Sashe 67
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ya tura kansa ciki, da farko baya ganin komai sai duhu sosai da ya mamaye dakin, sai da ya shiga ciki sosai sannan ya hange mutane biyu a zaune, daya ta jingina da kafad'ar daya, wani irin tsoro ne ya kamasa ganin mutanen da ke ciki matana, mata a irin wannan yanayi, mata da suke da daraja da kima su aka wulakantar saboda neman duniya, duk da besan wanne irin abu suka aikata aka kawo su wajen ba, amma yasan komene basu chanchanci wannna hukuncin ba, be taba sanin abinda ake fad'a a gidan sarauta haka yake ba sai da ya shigo Masarautar Saji, tsantsar zalinci da mulkin mallaka ake ma al'umar musulmi. Hawaye yaji na neman zubo masa, yasa hannu ya share yana jin zuciyar sa na zafi, yana jin da ace zai samu dama,da ace zai iya wani abu, da ace shi din wani ne me karfin iko a Masarautar da ya chanja komai, amma waye shi? Shi da bashi da uwa balle uba, baya raba daya biyu a cikin matan nan ko daya itace mahaifiyar sa, ko kuma wata makusanciyar sa tunda har Madaki yace ya neme su lallai kafin ya bar Masarautar. A sanyaye ya karasa ya durkusa a gaban su yana kallon yadda daya daga ciki ke fitar da numfashi a wahale, kamar ma bata da lafiya.
"Kuyi hakuri." Ya samu kansa ta furtawa bayan yayi kokarin tattaro abinda ya kamata ya fad'a musu da zai rage musu rad'adin abinda suke ji ya kasa, da sauri ta bud'e idonta, ta sauke su akan sa, a lokaci daya ta mik'e tsaye tana sake fitar da tsantsar mamakin ta.
"SULTAN!" Ta furta da sauri tana nuna shi da hannu.
***Kai tsaye kurkukun ya nufa, daga shi sai amintaccen bawan sa guda daya, tun kafin ya karasa aka bada sanarwar isowar Sarki, cikin wani irin tashin hankali bafaden nan ya shiga, yasan babu wata hanya da Mutumin da ya bari ya shiga wajen zai bi ya fice ba tare da sun hadu da sarkin ba, ba kuma zai iya fitowa kafin sarkin ya karaso ciki ba. Be gama fita daga cikin tashin hankalin da yake ba, Sarkin ya karaso fuskar sa a matukar bace, kallo daya zakayi masa kasan akwai babban al'amarin da ya kawo shi wajen. Fitsari ne kawai yaji ya fara bin kafar sa da yaji muryar bawan nan na isar da sakon sarki akan a bud'e masa kurkukun me lamba 108.
***I'm very sorry please🙏🙏🙏🙏🙏_Abinda ke cikin zuciya_
_Hafsat Rano_
_Page 31_
***Mike kafarsa yayi yana kallon yadda ta dan daga ta kumbura, kwana biyu baya jin dadin jikinsa, sosai kafar ke matsa masa har wani lokacin sai yaji kamar ba zai iya takata ba. Yana zaune ta turo kofar ta shigo, ya bita da kallo har ta zauna a gaban sa, zaman dirshan, irin zaman da be taba gani tayi a gaban sa ba tun zuwan su k'asar. Sosai ya maida hankalin sa akanta dan yasan ba karamin abu bane ya kawo ta.
"Ya akayi gimbiya?" Yace ganin taki cewa komai. Shiru tayi tana kallon k'asa, hannun ta daya tana murza shi jikin zoben dake dayan hannu. Dabi'ar ta kenan tun lokacin baya idan har tana son yin magana dashi kuma maganar ta kasance mai muhimmanci ce a wajenta, murmushi yayi me kyau, hakan da tayi ya tuna masa da lokacin chan baya,sanda suke cikin kwanciyar hankali kafin komai ya lalace ya zama tarihi, sai dai be fitar da rai ba, yana ji a ransa kukan su ya kusa karewa, komai zai dawo musu ko da ba a yadda yake a baya ba saboda shekarun da suka ja, amma yana fatan wani yanki na farin cikin su ya dawo suyi rayuwa irin wadda ya dad'e yana musu mafarki.
"Ina sauraron ki, kinsan babu abinda yafi muhimmanci a wajena fiye da damuwar ki,dan Allah ki sanar dani ko da ba zan iya yi miki wani abu akai ba, amma ina so mu raba damuwar tare."
Matsawa tayi kad'an ta sake kusantar sa, fuskarta na sakewa ba kamar farkon zuwan ta falon ba, tace
"Na damu da yaron nan Muhammad, na kasa samun nutsuwa tun ranar da ya barmu, me yasa nake jin sa haka a raina?"
"Be ke kad'ai ba, ni kaina hakan ce a wajena, sai dai nafi alakanta haka a matsayin rasa wanda zamu iya tattaunawa dashi akan rayuwarmu da mukayi tsawon lokaci sai bayan haduwar mu dashi, watàkila hakan ne dalilin da yasa muke jin sa har cikin ranmu."
"Haka ne." Tace tana jan ajiyar zuciya.
"Zan kokarin had'a ki dashi gobe a waya kinji? Idan kukayi magana hankalin ki zaifi kwanciya nasa."
Da sauri tace
"Yauwa dan Allah."
"In Sha Allah." Yace yana murmushi.
"Nagode."
"Anything for my queen."
Sai kawai tayi murmushi.
***
"Sultan kaine anan?!" Ta matso sosai, dan hasken da ya ratso ta cikin dakin ya bashi damar ganin ta sosai, da sauri yasa hannu ya rufe bakin sa, fuskar sa na dauke da mamaki, tun lokacin da ya shigo dakin nad'in da yayi wa kansa ya cire hakan ya bata damar ganin fuskar sa, ba wata bace face Maman Yara, matar da dalilin neman ta ne ya kawo shi wajen nan, amma me take anan? Menene alakar ta da wannan rikirkitarciyar Masarautar me cike da mugayen mutane, menene alakar ta da Madaki da kuma dalilin da yasa tace ya neme shi wajen neman iyayen sa? Bashi da amsar ko daya a ciki, sai dai ganin ta yanzu ya sa shi jin wani sakayau a ransa, yana da yakinin abubuwan zasu zo masa da sauki tunda ya tabbatar da tasan wani abu game dashi ko ba dukka ba. Amma abinda be sani ba shine, suna da lokaci kuwa? Me zai faru idan komai ya lalace aka gano ya shigo wajen, za'a iya chanja musu wani wajen da har abadah ba zai sake ganin ta ba.
"Maman Yara!"
"Alhamdulillah, Allah kaine abin godiya, sultan ya akayi ka shigo nan, yaushe ka shigo Masarautar? Ka hadu da Malam Bako? Ka hadu da Madaki ?"
Da ka ya amsa mata sannan yace
"Madaki ne ya turo ni akan wani zobe, ya kuma ce lallai na nemi kurkukun nan kafin na fita, hakan da zanyi shine zai sa ya had'a ni da iyayena."
"Karka taba yarda ka bashi abinda yake nema, nima kaina na yarda dashi har na bar komai a hannun sa ba tare da nasan mugun nufin sa ba, zoben nan shine duk wani matakin nasarar Sarki Bello, kuma shine yake dauke da duk wani kulli da akayi maka kai da yan uwanka da iyayen ka, kaine magajin Masarautar Saji Sultan, kaine kad'ai zaka gyara komai ka dawo dashi yadda yake, sai dai ba abu bane me sauki, sai ka kula, sai ka kula!"
"Magajin Masarautar Saji?" Ya tambaya muryar sa dauke da wani irin Amo, cikin rashin fahimtar abinda take nufi."
Daga masa kai tayi da sauri sannan tace
"Kai din dana ga Adalin Sarki, Sarki Usman Muhammad Moddibo Saji!"
Sai ta dora
"Akwai abubuwa da yawa da dole sai ka samu zoben nan, wanda barin yake tare da Aminatu gata nan, anan ne komai zai dinga warware kansa a hankali a hankali."
Sai ta bud'e hannun sa ta saka masa shi ta rufe sannan tace,
"Karka bata lokaci dan mutanen nan basu da kirki, kayi sauri ka aiwatar da abinda ya kamata kafin su farga da kai, ka dage da addu'a dan itace take rik'e da kai har zuwa wannan lokacin Sultan."
"Wacece wannan matar?" Ya nuna Aminatu dake kwance tana bin sa da kallo sosai, idanun ta na fitar da hawaye masu zafin gaske. Girgiza masa kai Maman Yara tayi
"Abubuwa da yawa ba zaka sansu yanxu ba, babu lokaci Sultan, Idan har kayi nasarar daukar zoben nan, zaka samu dukka amsoshin da kake nema, amma a yanzu mu bar komai a yadda yake."
"Amma..."
"Shissshi..." Tayi saurin saka hannun ta tayi masa alamar yayi shiru, k'asa kunne tayi taji da gaske sanarwa ake na isowar sarki,sai a lokacin shima Sultan din yaji abinda yasa ta dakatar dashi, a birkice ya maida kallon sa kanta da sauri yace
"Zan dawo, zan fitar daku daga nan ba za'a dau lokaci ba."
Daga masa kai tayi tana jin yadda takun tafiyar Maimartaba na kara kusanto su, hannu ya sa ya maida nadin kansa ya rufe har fuskar sa sai kwayar idon sa da take a bud'e, yaji an turo kofar an shigo, bawan ne a gaba yana shigowa ya durkusa daga gefe da sauri Sultan yayi yadda yayi shima ya durkusa a gefen sa. Cikin takun sa me cike da Izza ya shigo ciki, ya sauke idon sa akan Sultan da wani irin yanayi.
"Waye kai!" Ya daka masa tsawa, tsawar data firgita hatta masu tsaron kofar wajen amma ko gezau Sultan be yi ba, a yadda yake jin zuciyar sa na tafarfasa zai iya tashi yayi kukan kura ya damki wuyansa har sai ya daina numfashi, amma da ya tuna matan nan biyu da bawan nan da ya taimaka masa wanda yasan idan har ya bari aka gane yadda ya shigo wajen toh yasan karshen ta kashe Sarkin zai yi, shi kuma ba zai samu damar yin abinda ya kamata ba. Wadannan dalilan su ne suka sashi kasa komai, ya cigaba da karanto Addua a zuciyar sa, ya dogara da Allah yasan kuma shi kad'ai ne zai iya fitar dashi daga halin da yake ciki.
Mikewa bawan nan yayi ya fita, sai gashi sun dawo tare da wani faffafan mutum me wani irin yanayin halitta, kallo daya zaka masa kasan babu d'igon Rahma a fuskar sa, takobi ne irin Wanda ake kira da gayawa jini na wuce tsirara rike a hannun sa, ya fad'i yayi gaisuwa sannan yayi wajen Sultan ya dora takobin a saman wuyan sa ta bayansa.
"Waye kai? Ta yaya ka shigo Masarautar nan? Waya baka izinin shigowa nan?*
"Nine na bashi izini." Ya fad'a yana tsayawa a kofar, dukka suka juyo, Maimartaba Sarki Bello Moddibo yace
"Yarima!?"
"Tuba nake ranka ya dad'e, waje na yazo abokin karatu na ne, sai muka fito zagaye dazun daga nan muka shigo nan muna duddubawa,wani uzuri yasa na koma na barshi anan."