kuma abinda ya faru, hakan yasa ya mike da kwarin sa,duk da kansa na masa ciwo har lokacin amma labarin da ya samu ya saka shi raguwa zuwa kaso mafi yawa. Shi kad'ai ne a dakin Safwan na dakin sa daban, tashi yayi da k'yar Adnan ya taimaka masa ya shiga yayi alwala yazo ya rama sallolin dake kansa, sannan ya bukaci ganin Safwan din, babu wanda ya hanashi, haka suka fito shi da Adnan da zai raka shi, a hankali yake tafiyar saboda yadda yake jin iska na kad'a shi kamar zai fad'i, ya iske su Mah-Mah a waje suna zaune da wasu mata da be tsaya tantance su waye ba, ya wuce su kawai ya tura kofar dakin, a yadda ya ke tun bayan zuwan su asibitin haka yake still sai dai yanzu da banbanci da dazu, yanzu akwai alamun nutsuwa a baccin da yake yi, ya dade a tsaye, yana duba file din da bayanan dake jiki kafin ya ajiye, ya gyara masa kwanciyar sa ya fito.
"Sultan be ganmu bane?" Ya Umma tayi maganar tana kallon Mah-Mah
"Ba lallai idan ya lura damu ba, shima yana bukatar hutu don shima ba lafiyar ce dashi ba."
"Toh me kuma ya sameshi? Bayan shine ya jawo komai."
"Dan Allah Ya Umma mu bar maganar nan, yanzu ba lokacin ta bane wani lokacin."
Da mamaki Ya Umman ta kalle ta, ganin ta dauke kai yasa ta tabe baki tayi shiru tana tunanin abinda ya hau kan Mah-Mahn.