← Book details Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 108

Sashe 8

Abinda Ke Cikin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka gode wa Allah domin yana sonka, lately mukayi magana da Prof Mudi head of department dinku akan kokarin ka da kwazon ka, hadi da irin course din daka zaba da ya zama ba kowa ne yake yi ba, muna lacking Cardiologist a kasar nan bama a garin nan ba, abun mamaki sai ga invitation daga Babbar University, University of Medicine Canada (My university thou 😁 I don't know ko akwai ta ko babu, just my imagination) suna neman hardworking and talanted students zasu dau nauyin sa yayi wani course na 3years akan Brain, so babu bata lokaci muka tura sunan ka da details naka, to cut the long story short, ka samu admission, duk wasu shirye shiryen sun gama, tafiya kawai ta rage maka."

Cikin tsantsar farin ciki yake kallon Dr Ahmad din har ya dire bayanin sa, àlhamdulillah ya ambata a fili yana jin kamar matsalar Safwan din sa ta kare, abin da yake tunanin yi kenan, abinda yake buri kenan, Sai gashi Allah ya kawo masa a daidai lokacin da yake bukata, godiya kam ranar Dr Ahmad ya sha ta, har sai da yace ya isa haka Allah zai gode wa, a take ya karbi mail dinsa yayi updating komai sai gashi sun turo masa admission letter din a take, da form din da zai cike for sauran abubuwan da zasu biyo baya.
   Fuskarsa ta gaza boye halin da yake ciki, sauri sauri ya dinga yi ya kira Safwan ya bashi labari, yana fita ya tsaya jikin wata kofa ya danna masa kira yana jera godiya ga Allah da yayi masa wannan gatan.
   Yana jin ya daga yayi wata dariya da shi kansa Safwan din sai da yayi sensing Sultan yana cikin tsantsan farin ciki

"Ya akayi? Daga jin muryar ka nasan akwai kyakkyawan labari, share it."

"Kana ina?" Yace

"Gani na je airport dauko Umaima, ya akayi?."

"Umaima!?" Ya fadi sunan yana son tuno ina yasan sunan

"Amma kai dan rainin wayo ne Yarinya Antyn Lagos fa."

"Ohh na tuna, wallahi sunan ne ya kwanta min."

"Haka kake ai, gashi ita bata manta da kai ba, sai tambaya take kana nan."

"Nima na tuna ta, an jima rabon da suzo kasan, anyways idan ka fito ku biyo nan sai mu wuce, akwai babban albishir."

"Sai ka dai ja min aji sannan zaka fada min ko? Shikenan gata nan ma ta fito tana zara ido, sai munzo."

Ya katse kiran, maida wayar yayi aljihu ya taka a hankali ya koma wajen aikin su, yana zuwa kai tsaye ya nemi izinin team leader dinsu akan zai je gida, be tambayi ba'a si ba yace shikenan sai gobe tun da dama be fiya daukar excuse ba. Kayan sa ya tattare ya zuba a jakar system din sa ya fito bakin wajen ya zauna yana jiran Safwan yana danna waya.

***Tun da suka tawo hanya take masa surutu, duk son magana irin ta Safwan sai data kure shi yaji ya gaji, ya fara amsa mata da eh ko a'ah, har suka iso asibitin be kara wata doguwar magana ba, kallon gate din tayi ta karanta abinda aka rubuta, sai ta fad'ad'a fara'ar ta tace

"Wajen Ya Sulty zamu?"

"Umm." Yace mata dan gaskia ta bashi haushi

"Yes! Rabo na dashi an dade, kamar kasan shi nake son fara gani kafin kowa ma, thanks so much."

Da mamaki ya dube ta, hadda su thanks so much, sai ya girgiza kansa kawai, bata san waye Sultan ba, zai iya share ta ya bawa iska ajiyar ta wallahi, dan ya tuna wani zuwa hutu da tayi lokacin ana gyaran kitchen cabinets Sultan din ne tare da me yin aikin, shi kuma Safwan yana daga kan fridge yana danna waya ta shigo kitchen din tana iyayi, tana tambayar sa ina aka ajiye plate da spoons zata ci abinci, be amsa mata ba sai kawai yaje ya dauko komai da yasan zata sak tambaya ya dire mata a wajen ya fice ya bar mata kitchen din, ba karamin dariya Safwan yayi a lokacin ba, tunowar da yayi yanzu ya kara sashi dariya sosai yana hasaso drammar da za'a sha idan ta nemi matsa masa.
   A bakin wajen yayi parking tayi saurin balle murfin motar ta fito, a daidai lokacin Ammi da Aisha sunzo wucewa, tana budo kofar ta bugawa Ammi a kafa, da sauri tace wash tana dan durkusawa saboda yadda taji zafi, a yatsine ta kalle su, irin kallon wulakancin nan kafin tace

"Ku baku san mota bane ko babu ita a kauyanku? Ba zaku dinga dubawa ba aikin banza."

Da sauri Safwan ya fito ransa a bace ya daka mata tsawa

"Wanne irin wulakanci ne ki bige mutum ki kuma bishi da cin mutunci huh?"

"Dan Allah Mama kuyi hakuri."

"Ba komai." Ammi tace suna yin gaba, ran Safwan ya baci sosai, yayi mata wani kallo kafin yace

"Wannan ba halin kirki bane, mutum daraja ne dashi baki san su waye ba."

"Baka ga laifin da sukayi bane? Ko basu da ido basu ga mota ta tsaya ba, zasu zo su makale a jiki."

"Ya isa! Ki koma mota ki jira na kirawo shi, ba shiga zakiyi ba ai."

Ranta ya baci ta juya a fusace ta shige ta zauna hade da bugo kofar da karfi, be ko juyo ya ga me tayi ba ya wuce ciki. Kafin ya karasa Sultan ya hango shi ya taso suka hadu a hanya, hannu ya mika masa suka gaisa sannan suka tawo still hanayen nasu sarke da juna zuwa wajen motar.

****
Toh masu karatu, ga Safwan na jiran zuwan sahibar zuciyar sa, sai dai gashi tafiyar ba zata yiwu da ita ba, gefe daya ga tafiyar da Sultan zai yi wadda zata zama budar mukullin labarin zuciyar mutane da yawa.

Wacece Ammi?
Wacece Umaima? Me zai faru Idan sultan ya tafi Canada, akwai soyayya me tsayawa a zuciya da ruhi
Akwai riguntsumi sosai da zai biyo bayan wannan sai dai amsar tana cikin littafin ABIN DA KE CIKIN zuciya

Domin mallakar naka sai ka tuntubi wadannan lambobin

0903 234 5899
Ko*_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

©_Hafsat Rano_

         Last free page (6)

***
Yana shigowa motar ya ji an kira sunan sa, ya juyo da dan sauri dan be ma lura da ita ba, murmushi yayi mata ya amsa sannan ya juya, sai ta fara masa surutu, dafe kansa yayi ta hannu daya yana jin wani haushi na kamashi, har suka zo gida bata yi shiru ba, haka suka fito suka shiga ciki still tana cigaba da surutun da babu me kulata a cikin su, sai ma kara sauri da Safwan yayi ya shige bangaren su yana daga waya.
   Jerawa sukayi har falon Mah-Mah, kana kallon yadda yake amsa mata zaka gane ba son hirar da take masa yake ba, zama yayi Mah-Mah ta fito kenan daga kitchen da sauri Umaima taje ta rungume ta suka saka dariya a tare

"Yanzu muka gama waya da Amina tace min kin iso? Nace dai Safwan yaje daukar ki ashe tare ma kuke da Sultan."

"Tare muke, sai da muka bi muka dauko shi."

"Sannu da zuwa toh, ki shiga ciki ki huta Hauwa zata kawo miki abinci."

"Ok Mah." Taja jakar ta ciki bayan ta juyo ta sakar ma Sultan murmushi, girgiza kansa yayi ganin irin kalar tata tarbiyyar, be ji lokacin da ta gaida Mah-Mahn ba kuma ko a jikinta,Allah ya kyauta kawai yace ya dan zamo ya ce

"Barka da gida Mah-Mah."

"Barka Sultan, ya aikin?" Ta zauna tana rage karar tv,

"Alhamdulillah."

"Ina dan uwan naka ya tsaya?"

"Ya shiga ciki."

"Owk sannun ku, abinci fa?"

"Um sai dan anjima, ni wani kyakkyawan labari nazo dashi ma Mah-Mah, yaushe Daddy zai dawo gida?"

"Ah Alhamdulillah, ko nayi sirika ne?"

Sosa kansa yayi ya girgiza shi yana dariya

"Scholarship na samu akan course din da nake."

"Alhamdulillah, alhamdulillah kai amma naji dad'i."

"Abin da ya dawo dani ma gida yanzu kenan, kin ga har sun turo komai."

Ya bude mail box din sa ya mika mata, karantawa tayi, sannan tace

"Wannan labarin yanzu zaka kira Daddy ka sanar masa, naga abin ba zai dau lokaci ba sai ka fara shiri."

"Shirin me za'a fara?"

Ya karaso ciki yana kallon Sultan, sai ya mika masa wayar yana murmushi, layi bayan layi yabi ya karanta sannan da sauri ya dago yana nuna farin cikin sa

"Amma gaskia baka kyauta min ba, da wannan good news din amma muka tawo all the way from asibiti har gida baka fad'a min ba."

'dage kafadar sa yayi yana murmushi yace

"Uwa ce gaba da dan'uwa ko baka gane ba?" Ya kanne masa ido daya yana kallon Mah-Mah

"Haka ne." Mah-Mah tace tana dariya

"Kaci bashi wallahi, akwai abinda nake son fad'a ma nima amma na fasa Wallahi, sai komai ya kankama zaka ji."

"Kar muyi haka dakai dan Allah, dan fesa min mana."

"Zaka bushe ka fado kamar ganye aikuwa, idan lokacin jin naka yayi kaji Malam."

"Kai kuwa Sultan kyale shi, dole dai zaka sani din, tashi kaje kaci abinci sai ka kira baban naku, kasan yafi so ku yayan sa ku fad'a masa abu kai tsaye ba wai yaji ta waje na ba."

"Toh Mah-Mah, bari na kirashin dan bana jin yunwa yanzu sai ko anjima."

"Allah ya kaimu anjiman."

"Amin." Suka fad'a a tare. Tashi tayi ta shiga ciki ta barsu suna cigaba da hirar tasu,
Chapter 8 · 0% Book details