← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 108

Sashe 89

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shikenan ina zuwa." Nayi gaba na koma wajen da na bar safiya na karbi jinjirin guda daya nace mata ina zuwa, na juyo na kawo masa, ya tashi da sauri ya miko hannu, ban bashi ba nace ya fara cika alkawari, motar sa muka nufa ya ciro cheque ya rubuta min kudade masu yawan gaske, ya bani, sannan yace yana bukatar muyi yarjejeniya a rubuce akan ba zan dawo daga baya nace ya bani yaron ba domin yana so idan matar sa ta farka ya bata shi a matsayin wanda suka haifa,na yarda mukayi ya saka hannu nima na saka sannan ya karbi yaron ni kuma na karbi cheque din na juya na tafi."_

Dafa bangon wajen Sultan yayi jin zai fad'i da gaske

_"Safiyanu Madaki! Na taba ganin sunan a wasu takardun Daddy."_

Sultan yaji maganar Safwan na amsa kuwwa a kunnensa

_"Yanà da ciwon zuciya_" zuciyar sa ta sake fad'a masa, runtse idon sa yayi yana hango kalar tashin hankalin da mutane da yawa zasu shiga idan har wannan labarin ya fito, me zaiyi? Farin cikin samun Safwan a matsayin dan uwan sa na jini ko kuma tunanin yadda Safwan, Mah-Mah da sauran mutane zasu ji idan har maganar ta fita, tabbas dole ne komai ya bayyana, idan ya rufa ya bar maganar yana ganin kamar be wa mutane hudu adalci ba, Maimartaba, Gimbiya, Aminatu da kuma Safiya. Gefe daya kuma idan ya tuna kalar tashin hankalin da Mah-Mah zata shiga sai yaji wani irin weakness, me ya kamata yayi?

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun." Kawai yayi ta maimaita dan beyi tunanin labarin zai juye ya zama haka ba.© Hafsat Rano
Page 47

***"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun."

Kawai yayi ta maimaita dan beyi tunanin labarin zai juye ya zama haka ba.
  Juyawa yayi ya fice da sauri be jira Madakin ya gama ba, ya iske Daddy a tsaye yana jiran fitowar sa, daga ganin yanayin fuskar sa akwai firgici musamman ganin Sultan din ya dad'e a ciki.

"Me yace maka?" Daddy ya tambaya da sauri, girgiza kai kawai Sultan yayi zai yi magana Farouk D ya fito.

"Dr akwai wasu bincike da mukayi inda muka gano wasu harkoki da yake yi wanda basu dace ba, toh dai muna cigaba da bincike duk abinda muka samu zamuyi aiki akai.

"Nagode sosai oga, kuyi aikinku babu matsala."

Sai ya mika masa hannu

"Bari mu wuce, thank you very much."

"Babu damuwa."

"Baba agaida gida." Ya dan rissina yana kallon Daddy.

Har suka isa mota suka shiga Sultan yaki yarda su had'a ido da Daddy da ya gama karantar sa tsaf yasan kuma ya samu wani information akan labarin. Sai da ya bari ya tada motar suka hau titi sosai sannan yace

"Sultan bani da zabi ne a lokacin, ka saka kanka a matsayin halin da nake ciki a lokacin, ina tunanin ba kowa ne zai ketare ba, bayan haka ban san dalilin da Allah ya kawo Safwan cikin rayuwar mu ba, may be kaddarar shigowar sa ita tasa yaron mu ya rasu, idan naki karba kamar nayi butulce ne." Sai ya dora

"Sannan Sultan kai kanka ka sani, zaman Safwan a wajen mutum irin Madaki,da tuni rayuwar sa ta lalace, ina ganin hakan da nayi shine kawai mafita garemu dukka. Duk da babu ranar da zata fito ta fadi banji a raina cewa irin wannan ranar na zuwa ba, sai dai tsoro na daya ne, halin da mamanku zata shiga da kuma halin da Safwan zai shiga, ga lalurar sa, idan na tuna wannan sai naji duk na rasa inda zan saka raina naji dad'i, ya zanyi idan na zama sanadiyar tarwatsewar rayuwar mutanen da nayi iyakar kokari wajen kare wa, ta yaya zan fara sanar da su wannan labarin? Ta yaya Sultan?"

Shiru Sultan din yayi be tanka ba, kansa yana kallon titi yana jin sanda kwalla ta taru a idon sa, me zai ce ne wai?kamar Daddy ya san me yake tunani a ransa sai ji yayi yace

"Kace wani abu dan Allah sultan,kace banyi son zuciya ba wajen abinda na aikata sai son kare rayuwar su, idan kace nayi ha'inci ko zalunci hakika ba zan taba yafewa kai na ba."

"Bakayi ba Daddy, bakiyi ba, kai uba ne irin wanda kowanne d'a zai yi farin cikin samu, kuma tabbas kaddara ce me karfin gaske ta shigo da mu cikin rayuwar ku, kuka kuma karbe mu hannu biyu ba tare da kun gaza ba... Sai dai."

Sai yayi shiru, yana tunanin ta yaya ma zai iya cewa Daddy kuskuren sa daya rashin sanar da Mah-Mah da Safwan din,bai san da wanne kalar magana zai yi amfani ba,duk wadda ya kamo sai ta goce ko kuma yaga bata yi daidai da abinda d'a ya kamata ya fad'a wa wanda yake ma kallon mahaifi ba a matsayin gyara, yanayin yadda yake ta kokawa da zuciyar sa wajen hado kalmomin ya saka daddy cewa

"Sai dai nayi kuskuren rashin sanar dasu Sultan, nayi kuskure sosai, idan babu komai ai akwai halin mutuwa ko?"

"Tsoron abinda zai faru ya saka na bar Abin a cikin zuciya ta, na binne shi nayi kokarin karbar kaddara ta da hannu bibiyu, idan na kalli tsantsar kaunar da ke tsakanin Safwan da Maman ku sai naji bani da sauran damuwa, nasan babu wanda yasan abinda ya faru saboda haka bani da fargabar wataran wannan farin cikin da nake gani a tare dasu zai kau, sai gashi cikin rashin sani, Allah Hakeem ya sake kawo ka cikin rayuwar mu, ba tare da sanin alakar dake tsakani ba, lallai wannan shine kaddarar da ake cewa bawa baya ketare mata,yanzu ya mahaifanku suke ji rashin ku tsawon wannan lokacin, 'yaya uku ba daya ba, wannan wane irin zalunci ne,tabbas mutane basa tsoron Allah basa tunanin mutuwa da hisabi, da ana tuna za'a mutu da abubuwa da yawa ba'a aikata ba Sultan."

"Idan na hanaka sada Safwan da iyayenku ban musu adalci ba, na kuma so kaina ainun, saboda haka na baka dama Sultan, na baka dama kayi duk abinda ya dace, ina rokon Allah ya duba niyyata da zuciya ta ya kawo min komai cikin sauki."

"Amin Daddy, in Sha Allah komai zai warware cikin sauki, da nayi niyyar had'a tafiyar tare da su dukka kafin komai ya chanja, amma yanzu zanje ni kad'ai, idan yaso a wannan lokacin kayi kokarin fahimtar da Mah-Mah, yadda zata fuskanta duk da ba wai abu ne me sauki ba, ina fatan komai yazo da sauki."

"In Sha Allah, Sultan amma dan Allah kar a sanar da Safwan har sai ya samu lafiya sosai, bana son abinda zai taba lafiyar sa dan Allah."

"Nayi maka alkawari Daddy, har sai ku da kanku kunji ya kamata ya sani kun sanar dashi sannan zan gabatar masa dasu, kun fi kowa sanin sa, saboda haka ku ya kamata ku fad'a masa."

"Nagode Sultan."

Gida ya maida Daddy, ya dauki wayar sa ya kira number Muhammad, be daga ba har ta gama ringing, kawai sai ya wuce asibiti, ya fara zuwa aka sallami Amrah ya kaisu gida ita da Afrah sannan ya dawo ya koma wajen Safwan.
  Yau ranar daban ce da sauran ranaku, haka ma matsayin Safwan din ya banbanta da na baya duk kuwa da ada din ma yana jin sa ne sosai kamar d'an uwa na jini, ko da ya shiga sai ya tsaya ya hard'e hannun sa ya jingina da kofar

"Kana sauri ne?" Safwan yayi maganar yana dubansa

"A ah, akwai matsala ne?" Ya tako zuwa tsakiyar dakin

"Ko daya, kawai na gaji da asibitin nan ne, inaso a sallame ni, tunda gaka pls ka saka su sallame ni."

"Sai ka kara sati daya, sai ka koma gida Dr Labaran ya tunda zuwa yana dubaka."

"Har sati?be yawa ba."

"Be yi ba, kamar yau ne ka kwantar da hankalin ka."

"Tunda kace, shikenan amma sati daya kawai wallahi."

"In Sha Allah."

"Ka zauna mana, kwana biyu baka zama balle muyi magana, naga kamar akwai abinda yake damun ka, idan akan abinda ya faru ne pls karka saka a ranka, haka Allah ya tsara."

"Babu abinda ke damuna, zan koma Canada!"

"Wait what!"

"In sha Allah."

"Why so soon? Wani abun aka turaka?"

"No wannan personal tafiya ce, ba zan dad'e ba kuma in Sha Allah."

"Personal? Zan iya sanin me? Cause jikina na bani something is not right."

"Karka daga hankalin ka, tafiyar alkhairi ce in Sha Allah, kayi min addu'a."

"Baka da doubt akan wannan, zan maka as always,just make sure you stay safe."

"I ll, kaima make sure you stay healthy, kasha magani banda korafi, kar ka ce kuma su sallame ka lallai idan sunce ka zauna kuma."

"Sallamar dai? Toh shikenan ba zan ce ba."

"Yawwa good b..." Ya rufe baki da sauri yana dariya

"Boy ko? Dan kayi aure ka barni, zan yi rama ne bari na tashi daga gadon nan."

"Zaka rame yaro, Allah kuwa."

Dariya suka saka a tare, suka cigaba da hira har zuwa sanda Mah-Mah suk shigo da wasu kawayenta da suka zo duba Safwan din, yadda take ta nan nan da Safwan din ya sake saka Sultan a tsananin tausayin ta, yasan idan komai ya bayyana ita zata fi kowa zama a bar tausayi, tashi yayi ya fita ya shiga cikin asibitin,suka hadu dasu Dr Ahmad dasu Dr Osas suka yi hira sosai, anan ya sako wa Dr Ahmad maganar ajiye aiki da yake son yi, sosai ran Dr Ahmad ya baci ganin cewa bangaren Sultan din basu da yawa ana bukatar sa sosai, yanzu ma saboda abubuwan da yadda suka kasance ya saka yayi shiru akan Sultan din, sosai yayi kokarin fahimtar dashi duk da be fito kai tsaye ya sanar dashi dalilin sa ba, amma sai yayi funfurus yace ba zai saurare shi ba, idan ma so yake dai a kara masa lokaci ya bashi enough ya gama sorting out duk matsala da yace ta taso masa. Haka ya hakura yayi musu sallama ya tafi. Ya koma ya sake duba Safwan sannan ya fito ya wuce gida.
Chapter 89 · 0% Book details