Sashe 7
Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***
Tana kwance bayan ta gama duba gifts din da suka karba tana jiran dawowar Abba da wayar da yàce zai siyo musu a matsayin gift dinsa na grad da sukayi, duk da bata da tarin kawaye balle ace zasu dinga waya ko chat, amma tana so taga yadda duniya ta zama, tana so itama ta zama social ta shiga kowanne lungu da sako na social media taga me ake yi, me ake ji, plus abubuwan da suka shafi harkar chefs, girke girken dishes na kashashe daban daban da ya kasance passion dinta, idan da wayar zata kara samun experience na abubuwa da yawa, gashi tana da sha'awar karatun novels na manyan marubuta online both na turancin dana hausan ma.
Da sauri ta tashi jin maganar Abban a falo, ta fito da sauri har tana neman tuntube, boxes biyu ne a hannun sa an rufe su, hasken fuskar ta ya karu, ta karasa da d'an gudun ta suka saka Abban a tsakiya, sai da ya gama yi musu nasiha sosai sannan ya basu sabbin wayoyin hade da gargadi da ya fi yiwa Afrah, sunyi masa godia da alkawarin babu abinda zai faru in Sha Allah. Dakin su suka tafi suka hau kan wayoyin sukayi ta fama har dare yayi suna aikin abu daya, sai da Adnan ya shigo sannan ya taimaka ya tayasu yin wasu settings din shima sai da yayi ta ja musu aji.
Shirye shiryen tafiya Nigeria ya kankama, suna ta murna da dokin zuwa, ranar da daddare Abba ya dawo a gajiye ya shigo lokacin ma suna dakin su suna sabon aikin wayar da ya same su, ya same su man dan tun da wayar tazo basu huta da hidimar ta ba.
Bayan Umma ta gabatar masa da abinci da ya kasance snacks ne da milk shake, be iya ci ba yace ya koshi ya karbi black tea kawai yasha sannan yace
"School din nan da na taba yiwa Amrah applying sun fitar da circular zasu fara classes next week, akan girke girke da gyaran jiki da abubuwa dai, yanzu ne opportunity din da zata samu tayi kafin su shiga university."
Dan bata fuska umma tayi dan har ga Allah bata son abinda zai katse mata tafiyar ta, muryar Abba ta katse mata tunani
"Ba zan iya hanaku tafiya ba, dan kunsa rai bayan haka ma ya kamata kuje din, dole dai ita Amrah ta zauna sai na hakura ni dama akwai ayyukan da nake son karasawa."
"Toh yanzu ba yadda za'a yi kenan?"
"Eh hakan za'a yi, idan kuka dawo mu sai mu sa lokaci muje in Sha Allah."
"Toh Allah yasa haka ne mafi alkhairi, ita na su Afran basu fara ba kenan?"
"Eh su sai nan gaba, sune batch din da zasuyi bayan mamana sun gama."
"Okh Allah ya kaimu." Tace tana tunanin yadda Amrah zata ji idan aka ce babu tafiya
***
Duhu ne sosai da ya mamaye kowanne lungu da sako na dakin, karamin daki ne na gaske babu komai a ciikin sa sai ta wata yagalgalalliyar katifa data cinye kusan gaba daya dakin, daga chan kuryar dakin take kwance ta zuba wa saman rufin kwanon da rana ta gama dukansa duk ya bule hakan yasa haske rana ke shigowa ciki musamman idan ana tsananin ranar.
Sha biyu da wasu dakiku na dare, shiru kake ji garin yayi babu karar komai sai chan k'asa k'asa zaka dinga jiyo haushin karnuka da karar injinan gidan masu hannu da shuni dake chan kasan unguwar.
Juyi take ta tana aikin tunanin yadda rayuwar su ta zama yanzu, idan baka dashi shikenan rayuwar ka ta gama tagayyara, mutane a wannan zamanin kowa kansa ya sani, daga shi sai iyalin sa. Shisa gaba daya rayuwar tayi wahala ainun, babu me jin kan na kasa dashi balle ya taimaka masa, sake gyara kwanciyar ta tayi, ta cigaba da tunanin sana'arta ta kosai da take yi a kullum, abinda suke samu su rayu kenan ita da yayanta biyu mace da namiji Muhammad da Aisha, sosai Muhammad yake fafutuka akan su,tasan yana iyakar kokarin sa wajen ganin ya kyautata rayuwar su, ya inganta musu ita, sai dai komai baya tafiyar musu a daidai, babu me kula su da sunan abota, babu me hulda dasu saboda wani dalili da take ganin sa mara tushe, dalilin da be kai a wulakanta dan adam akan sa ba, musamman idan baka da masaniyar ainihin abinda ya samu rayuwar mutum har ya zama abinda ya zama. Allah da kansa ya ce ya karrama bani Adam, toh me yasa wasu mutanen suke wulakanta wannan darajar da Allah ya basu?
Gidan da suka zaune gidan haya ne irin babban nan, yana kunshe da dakuna a kalla guda asharin masu falle falle, sai kuma irin nasu me ciki da falo da ya kasance guda biyar irin sa a cikin gidan, kar kayi tunanin idan ance ciki da falo ana nufin hadadden daki, babu wani banbanci tsakanin nasu da sauran masu falle dayan, banbancin kawai guda biyu ne aka hade su suka bada ciki da falo. Suma da chan a guda dayan suke, amma sai aka fara juya magana ganin Muhammad ya girma ana musu mummunar fassara har ta kai maganar ta dawo kunnen su, ran shi ya baci sosai haka ya kara kai mi wajen yar sana'ar da yake ya samu suka kama daki biyun,shi yana falo su kuma su na ciki. Duk da haka basu tsira da maganar mutane ba, sai kawai suka tattara su suka watsar suka cigaba da rayuwar su yadda Allah ya hukunta musu.
Shekaru sun ja sosai haka ma rayuwa ta sauya wa mutane da yawa, ciki har ta wannan baiwar Allah me suna Safiyya, Wanda yayan ta suke kira da Ammi, mace ce jarumar gaske, da wuya ka gane wani abu a tattare da ita da zai iya yi maka fashin baki akan halin da take ciki, tana da kuzari da kazar kazar sosai wanda idan ba samun ta kayi a irin lokutan da take warewa musamman don tunawa da rayuwar ta ba, zakayi tsammanin bata da wata damuwa da irin rayuwar da suke yi, a zahiri ko yaushe cike fuskar ta take da farin ciki da annashuwa, Sai dai a bad'ini zuciyar ta ba haka bane, a chunkushe take da manya manyan kaddarori masu wuyar fassarawa, tabbas abinda ke cikin zuciyoyin mutane baki ba zai iya fidda su ba, wasu zakutan dankare suke da matsaloli masu yawan gaske. Duk da bahaushe kan ce labarin zuciya a tambayi fuska, amma a gurin wasu tsirarun mutane irin Ammi zai yi wuya ka iya gane ainihin abinda suke ciki, mace ce jarumar gaske, ta kowanne bangare tana iyakar kokarin ganin ta tsaya da kafar ta da rayuwar ta, tayi kuma kokari wajen manta baya!
Da yin assalatu take soma aikin sana'arta, ta gyara komai ta kimtsa shi waje guda, ba karamin karbuwa tayi da sana'ar tata ba, shiyasa bata k'asa a guiwa wajen kula da sana'ar tata.
Tashin Aisha taje yi ganin har rana ta soma fitowa bata ji motsin ta ba, sai ta same ta a dunkule waje daya tana motsa kafarta alamun idonta biyu
"Aisha?" Ta kira sunan ta, tana kokarin kai hannu jikin ta, juyowa tayi sai ta yi salati
"Baki da lafiya?" Tace tana matsowa kusa da ita
'Daga mata kai tayi tana ciccije baki irin na marasa lafiya, kama ta tayi ta zaunar sannan ta fita, sai gata ta dawo da kofi da ta jika kanwa, ta mika mata tasha lokacin har Muhammad ya shigo ciki yana yi mata sannu. Amsawa tayi ta koma ta kwanta a hankali sai cikin ya saki, ganin haka yasa Ammi ta koma wajen sana'arta ganin lokacin har ya fara shurawa.
Wajejen karfe sha daya bayan Ammi ta gama ta dawo da komai ciki, sai ciwon cikin ya kara tsananta, dole suka dunguma suka tafi asibiti da ita ganin yadda take murkususun ciwon kamar zata mutu.
***Ranar a gajiye yake, ga wani mugun ciwon kai daya addabeshi, ya takura masa har baya gani sosai, magani ya dauka yasha sannan ya koma bakin aiki, yau itace busiest day dinsu a clinic, shiyasa ma ko waya baya dagawa sai ta zama dole.
Kiran Dr Ahmad (Ruhi Daya) ya shigo masa a lokacin da yake kokarin maida wayar silent, da d'an sauri ya daga yace
"Sir."
"Kazo office ka same ni."
"Okh." Yace ya katse kiran ya fita da sauri, sauran wanda suke tare suka bishi da kallon tambaya, be bi ta kansu ba ya haye kan doguwar barandar da zata sadaka da ofishin Dr Ahmad, hannun sa sakale da bayan a bayan sa, yazo daidai wajen wani x-ray room yaji gaban sa na tsananta faduwa, tsayawa yayi ya dan waiga kamar me neman wani abu, babu kowa sai wani mutum da yake nufo shi, cigaba da tafiya yayi yana jin wani strong attachment da wajen, ganin babu komai yasa ya hakura ya karasa office din Dr Ahmad yana jin kamar ya bar wani abu me muhimmanci a wajen da ya baro.
Ba kowa ke samun damar ganin Dr Ahmad ba, ba kuma wai dan yana da wulakanci ko wani abu ba, sai dai kasancewar sa mutum me kwazo da iya aiki, baya gajiya kamar agogo haka yake shi yasa duk yadda kaso ganin sa, sai ka hada gumi ka share kafin ka samu ganin sa. Sultan ya kasance me tsananin sa'a dan shi har mamakin yadda ake zuzuta wahalar ganin Dr Ahmad yake, iya zaman sa a asibitin ya ganshi yafi sau nawa, da kansa ma ya karbi number sa yace zai neme shi, gashi kuwa ya neme shin duk da be san dalilin kiran ba, sai dai yana jin ko menene yana da muhimmanci.
Knocking yayi aka bashi Izinin shiga, sai ya yi sallama ya shiga cikin tsantsar nutsuwar sa dake kara masa girma a wajen mutane.
Fuskar Dr Ahmad a sake ya amsa sannan ya nuna masa wajen zama bayan ya amsa gaisuwar sa
"Muhammad Sultan Sulaiman."
Ya kira sunan shi yana kallon allon computer
"Yes sir."