← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 108

Sashe 82

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin cika tsoro, allurar ma?" Yace yana zama kusa da ita, sannan ya jawo ta jikin sa, ya dora mata fuskar ta a saman fad'ar sa, kamar yadda ake rike kananan yara haka ya rike ta, ya rada mata wani abu a kunnen ta wanda ya saka ta mantawa da allurar da za'a yi mata, da hannu yayi ma Nurse Falmata da tayi mata,fuskar ta cike da murmushi ta matso tayi mata allurar, sai bayan da ta cire sannan ta motsa tana son tashi, ya sake matse ta sosai.

"Malama don't pretend sai bayan an gama zaki wani tashi, kin san sanda akayi miki?" Ya tsare ta da ido bayan ta dago kanta.

"Bata sani ba kam Dr, Allah ya bada zaman lafiya." Nurse Falmata tace tana juyawa ta bar dakin tana murmushin abinda ya faru.

Turo baki Amrah tayi tana son tashi, hana ta yayi, ya zagayo da hannun sa ta bayan ta,

"Police din nan suna jiran ka fa." Cikata yayi dan har ga Allah ya manta dasu, ya juya ya bar dakin. Kasa controlling farin cikin da take ciki tayi, ta dinga blushing, kumatun ta har wani lotsawa yake saboda farin ciki, babu abinda yafi soyayya dadi idan kayi dace, musamman da mutum irin sultan wanda yasan yadda zai ya faranta maka.

Hajiya da kanwar Abba basu dawo dakin ba sai Umma da zata kwana ita da Afrah suka shigo suka zauna, basu dad'e da zama ba ta koma baccin cike da mafarkin Sultan

***Ko gaban ta bata gani, haka ta karasa wajen da suke zaune, kad'an ya rage ta taka kafar Mah-Mah Allah ya kiyaye.

"Ke Umaimah, me kike yi haka?" Anty Farida ta yi maganar ganin yadda take kamar zata fad'i, rik'e ta Ya Umma tayi, ta jata gefe.

"Menene?"

"Bakin gani nayi, Sultan tare da banzar yarinyar chan, wayyo zuciya ta zata fashe wallahi."

Da sauri Ya Umma ta rufe mata baki

"Karki tara mana mutane anan kike daga murya haka, Matar sa ce fa."

"Allah Anty Ummah ba zan iya dauka ba, zuciya ta na mun zafi noo I can't take it." Ta girgiza kai tana buga kafa da karfi

"Nace ki bar komai a hannu na ko? Kinga ban yi wani abu bane ko Yaya? Ki bar komai hannu na."

"Lokaci tafiya yake ai."

"Karki damu, ki barmun komai kawai kinji yar albarka?"

"Shikenan." Ta barta a wajen tayi hanyar da ba wajen da su Mah-Mah ke zaune ba.

"Allah ya kiyaye wallahi,yadda na tsani yaron nan ficika ba zan kashe ba, haka zaki hakura ki samu wani me arziki da tushe ki aura." Tayi maganar tana komawa wajen su Mah-Mah.

***Abubuwa sun kara baci a Masarautar Saji,gaba daya komai ya tabarbare, sosai Yarima Bilal da Sarki Bello ke haurawa sama, shi Sarki Bello damuwar sa yadda za'a yi komai ya daidaita, wanda shi kuma Yarima ta mulkin kawai yake wanda shi a haukan sa tunda ya samu shikenan,be san abinda zai biyo baya ba. Duk wadanda ke da ruwa da tsaki a cikin maganar sun shiga damuwa, gashi aikin suke babu dare babu rana amma shiru kake ji kamar an shuka dusa, ko isasshen bacci basa yi suna kulla yadda komai zai kasance, ya kuma cigaba da tafiyar musu kamar yadda yake, sai dai abinda basu sani ba shine... Allah zai ta arawa mutum dama ne, har zuwa wani lokaci, lokacin tonan asiri, lokacin jin kunya da dana sani mara amfani.
Madaki tun da ya samu labarin kama yaron sa daya da akayi, ya tsallake ya bar kasar, dama akwai tafiyar da zai yi washegarn ranar Kawai sai yayi amfani da wannan ya cikawa wandon sa iska, duk da ba wai ya hakura bane amma kuma yana bukatar lokacin tunani.

***A hanya suka hadu da Umaimah, tayi kamar zata fad'a kansa da ta ganshi, yayi baya kadan

"Are you ok?" Tace tana kallon jikin sa, tayi kokarin kai hannu saman kansa fuskar ta na nuna tsantsar tausayin sa

"Ya jikin? Me yake maka ciwo yanzu?"

"Babu komai, na samu sauki."

"Amma ka rame sosai."

"Yaushe kuka zo?"

"Dazu, nazo zan dubaka dazu sai..."

"Ohh kece kika shigo dazu dama?"

"Amma mesa baki shigo ba kika koma?"

"Naga kamar u guys are busy ne, bana so na dame ku." Tayi maganar tana son karanta expression din fuskar sa.

"Ok. Yayi." Ya juya ya cigaba da tafiya, jerawa tayi suka cigaba da tafiyar tare tana cigaba da yi masa hira, da k'yar yake hada kalma uku zuwa hudu wajen amsa mata, dan bata san yadda ya gaji bane shiyasa, gashi sai son sako maganar Amrah take a fakaice tana son ganin yadda zai yi, ya jima da sanin take taken ta, ya kuma san dalilin da yasa take hakan. Shi ba wannan ne a gaban sa ba, da tasan abubuwan ma da suke kansa da ta shafa masa lafiya ta barshi da wannan uban zancen nata. Suna kawowa dakin da Safwan yake ya ja ya tsaya sannan yace

"Ba'a shiga wajen sa." Yayi gaba kawai ya barta a tsaye, yasan bin sa zatayi da be mata haka ba, shiyasa ya dakatar da ita dan ba'a bukatar hayaniya ko surutu a dakin shiyasa babu wanda yake shiga daga Mah-Mah sai Daddy sai kuma Sultan din.

Dakin Safwan din Sultan ya koma ya zauna yana lura da duk motsin sa, har wajen uku na dare be runtsa ba, baya jin baccin gaba d'aya,sai wajen asubah ya kwanta ana kiran sallar ya tashi,yayi sallah ya zauna ya bud'e wayar sa ya bud'e wani app din Al'qur'ani ya shiga karantawa a nutse.

***Leka wa Maman Yara ta sake yi tayi, tana mamakin abinda ya hana Sultan zuwa ya gansu tun bayan ya fita, duk sai taji babu dadi tana kuma tunanin Allah yasa lafiya dan tasan babu abinda zai hana shi zuwa garesu sai dai idan wani abu ya rike shi.

"Me yasa har yanxu Sultan be dawo ba?" Aminatu tayi maganar tana kallon Maman Yara

"Yanzu ma maganar sa nake a raina, Allah dai yasa lafiya."

"Amin." Sai sukayi shiru gaba daya. Kowannen su na fatan ba wani mugun abu bane ya tsaida shi ya hana shi zuwa. Babu wanda Maman Yara take tunawa irin Madaki,tana tsoron abinda zai iya akan Sultan din tana kuma addu'ar Allah kar ya sake bashi dama akan kowa ma.

***Shiryawa yayi, ya dan ci abincin da Baba Altine ta dafa musu ya fito, so yake ya fara zuwa ya duba su a asibitin sai ya wuce wani waje. Keke napep ya hau ta kaishi har kofar asibitin ya sauka a gate ya shiga a kafa, duk da besa dakin da zai same su ba amma yasan ba zai sha wahalar nema ba, ya rik'e sunan Sultan da Safwan din ma saboda haka kai tsaye reception ya nufa, ya tambaye su, kwatanta masa sukayi yayi godiya ya tafi. Sai dai maimakon yayi bangaren maza sai ya nufi bangaren mata, ya duba number dakin itace wadda aka fad'a masa, ya tura ya shiga bakin sa dauke da sallama, direct kofar shigowa take kallo saboda haka yana shiga da ita ya fara cin karo. Wani irin shock yayi, yayi saurin cewa

"Kuyi hakuri ba dakin da nake nema bane." Ya juya da sauri,

"Bawan Allah!" Ta dakatar dashi, ta taso har da saurin ta

"Yaya sunan ka?" Ta tambaye shi tana kallon fuskar sa

"Muhammad."

Sai ta girgiza kai,

"Shikenan."

"Sai anjima."

Ciki ta dawo ta zauna, fuskar ta dauke da damuwa

"Lafiya Aminatu?"

"Ko kin sanshi ne?"

"A ah, bansan shi ba, kawai dai..."

"Kuskuren lamba ya samu da alama."

"Eh daga gani." Tayi maganar tana sauke ajiyar zuciya.

***
Sau wajen biyar kenan Daddy na katse kiran sa tun bayan da ya karanta sakon sa, be san dalilin kiran ba amma sai yake jin ba alkhairi bane kiran nasa, mamakin sa yadda akayi ya samu number sa, bayan dogon lokacin da aka dauka be sake jin duriyar sa ba. Ganin da gaske kiran ne ke sake shigowa yasa ya kashe wayar tasa ma baki d'aya, yayi abinda zai ya dauki abinda zai dauka ya koma asibitin.

***
Manage pls!!!!!!!!!!!!!    © Hafsat Rano
Page 42

****Ina ma’abotan son ingataccen *yaji* Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk abinci na al’ada by da zamani, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin

*@the_flavorland by Aceey*

Sun kawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da:
*Yajin daddawa*
*Garlic Yaji* waton yajin tafarnuwa da kuma
*Beef Yaji*  wato yajin nama kuma me hade da nama

Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da:

Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi da

Gashe gashe da soye soye kamar su

Kaza
Kifi
Nama
Doya
Dankalin turawa/hausa
Awara
Danwake
Gurasa
Kwado da dai sauransu....

Ba Mu tsaya anan ba——
*The_flavorland* ya hada da kayan tande-tande da lashe lashe da suka hada da
_Hoppers_ wato
*Fara*😛
_Milky candies_ wato
*Alawar madara*
da kuma
_Milky balls_ wato
*Gullisuwa*

Da de sauran abunda rai ke buqata...
Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka

*IG:* *@the_flavorland*

*Whatsapp:* *08104673847*

*Sending Some treats your way....*

*Let us satisfy your cravings:*
      We Deliver anywhere and everywhere.

***Sau wajen biyar kenan Daddy na katse kiran sa tun bayan da ya karanta sakon sa, be san dalilin kiran ba amma sai yake jin ba alkhairi bane kiran nasa, mamakin sa yadda akayi ya samu number sa, bayan dogon lokacin da aka dauka be sake jin duriyar sa ba. Ganin da gaske kiran ne ke sake shigowa yasa ya kashe wayar tasa ma baki d'aya, yayi abinda zai ya dauki abinda zai dauka ya koma asibitin.
  Yana zuwa ya tarar da Safwan ya farka, duk da babu wanda ya shiga dakin sai drs din sai Sultan da dama yake ciki, amma su Mah-Mah sun ce masa wai Sultan din ne yaga yana motsi, shine ya dubashi yaga ya dawo hayyacin sa. Kowa ka kàlla a wajen a cikin farin ciki yake, suna tsatsaye ana jiran fitowar Dr's din suji idan komai lafiya. Mah-Mah bakin ta ya gaza rufuwa gashi ta kasa zama waje daya sai zagaye take.
Chapter 82 · 0% Book details