← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 108

Sashe 72

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Duhu ne sosai a dakin wanda yasa har baya ganin gaban sa, dawowa yayi da baya ya bud'e kofar hasken falon na ratso wa ciki kad'an, tunawa yayi da wayar dake aljihun sa, ya ciro ta yana rufe kofar sannan ya kunna dim light na wayar ya shiga haskawa.  A saman wata doguwar couch ya hangi mutum a kwance sambal, hannayen sa sun kusa sauka k'asa, da dan sauri ya karasa wajen ya haske shi, yayi saurin ja da baya ganin Sarki ne a wani irin yanayi kamar me rai kamar mara rai, tsoro ne yaji ya shige shi, idan har Yarima Bilal zai iya yiwa mahaifin sa haka, waye zai bari kaf duniyar nan? Amma kuma sai wani tunani ya darsu a zuciyar sa, anya kuwa dan sa ne na gaskiya? Domin dai a yadda mutane suka lalace da son duniya da son mulki babu abinda ba za zasu iya aikatawa ba. Idan har d'a zai iya aikata wata cutarwa  ga iyayen sa, toh kuwa wacce irin duniya ce muke ciki haka. Amma kuma sai yayi tunanin ai dama shi fa sharri dan aike ne, duk inda yaje zai dawo, kuma shiyasa ake so mutum ya aikata alkhairi a ko yaushe, idan aka bi kidddigar mutanen da Sarkin ya zalunta, toh tabbas ba zai tsira ba, ba zai tsira a wajen kowa ba kuwa ciki hadda iyalansa da yayi komai saboda farin cikin su.
  Girgiza kai yayi ya wuce zuwa abinda ya kawo shi, akan guiwar sa ya durkusa bayan ya tattare hannun rigar sa zuwa damtsen hannun sa. Bismillah yayi ya shiga jawo akwatin da yaji ta da wani irin nauyi, beyi garaje ba ya cigaba da jawo ta a hankali har ya gama fito da ita gaba d'aya, dan matsawa yayi baya da sauri ganin wani haske me karfi ya fito daga ciki, yayi sama. Sauke ajiyar zuciya yayi yana addu'a a fili a hankali, ya riga ya san ba karamin abu ne a cikin akwatin ba. Komawa yayi ya sunkuya ya d'aga murfin da yake a bud'e babu padlock a ciki sai dai alamar shi a jiki. Tarkace ne sosai a ciki tun daga kan takardu, wukake da wasu kayan a nannade,sai wasu irin abubuwa kamar layu a nannade suma da yawan gaske, daga gefe wani mukulli ne na karfe an masa ajiya ta musamman,kusa dashi wata yar karamar akwati ce, karama sosai an nannade ta da wani bakin kyalle me sulbi.
  Ada kafin ya iso wajen tunanin sa zoben nan ne kad'ai a ciki, sai dai ganin abubuwa da yawa yasa shi son sanin dukka, sai dai yasan bashi da ishashen lokacin yin komai amma still yana da bukatar dubawa, layoyin nan ya kwashe tas ya zuba cikin aljihun sa. Sannan ya maida hankalin da yafi karkata akan karamar akwatin nan, yayi saurin ciro ta sannan na warware nad'in da akayi mata, a rufe take da mukulli, ya sake ciro mukullin da ya gani a kusa da ita ya saka a jiki ya bud'e. Kamar yadda yayi tunani hakan ce ta kasance,zoben ne a ciki, an dora shi akan wani jan kyalle me kyau da sulbi shigen wanda aka nannade akwatin dashi, sai dai kamar yadda ya sani babu wani bangare na jikin zoben ya saka shi ciro wanda yake tare dashi, yayi kokarin had'e su, kamar yadda zaka hada karfe da mayen karfe haka barin ya hade da jikin dayan barin ya bada zobe cikakke, a daidai lokacin yaga Maimartaba ya motsa k'ad'an fuskar sa na daurewa sosai bakin sa na yin motsi alamar yana son fad'ar wani abu. Kallon zoben Sultan yayi ya runtse idon sa ganin wani irin haske da zoben ki fitar wa, be taba hasashen shi a cikin irin wannan badakalar ba sai gashi ya samu kansa dumu-dumu a ciki, bismillah yayi ya zura zoben a babban dan yatsan hannun sa, wani abu ya shiga ji na yawo a saman kansa,  zuciyar sa na sake karfi sosai yana jin kamar tana ingiza shi zuwa wani abu mai girma. Jingina yayi da bangon dakin saboda yadda yaji dakin na juya masa kamar zai fado akan sa ya dafe kan sa da hannun sa dayan yana karanto duk addu'ar da tazo bakin sa, a hankali ya sulale a wajen yana jin idonsa na nauyi sosai, kad'an kad'an ya dinga rufewa har ya rufe gaba daya.

Shigowa Yarima Bilal yayi tare da wata mata, ya kunna hasken dakin yana murmushi zuciyar sa fes, bai taba tunanin zai samu cikar burin sa da sauki haka ba, sai gashi komai ya zo masa da mugun sauki, gefen da SULTAN ke yashe ya kalla yayi dariya sosai sannan ya kalli akwatin da ya jima yana kulafucin ta, kasancewar bashi da wata nasaba da Masarautar yasa ya kasa samun yadda zai kai hannun sa kanta, sai gashi a daidai lokacin da yafi bukatar ta, Musa amintaccen Yaron Safiyanu Madaki ya kirashi ya guntsa masa kyakkyawan labarin da ya sanya shi cikin matukar farin ciki shi da mahaifiyar sa, ya kuma yi amfani da damar wajen amfani shima da Sultan din kamar yadda Madakin ke kokarin yi, sai dai shi yayi sanya a aikin nasa don kuwa sai dai ya sake wata dabarar, kujerar Masarautar Saji yanzu ta Bilal ce, Muhammad Bilal Bello Moddibo Saji a zahiri, a bad'ini kuma*Muhammad Bilal Surajo* 
Dukawa yayi ya fiddo takardun kamar yadda suke, ya dauke su ya mika wa ma mahaifiyar tasa sannan ya karbi na hannun ta wanda suka kasance iri daya sak ya nufi inda Maimartaba ke kwance ya farfado amma kamar be san me yake wakana ba, kama hannun sa yayi da karfin gaske ya saka masa biro, sannan ya dora a daidai wajen da zai saka hannu, da sauri Maimartaba ya dora hannun sa akai sannan ya saka hannu kamar yadda Yariman ya bukata. Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar sa, ya mika mata da sauri yana cewa

"Kalli kiga, ta saka hannu, ya saka hannu wallahi, shikenan an gama, Kurunkus." Yace yana zare ido kamar sabon mahaukaci. Karba tayi ta duba ta saka dariya itama

"Lallai sai yanzu nasan na haifi d'a, sai yanzu nasan da cewa kai jini na ne da gaske."

Durkusawa yayi ya dauko wata wuka, masu, da wani sanda, sai doguwar takarda dake a nannade ya warwareta, yana karanta dokokin Masarautar Saji yana dariya.

"Wannan dokar tasa ce, daga yau tawa zan shinfida yadda naso."

"Kayi min daidai." Tace tana duba kayan, komai yacika, wadannan sune shaidar da take nuna sarautar Masarautar, kuma ana bawa duk sarkin dake kan mulki, kamar wani sign ne na Masarautar tun fil'azal

"Ina kayan karka manta dasu fa."

"Af kinga na manta shaf." Yace yana ciro kayan ya warware su. Kayan sarauta ne tun daga kan babbar riga da rawani da sauran su, kayan akan bawa duk sarkin da zai hau mulkin ya saka su a ranar da za'a yi nadi.
   Hasaso kansa ya shiga yi a cikin kayan gobe, yasan zai fi kowanne Sarki haskawa a cikin kayan kuwa saboda shi suka dace, ganin ya samu dukkan abinda yake bukata yasa ya saka kafa ya tura akwatin karkashin gadon, bashi da bukatar zoben duk da shine abu mafi girma a cikin sarautar Masarautar,amma kasancewar babu barin ya saka har ya bar Sultan din ya dauka domin babu amfanin da zai yi idan babu cikon sa.
   Fita sukayi suka bar Sultan a dakin, daga bisani wasu fadawa suka zo suka ciccibe shi bisa umarnin Yariman suka maidashi shashen sa suka saka shi cikin dakin da ya tare suka rufe.

***Da sanyin safiya aka shiga gyara Babbar Fadar Masarautar wadda sarki be fiya zama a cikin ta ba idan ba wani abu me muhimmanci za'a yi ba ko nadin sarauta. Duk manyan Masarautar suna kan hanyar zuwa fadar bisa ga umarnin Sarki kamar yadda dan aiken ya sanar dasu, babu wanda be yi mamaki a cikin su ba,dan ba haka Sarkin ya saba yi musu ba.
    Kafin kace me ciki da wajen fadar ya cika taf, dan layi layi yarima ya saka me shela sanar da baban taro wanda ake bukatar kowa ya hallara. Duk manyan yan fada sun gama isowa sun zazzauna suna jira fitowar Sarki suji dalilin taron gaggawa haka da kuma ya had'a da mutanen gari ma. Sun dan dau lokaci a zaune kowa na tattaunawa da na kusa dashi kofar da aka san Sarkin na shigowa ta cikin ta, sai dai a maimakon aga Sarkin sai suka ga Yarima ya fito cikin shigar da ta saka da yawan su tsorata, kai tsaye kan karagar Maimartaba ya nufa ya haye fuskar sa daure tamau ya saka wani bakin glass a saman rawanin da ya kusan cinye kafatanin fuskar sa.

"Lafiya Yarima?" Waziri ya tambaya yana mikewa tsaye. Da hannu Yarima ya bada umarni wasu fadawa suka shigo da sauri suka zube bayan sun ajiye kayan dake hannun su wanda Yariman ya dauko su a cikin akwatin nan. Da mugun mamaki duk suka kalli Yariman, sanin muhimmanci kayan d kuma abinda hakan ke nufi. Tsam suka yi kowa ya kasa furta komai har sai da Yariman da kansa ya taso sannan ya dauki takardar da Sarki ya saka hannu ya mika musu yana murmushi.

"Ina so ayi sauri a aiwatar da abinda yake cikin takardar nan, bana so a bata lokaci."
Chapter 72 · 0% Book details