← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 108

Sashe 86

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Gidan sa ya sake komawa, ya duba abubuwan da za'a bukata a gidan, ya duba dakin da yake son ajiye su Maman Yara, ya sake fita ya siyo duk abinda za'a bukata saboda yana so a sallame su har da Amrah ma, Safwan kad'ai za'a bari shima saboda wasu abubuwan da dole a asibitin ne za'a same su. Sai da ya tabbatar da ya gama hada komai na bukata a gidan, sannan ya koma asibitin, lokacin daf da magriba ne, Sallah ya tsaya ya fa rayi sannan ya shiga cikin asibitin. Da mayyar sa ya fara cin karo, dauke da basket da Mah-Mah ta bata ta kai dakin da Amrah take, yayi saurin dauke kai amma ta ganshi, dole ya tsaya suka gaisa ta nuna masa kayan hannun ta, jinjina kai kawai yayi be ce komai ba, yana tunanin ko Mah-Mah ta chanja ne? Dan ya ga chanji sosai a tare da ita, rashin maida hankali akai ya saka be gane hakan ba sai yanzu. Wucewa yayi dan so yake a sallame su a ranar duk da ka'idar asibitin ne ba'a sallama da irin lokacin amma tunda su ne masu sallamar zasu iya yi a duk sanda suka so. Dr Osas ya samu sukayi magana, yace ba komai tunda shi ma doc ne sai ya karasa kula dasu. Tare suka fito suka je su duba su Maman Yara, ganin ta a kwance rigis ya saka Sultan din cikin damuwa,Amma da ta ce masa babu komai sai ya kyale ta, suka sake yiwa Aminatu binciken da ya kamata sannan aka sallame ta. Gidan ya wuce kai tsaye, ya kaisu ya nuna musu daki da komai da zasu nema sannan ya sake komawa asibitin.

Sosai jikin Safwan yayi kyau dan har yana iya zama yayi wasu mintunan, har ma yayi hira duk da ba doguwar hira yake ba amma alhamdulillah, yanzu ma yana zaune amma a kishingid'e, Mah-Mah ce kawai dashi a dakin kowa ya tafi sai Umaima da ta aika ta kaiwa Amrah abinci wanda kullum take aika musu. Shigowar sultan ya saka Safwan din yin murmushi, ya tsuguna ya gaida Mah-Mah kamar yadda ya saba, ta amsa a sake ba tare da wani abu a cikin muryar ta ta ba, wajen Safwan ya nuna, ya bashi hannu yana me jin dadin yadda ya samu sauki sosai

"Yau ina ka shiga ne naji ka shiru?"

"Na shigo kana bacci, ya jikin naka?"

"Alhamdulillah! Sai godiyar Allah."

"Alhamdulillah, toh Allah ya kara sauki, akwai wajen ke maka ciwo ko babu dad'i haka?"

"Babu gaskia, alhamdulillah sai dan abinda ba zaa rasa ba."

"Toh ko..."

"Sultan." Mah-Mah ta kira sunan sa, ya fasa maganar da yake

"Na'am Mah-Mah?"

"Kayi hakuri dan Allah, duk abubuwan da nayi maka a baya wallahi sharrin zuciya da shaid'an ne, kayi hakuri."

"Iyaye basa taba dukan dansu dan basa sonshi, sai don su gyara shi, haka uwa babu abinda tafi so sama da yayanta, amma hakan me hana ta hukunta su ba idan sukayi ba daidai ba, wannan shine soyayyar gaskiya, idan kayi abu mara kyau a nuna maka laifin ka. Ni baki mun komai ba Mah-Mah, domin ke din uwa ce har gobe, bana kallon ki da wata siga ta daban bayan wadda nake kallon ki tun farko."

"Nagode Sultan, wallahi nima haka ne a wajena, bansan me ya hau kaina ba, dan Allah kayi hakuri ka kuma daina fushi akan maganar da nayi maka ta karshe, ka dawo gida mu cigaba da rayuwar mu kamar da."

"Subhanallahi...Idan har zan iya fushi dake Mah-Mah, toh tabbas banyi amfani da kyakkyawar tarbiyyar da kika bamu ba."

"Sultan... Nagode." Tace tana sauke kanta k'asa, saboda yadda kunya ta hana ta dagawa ma ta kalle shi, toh ai bata da ma idon da zata iya kallon nasa

"Allah yayi maka albarka, ya albarkaci auren nan, ya baku zaman lafiya da zuri'ah dayyiba."

"Amin." Ya amsa a chan k'asan makoshin shi, Safwan da yayi shiru tun da suka fara maganar sai murmushi kawai yake ya amsa da "Amin ya Allah." Hararar sa Sultan yayi sukayi dariya a tare

"Yaushe zaka sallame ni ne dactora?"

"Sai ka kara sati uku haka naga yanayin naka."

"Rufa min asiri wallahi bazan iya ba tab!"

"Haka ko zaka hakura, tunda nine me cewa."

"Aikuwa dai, idan yayi biyayya toh." Mah-Mah ta shiga zancen tana jin wani irin farin ciki, kwatankwacin wanda take ji idan suna irin wannan rahar tasu kafin ta dauki hudubar shaid'an.

"Nabi wallahi, nayi biyayya Ranka ya dade, Allah yaja da kwanan ka." Yayi maganar yana dungule hannu, kallon sa Sultan yayi tunanin sa na turawa zuwa Masarautar Saji, ko yaya suke ciki tsakanin UBA da DAN da yake shirin waiwaya dan da lokaci kadaan? Yanzu ba tasu yake ba shiyasa ma ya share ko ta kansu be sake bibiya ba. Yanzu tunanin yadda zai isa ga iyayen sa kawai yake, ba kuma zai je shi kad'ai ba sai tare da yan uwan sa in Sha Allah. Tunanin yan uwan sa da ya shigo ne ya saka ya tuna hoton da Madaki ya nuna masa, yayi saurin girgixa kansa,

"Ba zai yiwu ba kawai so yake yayi wasa da tunanina." Yayi maganar a zuciyar sa. Sallamar da Daddy yayi a kofar ya saka shi kallon kofar da sauri, ya kafe shi da ido yana son alakanta abinda Madakin yake nufi da kuma fuskar Daddy da babu komai sai kamala da dattako data nuna. Ya sake girgiza kansa ya karo na biyu, sai kuma ya tuna da maganar Safwan

_"Na taba ganin sunan a jikin wasu takardun Daddy."_

"Ya Allah." Ya furta a hankali ya shafi kansa

"Sultan." Ya tsinkayi muryar Daddy akan sa, da sauri yace

"Barka da shigowa Daddy."

"Tunanin me kake haka kai kuwa, akwai matsala ne?"

"A ah babu komai." Yace yana kokarin tura maganar Madakin zuwa chan bayan kansa, dan ko kusa be hango yiwuwar hakan ba, akwai ta inda aka samu matsala dai dole, ko dai Madaki yana so ya bata masa tunani ne, ko kuma an samu misunderstanding. Cigaba sukayi da tattaunawa da Daddy har lokaci yaja sosai, sai ya tuna da sallamar Amrah da yake so yayi, amma yana son ya fara yi mata bayanin su Maman Yara ba sai taje gidan kawai ta gansu ba. Duba agogon hannun sa yayi, ya ga har lokaci yaja sosai, yasan zuwa lokacin Umma ta koma gida tunda Afrah ce take kwana yanzu. Kai tsaye ya wuce chan din.

Tun da ta kai abincin me makon ta tafi sai ta samu kujera ta hakimce, ta ciro wayar ta tana daddanawa kamar me yin chat, lokaci zuwa lokaci tana sakin yar karamar dariya alamar chatting yayi dadi, babu wanda ya tanka mata a cikin su. Sai dai Amrah ta kasa dauke tunanin ta daga kanta, sai ta fara tunanin toh ko da SULTAN suke chatting din? Duk sai taji babu dad'i taji tana jin haushi sosai. Ko da ya shigo dakin, sai ta daure fuskar ta, ya kalle ta da sauri yaga ta dauke kai, ya juya ya kalli Umaima da shigowar shi ya sakata daina abinda take ta washe bakin ta.

"Ya Sultan..."

"Ya Sultan sannu da zuwa." Afrah ta fad'a tana aika mata da kallon banza, maimakon ya amsa na Afrah sai ya fara amsa kiran Umaiman

"Ashe kina nan?"

"Ina nan wallahi." Tace tana kankance idanun ta

"Afrah ya garin? Ya me jiki?"

"Da sauki." Ta amsa a chunkushe tana jin haushin yadda ya bawa Umaiman attention, tashi tayi zata fita tace

"Malama ki basu waje."

"A ah ta zauna..."

"Umaimah dan jira ni pls na gaisa da Madam two mint."

Far tayi da idonta, ta sake gyara zaman ta tana kallon fuskar Afrah da ta ji wani abu ya soke ta, tayi saurin ficewa tana bugo kofar.

Takawa yayi ya isa gaban gadon, ta ji kwalla na taho mata tayi saurin maida ta, ya lura da sanda ta maida kwallar, yayi wani kasaitaccen murmushi, ya rankwafo kanta, karfen dake jikin zip din gaban rigar ta ya makale a jikin tasa rigar, hakan ya kara basu kusanci, kokarin yadda zata cire karfen ta hau yi yayi saurin rike hannun ta, a hankali ya rada mata

"Stay still... Wani abu nake son koya miki."

"Ya jikin naki?" Ya tambaya yana dora saman goshin sa akan nata,daga idon ta tayi sama, tana kallon sa tana son gane abinda yasa yace ta tsaya.

"Idonki fari tas,I like it,nooo I love it zance." Murmushi tayi ta rufe idon, ya kalli saman idon nata da suke rufe ya bata light kiss a wajen...

"Ina son mace me kunya, me aji me class..." Ya dora

"Ba ballaga ba, wadda bata san me yake mata ciwo ba, komai classy yafi, just like you Amrahhh..." Yaja sunan yana fitar da siririn murmushi

"Garam...." Aka buga kofar, garin dagowa suka buge da kai kowa ya dafe nasa

"Ouch..." Suka fad'a a tare

"Ka fasa min ciwo na."

"Kin fasa min kaina dai, wayyo Allah."

"Akan ciwo na fa ka fasa min." Tace tana kokarin yin kuka.

"Kadanba ni kika kusa fasawa ba, karki yiwa bayin Allah asara wallahi."

Hawayen da tun dazu take rikewa suka zuba, yasa hannu ya goge mata yana girgiza mata kai

"Kina yin kuka shikenan taga lagon ki, kinyi na farko Afrah ta fada min, wannan ya zama last, shiyasa na hana ta fita saboda na nuna miki abinda ya kamata kiyi,I'm all yours, karki yarda ta saka miki wani tunani a ranki, babu komai tsakani na da ita, bayan alakar dake tsakanin Mah-Mah da Anty Amina, so please karki damu kanki kinga ba dad'i kike ji ba."

Wata matsananciyar kunyar ce ta kama ta,tasa tafin hannun ta, ta rufe fuskar ta da sauri. Dariya ya shiga yi mata yana tsokanar ta mai kishi, mai kishi. Kin kulashi tayi, taki kuma dago kan tana jin kamar k'asa ta tsage ta shige, wato Afrah munafuka shine ta fad'a masa tayi kuka, zata kama ta ne wallahi. Wayar ta dake kusa dashi tayi haske, ya saka hannu ya dauka ya shiga karantawa a fili
Chapter 86 · 0% Book details