← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 108

Sashe 74

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dagowa yayi ya kalli Safwan din, wanda shi ma ya zubawa Sultan din ido ganin masifaffiyar ramar da yayi cikin yan kwanakin da yayi be ganshi ba, sosai ya kadu da ramar Sultan din tun da yasan ba karamin abu bane zai sashi irin wannan ramar farat daya bayan kuma shi yayi tunanin tunda ya samu Amrah komai zai tafi daidai.

"Ina cikin matsala Safwan, ina kuma bukatar taimakon ka a matsayin ka na dan uwana kuma cikakken lawyer,ko da abun zai kaimu ga kotu nasan zaka tsaya min."

"Wanne irin abu ne haka dan uwana ya shiga bayan nasan shi din ba me yawan hayaniya bane balle fad'a,menene yake faruwa ne wai dan Allah!"

"Nasan inda Amrah take..."

"What? Toh me muke bata lokaci kuma?"

"Dole sai mun bi komai a sannu idan muna so mu karbo ta daga hannun shi."

"Waye shi?" Safwan ya tambaya mamakin Sultan din na cikashi

"Safiyanu Madaki."

"Safiyanu Madaki? Ina kuwa na taba jin sunan nan?"

Da sauri Sultan ya mike ya zauna

"Ka taba jin sunan? Aina? Zaka iya tunawa?"

"Umm..." Yayi shiru yana tunani

"Yes! A cikin wasu takardun Daddy ne, ban dai ga ainihin abinda takardun suka kunsa ba, amma tabbas naga sunan wajen saka hannu, amma zai iya yiwuwa bashi din bane sunane yazo daya."

"Ok ok, Allah sa hakan ne, dan bana jin akwai wani abu da zai hada Daddy da wannan da na sani."

"Wai menene ya had'a ka dashi, kuma ma yaushe kayi masa wannan sanin?"

"Safwan, Ina tunanin na kusa sanin ainihin waye ni..." Yace yana lumshe rinannun idonsa da suka turu da ja sosai

"Kamar ya? Ban gane ba dan Allah ka ganar dani, me kake boye min ne? Na chanchanci haka kuwa Sultan."

"Zan fad'a maka, dama dole zaka sani ko ba yau ba, yanzu dai bamu da ishashen lokacin labari, yadda Amrah zata fita daga matsalar nan ce kawai yanxu abin tunani, it's my battle, ni kad'ai bana so ya shafi duk wani na kusa dani."

"And she's your wife, ni kuma I'm your brother, kaga kuwa duk abinda ya shafe ka ya shafe mu." Yace yana kallon sa straight in the eyes dan ya gane haushin da yaji da yace battle dinsa ne shi kad'ai.

"I'm sorry, ba wai wani abu nake nufi ba..."

"Yanzu menene abin yi." Yace yana ignoring maganar.

"Wannan yake so!" Sultan ya mika masa hannun sa da zoben yake jiki

"Zoben nan yake so, sannan ne zai kyale ta."

"Menene special akan zoben haka?"

Daga kafad'a Sultan yayi

"Ban sani ba, kawai nasan dai daga jiya zuwa yau ina jin wani strong bound Tsakani na da zoben, ina jin kamar dama chan it belongs to me, kamar dama ya bata ne yanzu na dawo dashi. Yanzu dai nasan Madaki yana jiran zuwa na, ko kira na, nasan ya shirya wa hakan, dole ni kuma nayi playing nasa at his own game, kamar yadda ya chanja tsarin shiga Masarautar saboda wasa da tunanin sarkin, haka nima zan masa."

"Kana ganin barin ta a wajen ba zai zama matsala ba toh? Ba zai mata komai ba?"

"Babu abinda zai mata, trust me nasan abinda yake so, so ba zai taba yin abinda zai saka ya rasa damar sa a yanzu ba."

"Shikenan, amma yanzu kana cikin wanda ake nema, so be kamata kazo gida ba, ya za'a yi?"

"Mu hadu same time same place gobe, karka bari ko Adnan yasan dawowa ta, sai dai kawai na kawo musu ita."

"Ok tam."

"Ina zan kaika yanzu?"

"Maidani asibiti ina da patients."

"Ok. Yace ya juya motar zuwa hanyar asibitin. Har gaban wajen ya kaishi, sai da yaga shigar sa sannan ya juya ya fita daga asibitin yana jin duk babu dad'i. Ya san abinda ya faru na daya daga cikin abinda yasa Sultan din shiga wannan matsalar, da Mah-Mah bata matsa masa ba da babu abinda zai sakashi tunanin sanin abinda yake rufe tunda iya tsawon zaman sa dashi be taba nuna hakan ba.

***Tura wa yayi ya shiga bakin sa dauke da sallama bayan ya shiga wajen colleague din nasa ya ji progress din, ya kuma bashi room number da suke da sauran abubuwan da za'a bukata, takardar biyan kudin ce a hannun sa da sauran abubuwan bukata ciki hadda jini da za'a kara mata. A saman dankwallin ta tana Sallah ya samu Maman Yara, ya tsaya ya jingina da bangon dakin har ta idar, juyowa tayi ta fad'ad'a fara'ar fuskar ta.

"Sultan sannu kaji?"

Murmushi yayi ya matsa ya zauna akan kujerar dake ajiye a gefe kasancewar dakin su kad'ai ne private room,

"Ya jikin nata?" Yace yana kallon kan gadon

"Da sauki wahala ce kawai."

"Allah ya kara sauki, ga magangunan da ake bukata zan je a siyo sai kuma jinin da za'a kara mata gobe shima."

"Allah yayi Albarka, sannu kaima, wannan rayuwar cike take da mutane marasa tsoron Allah."

"Haka ne."

Shiru sukayi kowa da abinda yake tunawa a ransa

"Sultan." Ta kira sunan sa

"Ka samu sakona wajen Malam Bako ko?"

"Na samu, sai dai ban fahimci komai ba a ciki, illa mutum daya da sanadiyar sa ne na shigo Masarautar..."

"Safiyanu Madaki." Ta fad'a tana girgiza kanta

"Abinda yasa na saka neman sa, saboda shine ummul aba'isin kusan komai da ya faru."

"Menene alakata da shi da Kuma Masarautar? Ina jin kamar akwai wani abu me girma tsakani na da Masarautar."

Murmushi Maman yara tayi cike da jin dadi, dadin zuwan lokacin da tayi ta jira tsawon wannan shekarun, dama ta fad'a musu, watarana na zuwa, da komai zai bayyana, a ranar ne zasu gane cewa sun bar baya da kura, a ranar ne mutane da yawa zasu ji kunya, kunya irin ta duniya,kafin akai ga zuwa lahira.

"Alhamdulillah Sultan, Allah shine abin godiya, kuma shine madogara idan ka dogara dashi ya isar maka, a lokacin da suka yi tunanin sun rufe babin rayuwar ka, a lokacin ne Allah ya turo, ya kuma saka ka zama nagartacce wanda dukkan iyaye zasuyi alfahari da kai. Duk da ban san inda Maimartaba da Gimbiya suke ba a halin yanzu, amma nasan duk sanda suka ganka zasu fi kowa farin cikin kasancewar ka dan su."

"Sun cire wa mahaifiyar ka abu mafi soyuwa a ranta, suka dasa mata bakin ciki a zuciyar ta, sannan daga karshe suka yi makircin da ya saka su barin tushen su, asalin su. Duk dan saboda mulki, mulkin da za'a yi shi a duniya a barshi a duniya, mulkin da idan bakayi wasa ba zai kaika wuta. Sultan idan ba Allah ba, waye zai raya d'a ba tare da mahaifiyar sa ba?ya kuma shiryar dashi zuwa tafarkin daidai? Mahaifin ka Sultan shine Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji, kuma shi ya damka amanar ka a hannu na, shine kuma mamallakin *SMM Orphanage* wanda ya gina shi da sunan ka (Sultan Muhammad Modibbo Saji*), ba tare da ya san kai din zaka yi rayuwa a ciki ba, tsawon wannan lokacin ina neman yadda zan yi na sadu da Maimartaba, sai dai garin neman yadda zanyi, Madaki yayi amfani da hakan wajen chanja komai, wanda yayi sanadiyar kasancewa ta a inda ka ganni."

Juyi sosai kan Sultan ya shiga yi har sai dai ya rike karfen gadon, sai yanzu ya gane dalilin da ya saka yake jin su a ransa sosai, ya damu da damuwar su har yake jin zai iya komai. Wani karfi ne yaji ya zo masa na gaske, ya mike ya tsaya akan digadigansa ba tare da ya jingina da komai ba. Lokaci yayi da zai dawo wa da iyayensa martabar su, lokaci yayi da zai nunawa Madaki zan iya dashi, lokaci ne da ya kamata ya kalubalanci Bilal da kuma mahaifin sa, da sauran kuma wanda ma be gama sani ba. Wani irin haske zoben hannun sa yayi, Maman Yara ta kalli hannun nasa da sauri, sannan tayi murmushi. Jini ba karya bane, kamar yadda yake babu wanda zai iya Amfani da zoben nan face shi din ya kasance jinin Maimartaba, haka ce yanzu ta kasance, kasantuwar zoben a hannun sa kad'ai ya isa ya warware komai, amma duk da haka ba zata sanar dashi komai ba, zata fi su shi yayi komai da kan sa.

"Wacece ita?" Ya nuna matar da ke kwance wanda a dah ya saddakar da ita ce mahaifiyar sa.

"Aminatu, labarin ta daban yake."

"Itace aka yiwa dashe?"

" Ya akayi ka sani?"

"Bincike nayi akai." Yace yana boye mata gaskiyar inda ya samu labarin.

"Lallai Sultan dina ya girma, girman da nake buri da fata, itace kuwa Sultan, itace."

"Ina yaran?"

"Akwai wata mata Safiyya, wadda muke tunanin ita ce ta karbi yaran, sai dai rashin sanin inda take shine, amma tabbas Madaki yasan inda take, ya kuma san wani abu game da yaran tunda na taba jin shi yana maganar be san ina wajen ba."

"Shikenan, bari na siyo magungunan na dawo."

Sai kuma ya tsaya yana saka hannun sa a aljihu, ya fito da layoyin nan ya zube su a gaban ta

"Bansan na menene ba, amma ina ganin kone su za'a yi kawai."

"Tare da zoben suke?"

"Eh a dakin sarkin na debo su."

"Ikon Allah, shikenan zan san abinda ya kamata a yi dasu."

"Madaki yana son zoben!" Yace yana kallon ta

"Karka kuskura ka bashi, idan har yaje hannun sa komai ya lalace,wahalar da mukayi shekaru munayi ta zama a banza."

"Shikenan."

Ya juya da sauri ya bar dakin, kai tsaye office dinsa ya nufa bayan ya bawa wani masinja ya bawa takardar magungunan. Yana shiga ya durkusa a k'asa, ya rasa me zai yi,kuka ko dariya, kasancewar sa da na halak da ga iyaye masu matukar daraja. Be san a wanne gurbi zai ajiya yadda yake ji a zuciyar sa ba, ya san dai kawai he's beyond happy.

Wayar sa da ya manta ya saka ta a flight mood yaji tana kara, ya dauka ganin Umaimah yasa shi ajiye wayar, kiran na katsewa ya kashe wayar gaba daya, bashi da lokacin ta yanzu dan haka ma ba zai bata lokaci wajen magana da ita ba, maganar ta ta da yasan ba me ma'ana bace.
Chapter 74 · 0% Book details