← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 108

Sashe 61

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babura ne guda biyu, Sultan ya hau daya Musa ma ya hau daya suka dauki hanyar Masarautar Saji.
Gabannin magriba suka isa, sai dai yadda harabar Babbar Masarautar ke cike da wasu irin manyan fitulu masu hasken gaske yasa wajen ya zama kamar rana, daga chan gefe suka sauke su, sannan suka nufi wata hanya daban suka bar Sultan da Musa a tsaye.
Da ido Sultan ya shiga bin Babbar Masarautar wadda take da fadin kasa sosai ga wasu manya manyan bishiyu masu kyau da suka kara kawata wajen, girman ta ya kai girman wani garin, gidaje ne daga kowanne bangare nata wanda ya kasance an musu ado da irin adon da ake ma gidan sarauta. Tun kafin su karaso Masarautar ya lura da yadda tsari da kyau da Allah ya bawa garin na Saji,babban birni ne cikin manyan birane wanda kai tsaye zaka kirashi da lamba daya indai akan kyau da tsari ne.
Hankalin sa ne ya dawo kan masu tsaron Masarautar wanda a kalla sun ta samma su talatin kowannen su babu annuri a fuskar sa, zagaye suke kawai kamar mayunwatan zaki masu farautar neman abinda zasu ce, amma idan akayi la'akari da dalilin da yasa aka sake bazasu a wajen zaka san cewa dole ne su jajirce dan kuskure daya zasuyi komai ya lalace.

"Karka yi magana duk abinda zasu ce kayi shiru, mun riga mun tsara komai."

Musa ya rada masa a kunne sannan yayi gaba shi kuma Sultan ya bishi suka nufi Babbar kofar da zata sada ka da cikin Masarautar. Kamar mutum mutumi haka Sultan ya shiga binsa yana jin kamar jinin jikinsa na tsittsinkewa yana bin hanyar da ba ita aka tanada masa domin bi ba, wani irin sakayau yake jin sa, irin abinda be taba ji ba sai sau biyu, na farko a asibiti watarana da MD ya kirashi, sai kuma a Canada. Sai kuma yau da yake jin kamar ma har wani sanyi sanyi yake ji na ratsa shi, ko kuma ace a dauko kankara a dora masa a jiki a kuma zo a rufe ta da babban mayafi. Har suka karasa inda zasu din be iya sake fahimtar komai ba, yana jin sanda Musa yake magana da wani dake chan gefe shi kad'ai, sai kuma yaga ya taso sun sake bin sa har zuwa wajen wasu su uku suma, sannan suka je wajen wasu, anan suka dan bata lokaci sai kawai yaga an bud'e musu kofar ance su shiga, kallon Musa yayi yaga baya kallon sa sai ma saka kansa da yayi suka shiga takawa cikin Masarautar wanda yake jin duk wani takun da zai yana amsawa a dukkan gabobin sa. Tafiya suka shiga yi da dan sauri duk da haka be bari abu daya na daga Masarautar ya tsere masa ba, ya bi komai yadda ya kamata ya kuma karance wani abu kad'an daga cikin yadda mutanen Masarautar suke al'amuran su, wanda kallo daya zakayi musu ka gane basu da maraba da bayi, wanda tsantsar wahala da rashin walwala yayi ma katutu.
A wata kofar katako suka tsaya, wani da Sultan ya lura da yanayin yadda yake abubuwan da sauri sauri yayi saurin bud'e musu, suka kutsa kai ciki sannan yaja kofar ya rufe yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya kana ya bar wajen bayan ya tabbatar da babu wanda ya gansu.

***Hannun sa a goye a bayan sa yana kaiwa da komowa tsakanin dakin, daga chan gefe wasu ne a durkushe kansu a k'asa , dakin yayi shiru dukkanin su suna jiran suji abinda Sarkin zai ce, tsawon lokaci be ce komai ba sai dan siririn tsaki da yake ta ja a hankali a hankali. Sun cire rai da zai ce wani abu sai kuma ya koma da baya ya hau kan karagar sa, sannan yace cikin kaushin murya.

"Idan har abinda muke tunani zai shigo cikin Masarautar nan a gobe, ya zama dole mu tabbatar da zuwan sa hannu, duk da bamu da Ikon ganin ko menene ko waye, sai dai jikina na bani wani gagarumin abu ne ke tunkaro mu, dan haka ba zamuyi kasa a guiwa ba wajen ganin mun kare martabar abinda muka dad'e kafin mu same shi, ya zama dole ne, kowa a cikin ku ya zama a shirye shiri bana wasa ba, dan bamu san wanne shiri sukayi a kanmu ba."

"An gama ranka ya dad'e." Suka had'a baki wajen fad'a, wani daga ciki ya duka kad'an sannan yace

"A duban da nayi dazu, sai naga abun na kusa damu sosai, kusan da nake jin tsoron kar mu sakankance su shammace mu, ina ganin ya kamata a sake dubawa."

Babban yayi karaf da sauri yace

"Kana nufin abinda na gani akan zuwan nasu gobe ba daidai bane? Ko kana nufin bansan aikin da nake ba ne?" Ya karashe a dan hasale.

"Ba ina nufin hakan bane, sai dai..."

"Ya isa!" Sarki ya dakatar dasu

"Yanzu ba lokacin musu bane ko nuna wani yafi wani, lokaci ne na aiki babba, aikin da yafi wanda kukayi a baya, ruwan kune ku bar komai ya lalace."

"Tuba muke ranka ya dad'e."

Fuu ya tashi ya shige ciki ya barsu zaune, a hankali duk suka fice daya bayan daya cikin shigar su ta kowanne lokaci idan zasu zo ziyarar sarkin.

***Karewa dakin kallo Sulthan yayi, babu komai sai wata tabarma daga gefe, sai tarin wasu kaya daga dayan bangaren dakin, sai dai akwai bandaki karami a manne a ciki, da sauri ya sauke jakar sa, ya nufi kofar bayan ya tabbatar da hasashen shi, alwala ya dauro saboda ya samu yayi sallar data tsere masa, yana fitowa musa ma ya a shiga yayi alwalar shima, sultan ya jasu suka rama sallolin da suka tsere musu sannan suka yi Isha'i wadda ake yi a daidai lokacin.
Pad din sa ya ciro ya bud'e yana duba sakonnin da Amrah ta turo masa akan ta kira shi a kashe dan kashe ta yayi gaaba daya, murmushi yayi me kyau sannan ya tura mata reply,few lines masu ma'ana, kafin tayi reply ya maida wayar flight mood saboda baya son ta kira shi ta masa tambayar da bashi da amsar ta shima.
Suna nan zaune wanda ya rako su ya sake shigowa, ya ajiye musu kwanon abinci guda biyu kowa a gaban sa,ya rissina sosai wajen bawa Sultan wanda har yaso ya bawa Sultan din mamakin yadda suke girmamashi duk da be san dalili ba, be ma kuma san me Madaki da wannan amintaccen yaron nasa Musa suke shirya wa akansa ba, ya riga dai ya gama shirin sa shima lokaci yake jira ya aiwatar da komai amma kafin nan zai cigaba da bin su a yadda suka yi nasu tsarin.

******
Assalamu alaikum
Barkanmu da Sallah ya iyali? Masu complain na ki dawowa kuyi hakuri, abubuwa ne suka sha min kai plus bana gari. Hankali na gaba daya yana kan rubutun nan tunda duk abinda ka fara burin ka kawai ka gama shi ka sauke nauyi.
Nayi typing da yawa yana Wattpad sai dai ntwrk sam ya hanani logging, complain din da naji ne ciki hadda maganganu marasa dad'i yasa na rubuta wannan din yanzu. Nagode
[5/20, 9:05 AM] Maman Maryam: ©️®️ Hafsat Rano
Page 26

Wannan littafin na kudi ne, AMANA CE, duk wanda yayi mana sharing dinsa shi da ALLAH! Idan kina/Kana so ki/ka karanta ki/ka tuntubi numbobin nan*

*0903 234 5899*
Or
*09033181070

***Da sauri ya dago, yana son ganin ainihin gaskiyar abinda tace din,be yi tunanin abinda zata ce kenan ba. Sosai ya shiga shock har ya rasa me ma zai ce

"Mah-Mah?"

"Abinda nake so kayi kenan, a matsayin rama alkhairi da alkhairi, a matsayin tukwuicin abinda mukayi maka, idan kayi wannan bani da sauran komai a kanka."

Juyawa tayi da nufin barin dakin, sai kuma ta tsaya ta juyo

"Karka manta, kayi alkawarin zaka yi ko menene."

Ta karashe sannan ta fice daga dakin. Bin inda tabi ta fita yayi yana ganin kamar be ji daidai ba, kamar ba abinda Mah-Mah take son fad'a ba kenan, kamar ma ba ainihin Mah-Mah da ya sani bace ba, an chanja ta ne da wata daban ko kuma anyi brainwashing dinta ne.

"Zan iya? Zan iya?" Ya shiga tambayar kansa, sai kuma ya girgixa kai

"No...Ba zan iya ba, aure ba wasan yara bane, aure abu ne me girma da be kamata ayi irin wannan wasan dashi ba."

Ya bawa kansa amsa a fili yana girgiza kansa.

"Amma Safwan fa? Be chanchanci komai ba a wajenka? Ko da hakan shine abu na karshe da zaka aikta?"

Wata zuciyar daga chan bayan kansa ta tunasar dashi

"Toh ita kuma Amrah fa? Baku tunanin rayuwar ta sai Taku? Me take so menene zabin ta? Babu wanda ya damu sai kanku kuka sani?"
Chapter 61 · 0% Book details