← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 108

Sashe 25

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💙

_*KIBIYAR AJALI..*_💜
_MISS XOXO_
(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)
( _Igiyar zato_)
( _Kaimin halacci_ )
( _Naufal_ )

*_ABIN DAKE CIKIN ZICIYA_*🧡
_HAFSAT RANO_
( _ruhi daya_ )
( _Sauyin qaddara_ )
( _Daurin goro_ )

*_MIN QALB_*❤️
_MAMUHGEE_
( _buri daya_ )
( _tarayya_ )
( _eznah_ )

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥*K..........*

*NH*

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE! KI DUBI GIRMAN ALLAH KI SAYA DA KUDIN KI, KADA KI SHARING, TEMAKA KI SIYA NAKI A NAMBOBIN MU DAKE KASA*

*All characters/ some places/ Incidents, Portrayed in this novel are fictitious.. *
*(Duk mutanen ciki da sunayen wasu guraren da na saka, Da wasu abubuwan da suka faru, Duk tatsuniya ce, Idan yayi shige da rayuwar wani ko wata to akasi aka samu.) Consider it as synchronization👌🏾*

*15*

Gabaki d'aya sai hankalin mutane ya dawo kan Dije dake yashe a kasa. Shi kuwa sarki Salman tuni motarshi ta bar gurin taron tamkar ba sune suka jaza wannan ta'asar ba. Basu tsaya sunji me yake faruwa ba bare su san halin da yarinyar mutane take ciki. Kafin kace menene tuni aka dauke ta aka sa a mota sai asibiti domin bata san inda kanta yake ba. Kasan cewar akwai manyan jami'ai hakan ya sanya suna zuwa asibiti babu wani bata lokaci aka shiga bata taimakon gaggawa.

Mas'oud dake kan hanyar shi ta zuwa gidan radio saboda yaje gida ya maida mahaifinsa kenan, kawai yaji labarin cewar Dije na can asibiti bata san inda kanta yake ba. Ya juyo da motar ya nufi asibitin cikin tashin hankali da tunanin abinda ya sa har hakan ya afku a kanta. Koda yaje kasa shiga cikin asibitin ya yi, yan sanda sun hana kowa shiga. Ya ciro id card d'in sa ya nuna musu amman duk da haka suka hana shi shiga, dama duk sauran yan jaridar da suka biyo su suna tsaye a bakin gate an hanasu shiga, saboda so ake a boye maganar cewa bafaden sarki ne ya yi sanadiyyar hakan. Aka fara cewa ai cikowar mutanan gurin ne yasa numfashin ta ya dauke ta zo faduwa shine ta buge.

Tuni labari yaje wajan Alhaji Isma'il yana kan hanyar shi ta zuwa filin sauka da tashi na malam Aminu Kano zai je birnin Lagos. 'Innalillahi wa'ina ilaihir rajiun' ita kawai yake furtawa tare da juyo da motarsa ya nufi asibitin cike da tashin hankali. Yana hanya ya kira Mami ya sanar da ita cewa tayi maza-maza taje asibitin shima gashi nan zai je. Cikin mamaki duk kuwa da cewa tana cike da tsantsar mamakin jin cewar Dije na kwance a asibiti tace dashi.

“Toh bari na shirya naje, amman kai ya zaka ce ka fasa yin tafiyar bayan ka riga kayi booking d'in tafiyar.?”

“Hajiya wannan ba wata matsala ba ce, jin lafiya marainiyar Allah shine kawai burina. Karki manta Dije amanace a gare ni, kuma ya ce a waje na kamar yadda su Shukrah suke.”

Yana gama maganar ya katse kiran yana jin mamakin matarsa da sam ba ta son ganin yana kyautatawa yarinyar nan. Ta kasa fahimtar cewa wata rana itama zata rabu da nata ya'yan kuma ba ta san waye zai kular mata da su ba. Mata duk lissafin su guda d'aya ne wato za'a riga su mutuwa, duk kuwa da cewa sun sha ganin Allah yana dauke wanda yaso a lokacin kuma yaga dama. Ita kuwa bayan taji ya katse wayar sai ta rike habarta, abin da mijin ta yake yi sam bata jin dadin shi. Haka ta mike taje ta shirya tasa driver ya kai ta bayan ta tambayi wane asibiti ne, aka sanar da ita.

Alhaji Isma'il na zuwa ya sanar da yan sandan dake tsare da gare cewar shine mahaifin Dije, suka barshi ya shiga inda suka bar yan jarida guda uku suka bi bayan shi ciki kuwa harda Mas'oud. Mami ma tana zuwa aka barta ta shiga ta tarar da Alhaji Isma'il ya fito daga wajan likita yana gyaran babbar riga. Ta karasa suka hadu a center, kallon da ya yi mata shine kawai ya tabbar mata da cewar tayi masa laifi wanda ba zai rasa nasaba da nuna cewa aikin shi yafi Dije da ta nuna masa.

“Ashe zaki zo?”

Ya tambaye ta yana mai lasar lebensa da ya fara bushewa saboda kaduwar da ya shiga. Kanta yana kasa tana murza zoben zinarin ta tace.

“Me zai hana Alhaji.?”

“Naga kamar baki damu ba ne shi yasa, har na fara tunanin dakko wacce zata kular min da ita.”

Kamar tace ai yanzu ma ba ita zata zauna ba, sai kuma ta hadiye kasan cewar yaki sakar mata fuska ta kasa ganin walwalar shi kamar yadda ya sabar mata.

“A a zan zauna mana Alhaji, yanzu me yaje faruwa da ita?”

Yaja numfashi yace.

“Yanzu likitan ya kira ni yace ta farfado, gefen goshinta ya fashe. Dole sai ta d'an kwana ko biyu ne a asibitin dan bata kulawar likita.”

“Daman ban da fitina ina Dije ina aikin jarida tsakani da Allah fa. Duk irin karatukan duniyar nan ta rasa wanne za ta yi sai shi saboda kawai taso ta dinga shiga cikin ridan-ridan maza. Gashi nan yanzu taje an....”

“Ya isa haka Hajiya naji. Duk da haka ma dai zan kawo wacce zata kula da Dije, ke sai ki koma gida saboda yara.”

Ta fi nono fari daman ba so take ta zauna d'in ba kawai fushin sa ne bata so shi yasa ta yadda cewa zata zauna. Yanzu kuwa da yace ta tafi idan ta gama abin da zata yi bata ja ba saboda kar taje yace ya fasa dole ita zata zauna. Ya nufi room din da aka kwanta da Dije wacce ke ta faman bacci tamkar babu abinda ya same ta. Sunkuye suka tarar da Mas'oud a gefen ta yana sharar hawaye, Alhaji Isma'il ya tambayi waye shi suka tabbatar masa da cewa abokin aikin ta ne, gidan radio d'in su d'aya.

“Allah sarki, hakuri zaka yi muma duk shi zamu yi. Dubi goshinta duk da cewar an rufe kasan cewar ciwon ba kadan bane ba. Allah ya baki lafiya Dije, yasa kaffara ne.”

Sun jima sosai a dakin kafin su fito dan gabar da sallah. Addu'a kam Dije tasha a gurin Alhaji Isma'il da Mas'oud wanda ya kasa bayyana mishi alakarshi da ita. Mami ta zauna akan kujera suna waya da Hameedah tana sanar mata da abin da ya faru wanda taji a bakin wani d'an jarida da abin ya faru a gaban su.

“Kinji yarinya Mami, ko tayi zaton har yanzu a kauye take ne?”

“Kema dai kya fada.” Cewar Mami.

“Sarki fa! Taya Dije zata ce zata yiwa sarki interview banda dai ta latsawa kanta tunani. Ai gashi nan ta jawowa kanta an ji mata ciwo a banza. Kuma ance masarautar bata yi wani abu ba akan lamarin ko?”

“Uhmmm! Kin san dai ba sarauta bace ta kauye, kuma yanzu ma rufe maganar aje son yi saboda kar a batawa masarautar suna.”

Haka Mami ta zauna a gurin Dije babu wata alfarma da take yi mata saboda tsabar wulakanci, Allah ya taimaka ma bacci take ta yi, da watakila sai tayi hawaye da idanunta. Suna idar da sallah Alhaji Isma'il ya lallaba Mas'oud ya tafi kar ya damu zata ji sauki harma ta koma aiki da ikon Allah. Ya tafi ba dan yaso ba sai dan kar Alhajin yaga kamar bashi da kunya ko sabanin haka.

Gabaki d'aya Alhaji Isma'il ya kasa samun sukuni ko fita ya yi yanzu zaka ga ya dawo har dare lokacin da Allah yasa Dije ta farka. Da Mas'oud ta fara yin karo da idanuwanta, kasan cewar ya sake dawowa asibiti da aka yi salla magariba, ya kasa zama sam shi yasa ya dawo. Dishi-dishi haka ta dinga ganinshi, ta gane shi tsab sai dai bata iya ganinshi tar-tar kamar yadda ta saba kallon abu. Ya mike tsaye tare da karasawa gurin ta yana cewa

“Alhamdulillahi ta farka Allah mun gode maka.”

Alhaji Isma'il ya shigo da sauri cike da tsantsar farin ciki juyowa da ya yi cewar Dije ta farka. Kallon mutane kawai take ba baki taki koda motsa shi bare a saka ran zata yi magana. Nurse ta shigo wacce ita ce ya bawa kwangilar kular masa da Dije. Sannu a hankali ya taje ta gyara mata inda ya kamata cikin haka ne ma suka ji ta furta.

“Kawu daddy.”

Tamkar ta tsira masa wani abun, haka yaji ya nufe ta ya riko hannunta, hawaye suka biyo ta cikin kyawawan idanuwanta, yasa hannu d'aya da yake kusa da fuskar ya share mata yana cewa.

“Bar kukan nan Dije, dena kuka zaki warke da ikon Allah.”

Still bakin ba wai budewa ya yi da yawa ba wajan son yin magana, ta kuma cewa.

“Kawu daddy sarki ne ya harbe ni ko? Wallahi ba bu abin da nayi masa kawai daga tam......”

“Yi shiru Dije, tsautsayi ne kawai da kuma kaddara suka fad'a kanki. Allah ya riga ya kaddara cewa hakan zata faru dake tun farko. Kiyi hakuri zan tsaya tsayin daka, da ikon ubangiji zaki dawo kamar baki yi ba kinji yarinya ta?”
Chapter 25 · 0% Book details